Sashe 2
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Eh na miji Allah ya bani, me za ki yi, me zai faru? Me ya sa ba zaki yi hakuri kema Allahn da ya bani ya baki naki ba ,ai ba wai ya manta ki bane kema in ki ka yi hakuri watarana samu za ki yi,dan haka ku fita min a d'aki tinda ba arziqin yi min sannu ne ya kawo ku ba"
Gaba dayan su shewa su ka ɗauka sannan suka tafa kamar wasu 'yan daudu Goggo ta ce,
"Hahaiiiiii Cassssss, eh lallai ne, kinyi d'a na miji na gani tabbas, shine ya sa zaki fara min kitifi ko Balki ? to bari na baki wani labari, a da kam na damu amma a yanzu wani tinani ya wanken damuwa ta tass, Shi Uban yaran me ya ke da shi, me ya tara da zan damu raina akan haihuwar d'a namiji da girma na haka? Bayan ga 'Ya'ya mata Allah ya bani na zuwa Abuja ? Ki kalla da kyau duka Yarana kowanne namiji mai lafiya ya gansu sai ya yaba, dan haka bama zan bar labarin nan ya kwana ba"
Bakin ta suwaibah ke son rufewa tare da faɗin " Goggo ki bari ba yau ba kin sanar da su in komai ya kankama, ko kin manta halin yan baqin cikin ne? Se a shiga malamai a hana lamarin faruwa ai"
"A'a Suwaiba banni na fada masu su ji duk wani d'an baqin ciki se dai ya mutu, yarana guda biyunnan sun samu mazajen aure mazauna Abuja, dan haka sai ka bude kunnen ka kaji, zan basu izinin su turo magabatan su a zo ai komai nan kusa ba da jima wa ba"
Abbah Baballiya ne ya ce
"Hhmmmm Sarai kenan wato kece ma mijin yau ni ne matar ko? Umarni kk ban akan za su ce mazajen da za su aure su turo ko? Ba bincike ba komai kawai su turo, to bari ki ji na fada maki zan ba 'ya'yan ki mijin da suke so amma komai yaje yazo ki kuka da kanki kina jina ko? Fitsararriya mara kunya mai raina mijin ta a gaban 'Ya'yan ta dan su koya suma"
Ranshi a bace ya ke sanda ya yi maganar kawai se ya matsa kusa da Maman yana ci gaba da bata naman a baki
Shewa Saudat tayi tace
"Ikon Allah wai na kwance ya faɗi"
Dariya Suwaiba ta yi ita da Salma suka tafa har da uwar tasu suka fice suna dariya, can qasan maqoshin Goggo balki kuwa kishi ne damfare, kada kai ta yi a ranta tace,
'Kun yi ku gama da 'ya'yana sun tafi ABUJA aure kashin ku ya bushe a gidannan'
A kwana na bakwai da haihuwa aka yi suna yaro ya ci sunan Ammar kyakkyawa da shi sak mahaifin shi,ba wani taro aka yi ba da yawa saboda babu abin hasafin, ba qaramin so da gata yake samu ba a wajen iyayen shi da yayar shi Juwairiyyah ba, zaune suke a shimfidar tabarma a tsakar gidan inda ya sha shara ko ta ina yayi fes da shi ta na masa wasa kamar ya na jin ta, can cikin d'akin su kuwa qamshin turaren wuta na tsinke ne ke tashi, Sallama Abban su ya yi ya shigo jikin shi a mace, amma dik da haka sai da ya yi masu Juwairiyyah wasa ya sumbaci Ammar ya shafa kan Juwaira sannan ya shiga cikin d'akin Goggo Balki, kwalama Juwaira kira ya yi yace ta kira mishi Goggo Sarai.........
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 2:
Juwairiyyah bata b'ata lokaci ba wajen isar da saqon Abbahn nasu a wajen Goggo, da kyar ta amsa mata sannan Juwairiyyah ta koma bangaren su,da isa da qasaita Goggo Sarai ta shiga parlourn Mama,hakan ne ya sanya Abban murmusawa duk da cewa ranshi na matuqar quna game da abubuwan da take yi mishi.
"Sarauta kenan yi ki qaraso mu yi abinda zamu yi na fita sallah ko?"
Qarasa shiga ta yi tana hura hanci ta zauna a gefen hannun shi na dama, inda Mama Bilki kuma ke zaune a gefen shi na hagu, cikin wani irin yanayi mara misaltuwa ya buɗe baki ya fara magana,
"Da farko dai zan ma Allah godiya daya kawo min wannan rana da nake ta buri, duk da cewa ta zo min a bazata kuma ba a yanda na so zuwan ta ba, amma dai Alhamdulillah,a yau ne manema auren yaran nan su Suwaiba, Saudat da Salma suka zo, kuma mun karbe su a gidan Yaya Balarabe cikin aminci da mutunci, inda suka damqa mana dukiyar auren yaran, Suwaiba kudin sadakin ta da na gani ina so da kudin da zata hada lefe dika, an bamu million huɗu da dubu ɗari biyu, sai na Saudat Ita kuma Million biyu da dubu ɗari bakwai, a gaskiya na so na qi karba saboda kudin sunyi yawa, kamar wasu wanda zamu saida 'ya'yan?....... "
A hargitse cikin damuwa da jimami Goggo Sarai ta ce,
"Abban su ina fatan dai baka yi mana baqin ciki irin na iyayen zamani ka sa an rage kudin nan ba?"
