← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 61

Sashe 47

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ja ta tsaya a kan ta,a hankali Goggo ta buɗe baki ta ce,

" Suwaiba nice fa Goggon ki abar son ki, Suwaiba ba dan Adam ɗin daya wuce kuskure a rayuwar shi na san na yi kuskure,amma yanzu na yi nadama ku yafe ni ke da yan uwan ki, na san ban zama uwa ta gari ba a gare ku,ko wannan ciwon da nake fama da shi ya ishen azaba suwaiba, kullum da ciwon kai nake kwana ba qaqqautawa, na rasa ya zan kuma duk na san sanadin juyan baya da kuka yi ne, a tinani na a da rayuwa mai kyau nake baku ashe ban sani ba ina tura ku ga halaka ne, dan Allah suwaiba ku yafe wa Goggon ku kun ji?"

Kuka Suwaiba take yi sosai harda majina, kusa da goggon ta ta je ta zauna ta dora kanta a kan cinyar goggon ita kuma ta hau shafawa hankali, ba wanda ya qara cewa komai a cikin su, nan take Goggo sarai ta ji kamar ana zare mata ciwon kanta,damuwar ta na raguwa.

****************************

Jabeer ne ya sauka a saman machine cike da matsanancin farin ciki, bakin shi washe ya kasa rufe shi kamar gonar audiga ya shiga gidan, qoqarin shi bai wuce ya ganshi a gaban mahaifan shi ba da matar shi.

Cikin murna ya qarasa shiga bangaren Innarmu ya na kwala mata kira, sai dai abinda ya bashi mamaki be wuce ganin sashen nata wayam da ya yi ba an karo qofar sashen, bangaren su ya yi cike da doki da zumud'in ganin Juwairiyyah, durqushe ya ganta gaban ta robar da ta haɗa zuma da ruwan zam-zam ne da ta yi wa fatiha qafa bakwai, falaqi bakwai,nasi bakwai, da suratul ikhlas bakwai, sai Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla wa anta taja'alal hazna idhashi'ita sahla qafa bakwai tana sha tinda cikin ta ya yi wata takwas dan samun sauqin haihuwa, ta shan ye ya kai rabin robar tsabar azabar da take ji a Jikin ta, zufa kuwa sai karyo mata take ko ta ina, sai addua take tana qarawa,

" Allahu Allahu Allahu rabbi la ushrika bihi shai'an wa huwassami'ul aleem"

Shine abinda take faɗa tana maimaitawa, da sauri ya isa gare ta, ita kuwa ruwa ya fashe mata tana wani irin nishi na son ta sillub'o koma meye a tattare da ita, sauri ya yi ya juya ta daga durquson da ta yi sabida kar ta haihu a haka ta samu mummunan tsaga, zaunar da ita ya yi ta gaba ya koma bayan ta yana qoqarin taimaka mata, dan a yanda ya ganta da yanda suke karantawa shi da ita a wani littafi mai suna EVERY WOMAN ya san haihuwa ce ta zo, ba yanda zai ya fita da ita asibiti haka zata iya haihuwar a hanya.

Suna haka suka ji sallamar Innarmu ta zo da kwad'on rama zata bawa Juwairah,

"Ki na ina? Fito na samo maki ramar da ki ke so har na ma sa mata kuli na kwad'anta ta, ai ina zuwa gidan Iya mai rama na yi sa'a har zata fita talle na samu na samo maki"

Jin nishin Juwairiyyah da maganar jabeer ne ya sanya Innarmu saurin shiga parlour ganin gwagwarmayar da ake yi ne ya sanya itama ta duqa ta hau taimaka masu, nan take Juwairiyyah ta fara yin nishi mai qarfin gaske...........
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼   ' YAN ABUJA  💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 28:

Duk qarfin ta ta tattara ta damqe hannayen Jabeer ta ci gaba da nishi, har babyn da ke cikin ta ta samu damar sako kai cikin duniyar tamu,cike da murna da farin ciki jabeer ya qanqame Juwairiyyah a Jikin shi ya na jera mata sannu ba iyaka, sai share mata zufar goshin ta yake yi,a hankali ya sumbaci kuncin ta,Innarmu na ganin haka ta haɗe fuska ta na ɗaukar yarinyar ta kauda kai irin na mutanen da masu kunyar nan ta ce,

" Oh yarannan ba ku jin kunya ta sam, Jabeeru kalli yanda ka yi jagab da hawaye duk dan tausayin matar ka,ita kanta mai haihuwar ma ta yi jarumta ko kuka ba ta yi ba sai kai"

Cikin dakewa da son boye halin da ya shiga na farin ciki bayan kukan tausayin matar shi ya ce wa Innarmu,

" A gaskiya Innarmu ba abinda zan ce dake sai dai na ce kawai ubangiji ya miki rahama, ya sanya min ke a aljanna madaukakiya, ke kuma Juwairah Allah ya maki albarka, ya biya maki dukkan buqatun ki, ni Jabeer yau na qara alqawarin riqe amanar ki har qarshen rayuwata"

kallon Innarmu ya sake yi ya ce,

" Innarmu da ace mazaje suna shiga d'akin haihuwa da matan su su na ganin yanda mata ke k'ok'ari wajen fito da wata sabuwar rayuwar zuwa duniya tabbas da an rage mace-macen aure da wulaqanta mata, da maza sun daraja mata fiye da qima, Innarmu duba fa kiga irin wahalar da yarinyar nan ta sha, dan Allah Innarmu idan na taɓa aikata maki wani laifi ko na b'ata maki rai ba tare da na sani ba ko kuma na yi da ganganci ki yafe min, na yi alqawari daga yau zan zamo daga cikin yara masu biyayya,"

