← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 61

Sashe 36

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ka ji Maman nan ina ruwan ki da sa mana baki a maganar 'yan d'akin mu? To bazan koma ba ɗin har abada, sai dai ya biyo ni da takarda ta, ke kuma Allah ya bada sa'a zaki ce na fada maki, dama saboda irin wannan halin naki na ki yarda na sanar da ke tun a can da na sanar da ke da kin sa an kashe mu a banza"

Da jin kalaman Saudat sai Mama Balki ta bar wajen ta wuce d'akin ta,Juwairah kuwa sai ta qarasa cikin sake yin sallama,ta dan duqa ta gaida Suwaiba da ke qoqarin qota ta ta wuce, cikin b'ata fuska suwaiba tace wa Juwairiyyah,

" Malama bani waje driver na na jirana ina da wajen zuwa mai nisa, ko dake ke ya za a yi ki san nisan da ke tsakanin Kano zuwa Abuja tinda kin qunshe kan ki daga Kano sai kano?"

Ta na gama magana ta saka hannu a jaka ta d'akko kudi mai ɗan yawa ta watsa wa Juwairiyyah a jikin ta tace,

"Ga shi nan dama na san gaisuwar kenan, shine ya sa ki zuwa da wuri kar mu tafi ba a baki rabon ki ba"

Ta sa kai za ta bar gidan cike da takun kasaita ita a dole ga mai arziqi, cikin qunci da haushi tare da fushi irin na masu ciki in an tab'o su Juwairiyyah ta bi bayan ta ta jawo hannun yayar ta ta, kamar yanda ta wurga mata kudin a jiki itama ta wurga mata a fuska ta ce,

"Ashe har yanzu baku canja hali ba? Ban zo dan wannan banzan kud'in naku ba, nazo dan na ga 'yan uwana dana dad'e ban gani ba da kuma iyaye na, na zo domin zumuncin Allah ne, dan haka u keep ur filthy money with u,it will help u some day"

Ta juya tare da  shigewar ta cikin d'akin Mama Balki ta bar kowa na binta da kallo baki sake, tab'e baki Suwaiba ta yi daga baya ta dauke kud'in ta ta shiga mota tana d'aga ma Baban ta da Goggo hannu, suka juya birnin tarayya ABUJA.

Komawa ciki suka yi in da Baba ya shiga bangaren Mama ya isko Juwairah da Salma, Salma tana ba Juwairah hakuri akan komai da ya faru a baya, Juwairiyyah na ganin baban nasu ya shiga sai ta miqe da kyar dan ta durqusa ta gaishe shi, shi kuwa sai fad'in tayi zaman ta yake yi amma saida ta isa gare shi,ta durqusa ya dafa kafad'ar ta ta gaida shi tare da fad'in,

" Babana na yi kewar ka ba adadi ina ta so na zo na gan ku tunda Mama har yau bata je d'aki na ba ta sanya min albarka"

" Juwaireren Mama nima na yi kewar  ki sosai, da fa jibi muke saka rana zani ni da Salma mu gan ki, ki rabu da maman nan taki da alama sai na fara Kiran ta tsohuwa tunda ta na yi mana halin tsoffi"

Turo baki ta yi alamar shagwab'a ta ce,

"Babaaaa"

Dan ta riga ta gano faɗa kawai Shima ya yi ba zuwan da zai yi, shi ɗin ma kamar Mama Balki yake tun da aka yi mata aure ya daina zuwa gaida yayan shi a gida sai dai ya tadda shi a masallaci su gaisa  ya koma gida,dariya suka yi dikan su Mama Balki ta ce,

" Oh mai hali baya fasa halin shi an girma amma shagwab'a na nan"

Haka suka dinga hira cikin nishad'i da annashuwa, nan da nan Salma da  Juwairah suka qara shaquwa, hira suka shiga yi Salma ta ba ta labarin abinda ya dawo da ita gida, Juwairah akwai tausayi da saurin kuka dama,tausayin yar uwarta ne ya cika ta tai ta kuka kamar wadda aka daka, sai da ta gama ta rungume ta tace,

"kar ki damu yar uwa, da kin haihu zaki samu miji na gari inshaa Allah mai kud'in dai da kike so da yardar Allah"

" A'a Juwaireren Mama banni da talakan ma zan zauna ni ai yanzu talauci baya bani tsoro tunda na ga na gidan Talle"

" Kaiii Salma harda ke a Kiran wannan Sunan ko"

" A'a nima yau tab'awa na yi ai, ai baki taba jin na fada ba ko? To qara'i nai na da da ban tsokane ki ba"

" To shikenan ke kaɗai na yarda ki ce man Juwaireren Mama, ke ma iya na sati ɗaya kacal"

Ta faɗi hakan cike da nuna ita ɗin yar farin maman ta ce, dariya suka yi harda iyayen su dika, anan Ammar ya tashi daga bacci saboda shewar da suke ta yi, da sauri Juwairah ta isa ta d'akko shi, sai kallon ta yake yi, wasa take masa ta ji yana qoqarin yin magana,

" Mamma"

Shine abin da ya furta, daɗi ne ya kamata ta ce,

" laaaa mama yana magana dama?"

