Sashe 13
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunani suwaiba ta zauna ta na yi bayan ta katse Kiran da ta yi wa Goggo, so take ta tuna abubuwan da suka faru amma kanta ya kulle sai ma wani irin bugawa da ciwo da ta ji ya na mata, komawa ta yi ta kwanta a hankali,ajiyar zuciya ta sauke a qoqarin ta na dena tinanin,
" Babe what is wrong, na ga gaba ɗaya mood ɗin ki ya sauya"
A hankali ta furta,
"kai na ke min ciwo sosai, so nake yi na tina abubuwan da suka faru a tsakanin wannan watannin da akai auren mu amma gaba ɗaya na kasa"
Cikin sigar lallashi ya kama hannun ta ya ce,
"ki dena yawan tinani likita ya hana, saboda zai jawo maki ciwon kai mai tsanani, ki kwantar da hankalin ki kin ji, aikin da akai maku ne yasa kuka kai wadannan watannin ba tare da sanin inda kan ku yake ba, ni dinnan da kk ganni sai da nai sati uku a asibiti ban san ina kai na yake ba, abokina kuma wata daya da sati biyu, kafin mu ka ji sauqi ai ba karamin abu ne ya faru ba a ranar"
Tausayin kansu ne ya kamata, lallai ashe hatsarin babba ne? A haka bacci ya ɗauke ta shi kuma ya yi palour yana murmushin samun nasara, waya suka yi da Alhj Kalla, cikin nishad'i suka fara hira,
"Aboki ya ka qare da 'yar rigimar ka?"
"Ba wata damuwa Komai ya tafi as planed, ban samu matsala ba, wannan shegiyar uwar tasu ce taso sawa mata ta tinani,amma na kawar da shi, yanzu haka bacci take yi"
Sariya suka saka a tare sannan Alhj Ƙalla ya ce,
"Ai ni tashi ta yi tana min shagwaba sai na ji kamar na manta da ciwon na dan more ta kadan, dan sai ta min kyau sosai, gaskiya mun iya zaɓe aboki na, kyawawa na gidan talakawa a b'oye talauci duk ya rub'ar da wasun su, su zo a fantama da su a samu kuɗi amma sai ka ga sun ki wai su na Allah, yanzu su wadannan da suka fito ba gashi sun haɗu da mu ba za mu shagwab'a su da nera? Ga kyau ka kuɗi Alaji"
Dariya Alhaji Salihu ya yi sannan ya ce,
" shegen sama, ana halin neman yanda za ai a rufawa kai asiri kana neman biyan buqatar ka, to amma fa mutumi na suna da gaskiyar su,mu ɗin ba rud'in shaid'an muke bi ba, ai tsoron Allah ne ya hana su fitowa gwanda su je lahira su shiga aljannah, mu ma dai kafin mu mutu mun tuba,"
(Kamar an sanar da su ranar mutuwar su)
Dariya suka yi ta yi kamar abinda suke faɗa ɗin ba wani abun damuwa bane,Alhaji Ƙalla n e ya ce,
" Anyway gate can dai na yi mata dabaru irin namu na manya ta bar zance fatan ta Allah ya bata lafiya, kasan har yanzu maganin bai gama sakin su ba, bacci take ta yi"
"Haka ne, to sai dare in mun hade a gidan Oga, yau akwai meeting fa ka san"
"Eh haka ne fa,to ba damuwa sai daren ma haɗe a can ɗin"
kashe wayar suka yi kowa na jin daɗin samun nasarar da suka yi akan su suwaiba mutanen ABJ, yanzu tinanin su bai wuce yanda zasu na samun jini da aka ce suna kawo wa duk wata ba daga matan nasu, dan su ba sa son suna satar 'ya'yan mutane ana tsafi da su shi yasa suka yanke shawarar auren matan da za a dinga amfani da jikin su da kuma jinin su ana tsafin,dan satar yara a wajen su babban aiki ne da kuma wahalar wa,sannan su na tsoron kar watarana a kama su, dabara ce ta fado mai na yanda zasu na samun jinin daga wajen su, murmushi ya yi sosai,sannan ya ce,
"Dan ta rashin haihuwa me sauqi ne, tunda ba ni aka cirewa mahaifa ba bare na damu, 'ya'ya dama takura ne a rayuwa ta, sanda na so haihuwa na nemo matar da zan haihu da ita na aura,"
Dariya ya dinga yi kamar mahaukaci sabon kamu ni ko nace hmmmmm kwadayi mabudin wahala.
*****************************
A gidan Salman Talle kuwa, ko in ce Tallen Salma, ko kuma Tallen Marka, ana can ana badaqala uwa ba hantara uba baya nan sai ya ga dama ya leqo ya koma.
Huwaila ce ke duqe gaban murhu ta na hura wuta, can ta d'ago ta yi wurgi da maficin hannun ta ta na buga qafa a qasa ta ce,
" Ni dai Marka gaskiya na gaji da yin abinci kusan kullum a gidan nan habaa ai ni ba baiwa bace,kullum ni nake abinci talla sannan na yi na gida ?"