Nan take jikin Innarmu ya yi sanyi, dan kuwa tabbas ta san iyaye mata suna qoqari,bamu da abinda za mu yi musu da ya wuce muyi ta masu addu'a da qoqarin yi masu biyayya,a hankali Innarmu ta ce,

" Jabeeru duk abinda ka fada gaskiya ne,kai d'a ne mai biyayya da kyautata wa ga iyayen shi da ma duk wanda Allah ya haɗa ka zama da shi, ba abinda ka yi min a rayuwa mara kyau da zan iya tunawa balle har na riqe a raina,kyautatawa ce kullum a tsakanin mu da kai Jabeeru, Allah ya yi muku albarka ya raya jinjirar nan cikin imani,ka ga yanzu yarinyar nan tana ta bushe wa, tashi ka je sashe na ka saka ganyen magaryar nan a ruwan zafin da na saka dan na yi wanka su tafasa tare saboda ya fidda dattin jikin yarinyar sosai,oh ni Hansai Jabeeru kazo ka dauki 'yar ma mana ka riqe matar ka kamar wani zai ɗauke ta magana nake yi amma hankalin ka na wajen matar ka"

Dariya ya yi yana sosa qeya ya gyarama Juwairah zama sosai yanda zata ji daɗi sannan ya isa gaban Innarmu, kallon yarinyar yake da tsantsar soyayya irin ta uba zuwa ga 'yar shi, wani irin kyau ya ga Allah ya yi mata na musamman, wannan kyaun daga ina ta samo shi? juyawa ya yi ya samo amsar tambayar shi wajen juwairah, murmushi ya mata sannan yace,

"Tabbas na samu amsar tambaya a fuskar ki, kyaun yarinyar nan duk naki ne Honey"

Innarmu ce ta yatsuna fuska cikin rashin gane ne ya ce ta ce,

"Meye wata Hamee ni ta shi ka dora ruwan ka dawo ko kuma ka gyara ruqon ta naje na kwaso na bangare na dana zuba d'azu dan na yi wanka,riqe ta na je na dawo"

Gyara wa babyn zaman kanta ta yi dake a lankwashe a hannun Jabeer da bai iya ɗaukan jinjiraye ba sannan ta fice tana fad'in ,

"Yara ido ya bushe ba kunya, zamani duk ya canja iko sai lillahi ji yanda yaron nan ke abu kamar a fim din hindiya"

Zuwa ta yi sashen ta ta zuba ganyen magaryar a ruwan ya ci gaba da tafasa sannan ta kwashe ta qara wani,ta taho da shi sashen Juwairiyyah,yarinyar ta Karb'a a hannun Juwairiyyah da Jabeer yake wa tsiya ta fara wanke wa, mamaki ne ya ishe ta ganin Jabeer na gyara Juwairah kamar ya san ya ake kula  da mai jego,

"Sai wani tsokanar ta ka ke yi ta ji zuwa na ta na so ta ajiye yarinya, ba gwanda ita ba da sauran kunyar ta a Jikin ta,kai ni fa sai na bar maku wajen ku ku qarata, wannan rashin kunya har ina, wa ya koya maka yanda ake ma mai jego ni Hansai"

Cikin dariya Jabeer yace,

" Innarmu na koya ne a wani littafin anti-natal ɗin ta da na ke karanta wa lokaci zuwa lokaci, littafai ne da suka qunshi yanda ake renon ciki da haihuwa da kuma yaran kansu, da irin taimakon da uba zai ba uwa in ta haihu, ina fatan kin fahimta, baya daga cikin kyautatawa namiji ya bar mace ta yi ta wahala ita ɗaya bayan tare suka samar da abinda aka haifa ko za a haifa ɗin, yana daga cikin karamci da kyautatawa tare da soyayya namiji ya shiga dumu-dumu a yi komai da shi, hakan na qara ma ma'aurata fahimtar juna da so da tausayi, sai kiga aure ya dad'e ba fad'a ba yaji bare kai qarar miji gida"

Innarmu gyada kai kawai take yi dan kuwa gaskiya Jabeer ya faɗa ,  amma fa gaskiya ita kunya suke bata, shiru ta yi kawai bata ce komai ba, Jabeer ne ya kammala gyara wajen ya tallabe Juwairah suka fita tsakar gida, kujera ya bata ta zauna ya fita wajen Innar mu ya deb'o ruwan zafi, ya shigo da shi cikin babban bokiti, ya raba biyu, ɗaya a babbar roba ɗaya na wanka, kai mata ya yi ya koma d'aki ya dakko ruwan kal fari ya zuba kamar murfi uku a ruwan da zata zauna din, ya je ya fara tayata wankan,cike da shagwab'a Juwairiyyah ta ce,

" Yah Jabeer dan Allah ka bari zan iya yi da kai na,Innarmu fa na nan, ta yi shiru ta kyale mu ne  amma na san ba zata so ganin hakan ba,na san akwai fahimta a tsakanin mu da ita amma wani lokacin yawan zaqewar ka zai iya jawo min qiyayya wadda bana fata, ka je zan iya da kai na na gode, ina son ka da yawa"

" ke ba abinda zata gani kar mu b'ata lokaci, maza bari na gama maki kan ta gama da Babyn mu ki ka sani watarana ba a gaban su Zaki haihu ba za mu yi rayuwa a inda daga ni sai ke kawai kin ga dole ai ni zan yi maki ko?, ya kamata ma muje asibiti a duba ki duk da na ji Innarmu ta ce ba ki samu wata matsala ba"
Chapter 47 · 0% Book details