" A'a ya dai iya barna wannan"

Dariya suka yi suna kallon Ammar da ke taya su dariyar Shima,haka Juwairah ta gama yinin ta cijin jin daɗi,dan kuwa a tare suka yi girkin rana ita da Salma,ganin suna girki tare ne ya sanya saudat fitowa ta na ta auna masu rashin mutunci kala kala,amma ba wanda ya kula ta,dan kanta ta gaji ta koma daki, kyaliyar Mama Balki suka koya irin abun nan na mugun bata wa duk wanda yake maka masifa rai.

Ta bangaren Suwaiba mutanen ABUJA kuwa sun isa Abuja lafiya a matuqar gajiye kamar ita ta yi tuqin, tana isa ta tarar da masu aikin ta sun gyara gida ko ina fesss sai tashin kamshin turaren wuta yake yi,ga girke girke nan an yi na tarbon ta,ta na gama buɗe wa ta shaqi qamahin girkin sai kawai ta saki murmushi tare da fadin,

"Amma gaskiya Saudat shashasha ce, ni yanzu ina zan bar wannan gara ta wuce ni akan zargin banza da wofi? Hummmm bari ma na je na yi wanka na zo na ci na sha na yi hani'an gidan uba babu an dawo gidan miji ai sai a shoshale"

D'akin ta ta wuce direct wanka ta faɗa, bayan ta gama ne ta shirya cikin qananan kaya ta feshe jikin  ta da turare ta kwanta a gado ta na latsa wayar ta ta ce,

" Wawuya, yaushe zan bar wannan daula ta wuce ni, ana ki dawo kina wani ke gida yafi gidan miji, ai ni da barin Abuja sai da ziyarar ganin dangi"

A haka ko abincin bata samu ta koma ci ba bacci ya dauke ta, cikin baccin ta ji wani zafi kadan kamar an soke ta da wani abu mai tsini ta so buɗe ido ta ga menene amma ko bude ido bata sake iyawa ba ta lula duniyar duhu..........
[22/07, 8:44 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA  💅🏻

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 23:

Gobe ne ranar da Jabeer zai dawo gida daga wajen interview da ya je yi a Abuja, waya suke yi da Juwaireren shi wadda ke kwance a gadon ta da ya sha gyara kamar Jabeer na gida dan,bata daga cikin matan da ke qin gyara d'akin su saboda taqamar miji ya yi tafiya,hira suke sha ta soyayya gaba ɗaya Juwairiyyah ta shagwab'e masa ta susuta masa lissafi, ji yake yi kamar ya dawo a daren ko da fuskar ta ne ya kalla, ya san zai ji nishadi,  kwantar masa da hankali ta yi da cewar gobe suna tare da junan su da yardar Allah dan haka kar ya damu ya qara haƙuri,dole jabeer ya hakura ya daina yi mata shagwab'ar da ya ke sanya ta nishad'i da dariya, Itama ta na jin ta kai wata a wajen miji tinda duk girman shi ya yarda ya amince ya bayyana mata yarintar shi.

Suna gama hirar su ta soyayya ta tuna masa kar ya manta fa ya yi addu'ar bacci kafin ya kwanta,sai  su ka yi addu'ar tare suka kashe waya, bayan cika juna da "I love u", haka suka yi bacci cike da matsananciyar kewar junan su.

Da sassafe bayan tayi sallahr asuba tayi abubuwan da suka zama na al'adar ta da safe kamar yanda kuka san Juwaireren Mama, taso yau ta bar gyaran lambun ta da ta yi a cikin gidan saboda sauqaqa masu wahalar rayuwa sai ta ga dacewar ta gyara ɗin in yaso daga baya ta gyara gidan ta da girke girken tarbon mijin nata.

Da misalin 9:28am Juwairiyyah ce sanye da doguwar riga mara nauyi mai hannun shimi, ta dauki kayan gyara lambun ta ta fara gyara abubuwan da suke da buqatar gyaran, da ke ta na da saurin aiki cikin qanqanin lokaci ta gama cire ciyayi da bawa shukokin nata ruwa sannan ta ajiye komai inda ya dace ta wuce d'akin ta ta gyara shi ta hanyar sauya wankakken zanin gado da sauya wankakkun labulaye.

Tattare zanin gado da labulayen da ta sauya ta yi zata fitar Nafeesa ta yi sallama, cikin ɗan haɗe fuska Nafeesa ta ce,

" Haba matar Yayah ai sai ki kirani, da wannan tsohon cikin haihuwa ko yau ko gobe Zaki zauna ki na aiki mai wahala haka? Salon kawai ki ja mana wani aikin, habaa gaskiya ban ji daɗi ba"

Ta qarasa maganar ta ta na karb'ar kayan hannun Juwairiyyah, murmushi Juwairah ta yi ta dafa kafadar Nafeesa da ke kumbura baki ita a dole Fushi take yi sannan ta ce,
Chapter 36 · 0% Book details