Cikin ɓacin rai Abbah ya kalle ta ya ce,
" Amma dai na rasa me yasa baki da d'a'a Sarai? Ya ina magana ban qarasa ba zaki katse ni? Har kina ikirarin zan ma 'ya'yana baqin cikin iyayen zamani? Anya rayuwar da kk ɗora yaran nan akai za ta ɓulle da ku kuwa? Gaba ɗaya kin sa tarbiyyar yarana ta zamo a lalace? Kin raina ni baki ganina da qima da mutunci? Kedai harka in ba ta kudi ba baki san komai ba? Na gode Allah da yasa ina iyakar qoqarin riqe gidana ni Baballiya da ke kam na san da karuwanci zaki saka 'ya'yana yi su na kawo maki kudi, haba, bai ishe ki misali ba akan Balki da 'yar ta guda ɗaya tilo? 'Yarta ɗaya amma ta tsaya wajen bata ilimin addini dana zamani daidai iyawar ta, ke kuwa in ba Salma ba da ta yi sauka yarannan biyu ba zasu iya bude qur'ani su yi karatu mai kyau ba, Salman ma gashi nan ne dai kawai, to ina mai maki nasiha da kiji tsoron Allah akan abinda kk yi, ina jiye maki ranar kuka, ranar dana sani, ranar ni 'yasu,........ "
Da sauri ta d'aga masa hannu ta na yatsine ta ce,
"A'a faaaa, bafa zaka sani a gaba ba kana min mugun fata da kuma maganganu na nuna baqin ciki qarara a wannan al'amari ba, 'Ya'ya dai nawa ne, nice na yi naqudar su na haifa abina, ba wanda ya taya ni lokacin da nake qafa ɗaya a lahira, d'aya a duniya ko akwai? Dan haka sai wanda naga damar su aura sannan zasu aura, nifa takura ce bana so tammm, yanzu ka bamu kuɗin lefen da na sadakin dan musulunci bai yarda kowa ya taba dukiyar auren yara ba sai su ehe"
"Hmmmmm Sarai kenan, ke kaɗai ai ki ka yi cikin su ki ka haife su ba da ni ba dole ki ce yaran ki ne ke kaɗai,to bari kiji iya kuɗin lefe zan baku, sauran kuwa sai sanda akai auren su zan baki su,wai da ke a taki qaramar kwakwalwar sai na dauki wannan maqudan kudin na baki dika? Haka kawai aje wani abu ya faru bana fata ba ai aure ba ku barni da biya da tashin hankali? To bazai yu ba"
Bala'i ta miqe tana zazzagawa son ranta ita sai an bata kudin, tashi ya yi ya kad'e rigar shi ya fice dika a gidan, daidai lokacin da Mama Balki ke cewa,
" Ubangiji ya sanya alkairi da albarka, Allah ya kare dukkan abinqi ya basu zaman lfy"
"Hahaiiiiiiiii Cassssss, ni zaki wa bariki Balki? Zuciyar ki cike da baqin ciki amma wai kk addu'a mai daɗi irin haka,to dama dai ba daga bakin ki ta fito ba dana ce ameen"
Sa kai ta yi ta fice ta shiga madafin su ta hau aikace2, tana yi tana masifa kamar wadda ta zautu, yaran ne suka dawo daga yawon tazubar din su da sunan Islamiyya suka tarar ta na masifa, tambayar ta Saudat ta yi da cewa,
"Wai Goggo me ke faruwa ne gaba daya muryar ki har qofar gida ana jiyowa"
"Ba ni da wannan sallamammen uban naku ba ne, an kawo kudin auren ku sun riqe shida Balarabe, to ni ba zasu nuna min isa da iko ba, sai sun kawo kudin nan dika"
Cikin qasa da murya Suwaibah ta ce,
"Goggo kwantar da hankalin ki tashi mu shiga ciki ki gani"
D'aki suka shiga ta d'akko mata maqudan kudi a jakar ta ta zube mata su a saman gado, tsabar razana da ganin yawan su se da Goggo tai baya dafe da qirji ta na zaro ido,
"Suwaibah waya baki wannan kudi haka me yawa?"
Fari ta yi farrrr da idanun ta kafin ta ce,
" Alhaji Salihu mai tumbin Nera kk ji Goggo, cewa ya yi ga su ko zan qara wasu abubuwa a lefe yaso bayar wa a can wajen karbar sadakin se ya fuskanci za a iya cewa sun yi yawa, shi kuma yana ganin ko nawa ne zai iya kashewa ya samu yar zumar shi"
( Sunan da yakan kirata kenan lokacin watsewar su) dariya Saudat ta yi ta ce,
"Aaaaa kice Adda Suwaiba Alhaji ya ji zuma yau"
Dariya suka yi dika har uwar tasu suka tafa, baqin cikin ma da take ciki tuni ta manta da shi, ba sallah ba salati suna nan zaune ana maida yanda akai da yanda za ayi.
**************************