"Nima haka gaskiya, wannan yar rainin ajawalin na zaune a d'aki kullum sai dai mu dafa mu bata, ga Baban ma baya nan sai sanda ya ga dama yake zuwa"
"Tab ai ko yau ita zata yi tuwon dare ko ta ji a jikin ta, ni hutu ya samen, dan ba zai yu na nemo na tuqawa ba kuma na dafa na ba ku ku ci ba inaaaa, dole Itama ta fito ta girka ai gidan mijin ta ne itama"
Ihu 'yammatan suka sanya suna fad'in,
"Sai Markaaaa, uwar gidan Talle, an buga an barki"
Dariya da shewa suka sake sanya wa kamar wasu 'yan daudu, ita kuma marka ta wani d'age qafa tana zaune a qasa ta turo dankwali gaba, tana kada qafarta da ta yi fururu kamar tunda aka haife ta bata san menene nan shafi ba,
" Je ki kiran ita Huwaila yanzun nan"
Da hanzari Huwaila ta miqe kuwa tana gyara daurin qirjin ta, tana tafe tana banqaro qirji, qugun kamar an daurawa tabarya zani, ta na Isa qofar d'akin Salma sai ta tsaya a bakin kofa ta daga labule ta cake tare da kama qugu ta ce,
" Amarya ki zo Marka na son magana da ke yanzun nan"
Salma na kwance ta ji Huwaila na mata magana cikin raini sai ta ji kamar ba zata amsa ba dan kuwa duk tana jin su, sai dai kuma wani irin mugun tsoron su take ji yanzu, dan duk wani rashin mutunci da yake faruwa a gidan ya na shiga kunnen ta, yau da gobe duk tana jin su, fitowa ta yi dan ta tsira da jikin ta, dan yanda suke ikirarin dukan ta kullum tasan za su aikata,ga uban su baya nan, ko yana nan bata jin a tarbiyyar gidan Talle zai ɗauki mataki sun dake ta sun daki banza a banza ne kawai,
"Auuu kinzo shine ba zaki yi magana ba ma ki ka tsaya qiqam akan mutane haka?"
Cikin tura baki gaba ta ce,
"Gani"
Saida Marka ta kalle ta asheqe sannan ta ce,
"Salma ki ke ko wa? Ni kin San ba sabgar ki nake shiga ba balle na riqe Sunan ki,ki bude kunne da kyau ki ji, daga yanzu ke zaki dinga girkin gidan nan na safe da rana da dare, su yaran sun ji da na siyarwa, ba zai yu na yi ta wahala ba a gidannan, ke kina nad'e a gado, sai dai na dafa na miqa maki, ki cinye ki gyara d'aki ki yi wanka ki koma ki kwanta, ai ba abinda ya kawo ki gidan miji kenan ba, bautar aure kika zo yi, dan haka kula da yaran tsakar gidannan ma yana ciki, tsarkin kashin su da yi masu wanki, duk naki ne yanzu, in dai hutun amarci ne sati ɗaya budurwa, bazawara kwana uku, ke ko ban san ame zan saki ba, tsabar adalci irin nawa wata biyar da kwana hudu na baki kika huta, dan haka daga yanzunnan ba sai anjima ba ki dau aikin ki"
" Wooo ke wooo ke markan Talle"
Yaran suka dauka suna ta mata kirari tana kad'a qafa tana hura hanci su kuma suna dariya, kallon Salma da ke tsaye ta na kukan zuci ta yi ta ce,
"Ban ji kin amsa ni ba fa"
Cikin rawar murya Salma ta ce,
" To"
Ta juya zata tafi ta ji wani daga yaran na fad'in,
" Naaa gaaamaaa"
Kukan da take ta yi a zuci ne ya taso mata da karfi,nan take ta tuna da tinda take bata taba ɗaukan Ammar ba ma balle ta kai ta ga yi masa tsarkin kashi, gashi yau za ta yi wa ɗan wasu tsarki, kuma an maida hakan aikin ta.
Cikin Isa Marka tace,
"Ba ki ji bane ana sanar da ke an gama kashi ki je ki wanke sai kin gama qamar da dan mutane?"
Sim sim sim Salma ta wuce zata je wanke masa kashin,Haule ta taso tace wa Salma,
" Aunty bar shi na wanke masa"
Marka ta sauke qafar ta da ta ɗora a d'ayar ta kalli Haule ta ce,
"Ke uwar kitifi uwar kinibibi, ina ruwan ki da hukuncin dana yanke? To a hir din ki kar kina min haka ranki zai mummunan baci, ita na ga dama ita zata wanke"
Salma ce ta kalli Haule da murmushin yaqe ta ce,
"Na gode Haule zan masa kije kawai ba komai"
Wanke wa yaron kashin ta yi zuciyar ta na matuqar tashi, tana fitowa daga band'akin wajen zubar da na poo ɗin yara suka kwashe da dariya har da uwar tasu suka tafa, murhu Salma ta nufa ba tare da ta tanka su ba to me ma ta isa ta ce? Ta na Isa ta duqa ta ci gaba da hura wuta ta dora ruwan tuwo, ranar dai a taqaice ba ita ta kwanta ba sai goman dare, jikin ta ba inda baya yi mata ciwo dan aikin wahalar da ta tiqa, tuwo ta tuqa da ya kai yawan kwano ɗaya da rabi har na dumame, dan haka tana kwanciya ta hau bacci kamar wata matacciya.
**************************
" Dan Allah Juwairah ki yi sauri mana, duk wannan wankan naki na qa'ida sai ya sa ba mu fita da wuri ba"