← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 61

Sashe 46

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwalla ta share ta ja hanci, tana kallon su cike da tsanar halayen su, tashi ta yi daga wajen da su Marka ke zaune ta yi shigewar ta d'aki,addu'a take ta yi ma 'Yar uwar ta a ranta na Allah ya yafe mata, Yayan Talle kuwa bayan jinya da zaman d'aki ya jawo masa har da gudun abun kunyar da ya tafka gani yake mutanen waje sun sani, wanda bai sani ba ba wanda ya san ya na neman Marka a waje maganar iya cikin gida ta tsaya dan babu mai zamar yin kirari ya dab'a wa cikin shi wuqa a cikin su .

Duk maza da ke zama a majalisar qofar gidan su Talle sun sauya wajen zama,tabarmin da aka shimfid'a domin zaman makoki ba mutane akai da an gaishe su ake wucewa daga Baban gida da Badamasi sai Talle a wajen, Talle kuwa mugun haushin Yaran yake ji sai kallon su yake ya na jin kamar ya je ya shaqe su, amma haka ya dinga haɗiyar yawun baƙin ciki dan kuwa a irin iskancin da ya aikata a duniya ko kwata basu yi ba ya san sakayya ce yake Karb'a da hannun hagu tun a duniya.

Basu tashi a wajen ba sai bayan la'asar,Talle tashi ya yi ya hau nade tabarmar da yake kai sannan ya shiga gida fakam-fakam ya tsaya a kan Huwaila, kwalama su Baban gida kira ya yi, a tare suka isa tare da jingine tabarmar da suka zauna akai kan su a qasa kamar munafukai, cikin b'ata fuska Talle ya ce,

"A cikin ku waye me cikin Huwaila?"

Badamasi  ne ya nuna Bangis da sauri, shi kuma Bangis sai ya qara duqar da kai qasa,kallon su Talle ya hau yi daga sama har qasa cikin qunar rai ya ce,

" Yanzu yarannan wai har kunyi girman yi wa wata ciki? Ko dake maganar wai kun yi girma ma bata taso ba tinda ga misali kun bayar, kun yi sanadin mutuwar ɗaya ga ɗaya nan da tambarin abin kunyar da zai bi zuri'ar mu har abada, dan haka sai ka bari ta haihu a maku aure kun reni ɗan shegen cikin gidan da kuka samar tare,"

Ita dai Marka bata cewa umm bare A'a, ta yi dif sai hawayen nadamar rayuwar su ke fita daga idanun ta, a cikin zuciyar ta tana ayyana wannan lamari ba laifin kowa bane face na shi, daya tsaya ya tsare mata sha'awar ta da buqatun ta da bata yi zina da auren ta ba.

Ni kuwa na ce wannan ba hujja bace ga matan da suke ganin dan mijin su baya sauke haqqin shi akan su bari su bazama neman mazan waje, ko su fara aikata wani abun da ya kauce hanya, su sani Allah zai masu hukunci dai-dai da abinda suka aikata ne shima mijin Allah zai masa hukuncin abinda ya aikata,dan haka ni a ganina ba dabara bace aikata Zina da aure, wadda ke da matsala da mijin ta ta bangaren auratayya ta gaggauta neman mafita ta hanyar shari'a ko sulhu ita da mijin su rabu ta nemi wani, ko ya bi duk wata hanya ta halal da ya san zai katange ta daga fad'awa haram,bai halatta ta faɗa halaka ba da sunan rashin kulawar miji mu kiyaye.

Miqewa marka ta yi zata shiga d'akin ta, Talle ya dakatar da ita,cikin muryar da Marka bata taɓa zato ba ta ji Talle na fad'in,

" Marka ina neman yafiyar ki akan dikkan abubuwan da suka faru tabbas laifi nane, da na tsaya na zama namijin kirki da duk haka bata faru ba, ki yafe min mu dawo mu gyara rayuwar auren mu,"

kauda kan ta ta yi saboda kukan da yake neman cin qarfin ta ga wani haushin shi da take ji na jefa su wahala da ya yi, Yayan shi ne ya fito daga ɗan qaramin d'akin shi ya zube akan guiwowin shi ya na hawaye ya ce,

" Talle qanina ka yafeni na biye wa son zuciya, da rudin shed'an na aikata mummunan abun da ko mutuwa muka yi sai yabi zuri'ar mu domin kuwa shi mugun labari kamar tusa ne a wajen bodari ba ya riquwa watarana sai ta fita, ka taimaka ba dan ni ba domin Allah da zumunci ka yafe min"

kuka ya kifa hannayen shi a fuskar shi yana yi hakan kuwa ba qaramin bawa kowa tausayi ya yi ba har ta kai da Talle ya daga shi sannan ya ɗan daki kafadar shi dan shima kukan yake ji, kauda kai ya yi zai shige d'aki yaji maganar Yayan nashi na fad'in,

"A gaskiya sai mun haɗu mun gyara rayuwar gidannan namu kan komai ya tafi mana dai-dai yanda ya kamata cikin tsari da tarbiyya irin ta islama, na farko sai Marka kin gyara yanayin shigar ki a tsakar gidan, dan kuwa yanayin yanda iyalin ka take yawo a tsakar gidannan ne ya jawo min matsananciyar sha'awar kasancewa da ita,haka za ka ga tana yawo ba isasshen kayan da ya rufe dikkan jikin ta, tana tafe tana juya dikkan jikin ta, sannan ga maganganun ta da na ke jiyo wa wanda yawancin su akwai sakin layi, ma'ana akwai batsa da watsewa a cikin su, wajen kallon ta da maganar ta bata kiyayewa, wadannan abubuwan sun ja ra'ayina matuqa ainin, dan haka in muna son mu samu kwanciyar hankali da kiyayewar zinace-zinace a tsakanin mu sai mun kiyaye,sannan sakewa yarannan da muka yi shima ya jawo wannan bala'i da muka shiga har ya yi sanadin mutumar Jummai, Yaran nan kan su ba su yin shigar arziki ga mazan da ba muharraman su ba a cikin gida,mu na ji za su dinga mugun wasa a tsakanin su ba ma hana wa a haka muna ganin ai 'yan uwan juna ne,to wannan sakacin namu duk shi ya jawo mana komai,Su ma kuma yaran mata kamata ya yi idan maza suka kawo maku hari irin wannan ku na sanar da iyayen ku da wuri gudun kar abun ya ci gaba har a samu matsala yarinya ta lalace a gaban iyayen ta,iyaye kuma idan yara sun kawo masu magana makamanciyar wannan su wayar wa da yaran su kai akan yanda za su kare kan su da kuma karb'ar maganar su dau mataki akai kar su hantari yaro dan gudun zubewar mutuncin mutumin da ke neman cin zarafin yaran nasu ko gujewa tonuwar asirin yaran su, a dinga ɗaukan mataki saboda rage faruwar haka a cikin al'umma"

Talle ne ya amshe maganar da sauri ta hanyar gaskata yayan nashi,sannan ya basu tabbacin dawowar shi qauye da zama, don ya gama zaman birni kenan har abada, murna a wajen Marka kuwa da jin wannan labari mai daɗi ba a magana,sai dai ta bar wa ranta ba ta ce komai ba har wannan lokacin,a haka suka watse kowa ya kama inda zai yi cike da alhinin mutuwar Jummala.

******************************

A cikin sati uku Baba da 'yan taya aikin shi ko na ce 'yan taya hirar shi suka kammala ginin babban d'akin su suwaiban, da yake filin dama ya na da ɗan girma,sai dai kuma ba filasta ba fenti, sai ledar d'akin da suka fara shimfida qaton buhu a qasa sannan suka saka ta, katifa biyu suka yada, babba da qarama, sai kayan sawar su da suka kwaso suka zuba a ciki, d'aki yayi ba laifi, kullum dare Suwaiba sai ta yi kukan rashin mijin ta da kuma yanda ta koma mara amfani a cewar ta, yanzu wa zai aure ta a haka? Yaushe Salihu zai aiko mata da takardar sakin ta ko kuma ya zo ta gan shi? haka za ta yi ta saqe-saqe har bacci b'arawo ya ɗauke ta.

Hajiya Goggo kuwa mai niyyar hawa jirgi a je Makka bata samu hawa jirba ta samu mummunan hawan jini, sakamakon sanya tinani da damuwa da ta yi a ran ta,ta riga da ta saba a Koda yaushe Yaran ta na manne da ita suna shan hira,amma yanzu tsakanin su gaisuwa ne kawai,Shima dan ta san Mama Balki ta matsa masu ne da ba za su gaida ta ba,in suka gaida tan suka tafi sai dai ta jiyo hayaniyar su da Mama Bilki tana koya masu abubuwa masu amfani a rayuwar su ta duniya da lahira, wanda ita ya dace a ce ta koyar da su tun farko,gefe d'aya kuma haka za ta ji suna wasa da Ammar kamar ciki ɗaya suka fito da shi, abun ba qaramin d'aga mata hankali yake yi ba,uwa uba Baba ya juya mata baya, baya kula ta, baya cin abincin ta ballantana kwana a dakin ta,Goggo ta je asibiti a kwanakin nan yafi sau uku, dan kuwa wata rana sai kawai tana zaune ta ji wani jiri da duhu ya mamaye ganin ta har sai ta suma, haka za su kaita a bata magani  su yi qoqarin da zasu yi akan ta, da ta farfad'o su sallame ta Baba ya maido ta gida, a kullum takan ce a cikin ranta,

'Oh ni Sarai naga duniya,  Yarana da nake taqama da su a idon duniya su suka juyan baya yanzu, Allah gani gare ka ka dawo da hankalin su kai na'

Yau Goggo ta tashi da matsanancin ciwon kai, in da ta dinga kiran Suwaiba ta na zaune tana jin ta amma ta yi shiru, Mama Bilki ce ta leqo ranta a b'ace tace wa suwaibar,

" Suwaiba kina son shiga aljanna kuwa? Mahaifiyar ki na kiran ki kina ji amma ki yi shiru? ki kiyayi Allah, ki kiyayi fushin uwa akan ɗan ta suwaiba, meyasa kk da ruqo ne, shi wancan mijin naki mai qaton ciki ba dan d'an kyaun da yake da shi ba meye abin so a wajen shi, duk da wahalar da suka jefa ku ciki kina nan kina faman son shi, kina begen shi sai uwar da ta haife ki ce Zaki kasa yafe mata? To na qara jin tana kiran ki kina ji ki zauna kiga ya zamu qare da ke a gidannan shashasha kawai,kin miqe ko saina kwad'o maki wannan murfin kwanon a ka?"

A hanzarce ta miqe tana kallon hannun Mama Bilki mai riqe da kwano, shigewa dakin Goggon ta yi tana zumbura baki ta ce,

" Gani"
Chapter 46 · 0% Book details