← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 61

Sashe 61

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dariya suka sanya Salma ta ɗauki pillow ta wurga wa Saudat ta na cewa,

"Addah Suwaibah kin gan ta ko?"

Murmushi kawai Suwaibah ta yi hankali ya game jikin ta a yanzu bata cika hayaniya ba sam.

Jabeer ne ya yi sallama shi da Farouq da sauri Saudat ta miqe ta na wani yanga, Jabeer na shiga ya sauke idanun shi akan Juwairiyyah da ta riga shi kafe shi da nata idanun tin shigar shi parlourn,

"Ni ma ina baby na take? "

Cike da jin daɗi Juwairiyyah ta isa gare shi ya rungume ta sannan ta ce masa,

"Gani nan yayana, ya na ga kun ɗauko car keys sai ina?"

"Wai da fita muke dan so mu yi da ku tinda wancan baban yaran ya deb'i yaran shi sun fita suma"

Kallon juna matan suka yi dan kuwa sun so su tafi shopping ɗin su su kaɗai su sai abinda suke so, dariya suka sanya a tare Jabeer ya bi su da kallo ya ce,

"Lafiya?"

Da sauri Juwairiyyah da Salma suka ce,

"Babu komai,"

Sun yi haka ne dan hana Saudat faɗan abinda suke shirin yi, yanzu ita ce ta ɗauke halin Suwaibah na surutu, Farouq ne ya ce,

"To Babban Yaya a saki madam ta d'akko hijabi mu wuce ko?"

Dariya suka yi suka tafa, sannan Juwairiyyah ta wuce d'aki ta yi shigar ta ta Ninja in ji cewar Saudat, dan kuwa hijabi dogo take sanyawa da niqabi ba ruwan su da wai sun yi kuɗi yanzu bari a saka matsattsen kaya sannan a yafa siririn gyale, ko zata saka mayafin to fa kayan ta na da wadataccen ɗinki ba a matse yake ba.

Suna gama shiri Juwairiyyah ta kira mai aikin ta Huda ta ce ta dafa mata doya irin yanda take dafawa kafin su dawo ta na da miyar taushen ta a fridge dumamawa kawai za ta yi ta yi masu sakwara da sun dawo.

Motar Jabeer Suwaibah ta shiga suka nufi ShopRite, wanda da kyar Suwaibah ta saki jikin ta saboda tunawa da baya da ta yi yanda suka dinga kashe kud'in haram a ire-iren wuraren nan.

Bayan sun kammala siyayyar su ne suka tafi shan ice-cream,anan suka kirawo Ibraheem ya zo da yaran, su na gama sha kowa ya yi wa dan uwan sa sallama ya kwashi iyalin shi suka koma gida.

Haka rayuwar su Suwaibah, Saudat, Salma, da Juwairiyyah ta ci gaba da tafiya cikin farin ciki da tarin nasarori tare da albarkar rayuwa, Juwairiyyah da Jabeer basu taɓa nuna wa Suwaibah Abrar 'yar su bace ko su nuna suna son su karɓe ta, lokuta da dama ma Suwaibah ke haɗa Jabeer da ita idan ya je gaida su Innarmu aka yi sa'a ana masu hutu sai ya tafi da ita da an gama hutu ya dawo da ita gida,ita kan ta yarinyar ta na jin daɗin samun iyaye har guda huɗu dan kuwa har gori take yi wa wasu yara,ta san Juwairiyyah ce ta haife ta amma kuma Suwaibah ita ce Mommyn ta, rayuwa suke yi cike da fahimtar juna da soyayyar 'yan uwantaka, gaba ɗayan su sun kama sana'a duk da Jabeer ya ce tun da haihuwa ta yi jinkiri ma Juwairiyyah zai maida ita ta ci gaba da karatun ta, da jin haka Farouq da Ibraheem suka ce suma za su maida matan su karatu, karatu ba ya hana sana'a da kula da iyali, Alhaji Salihu kuwa ya ce kasuwanci kawai Suwaibah za ta dinga yi dan kuwa da kan ta ta ce bata son yawan shiga mutane saboda gudun kar watarana garin surutun ta ta bada labari rayuwar ta ta baya.

Tarbiyya da sanin ya kamata sun wadatu a gidan Talle sakamakon sauke girman kai da suka yi suka koma islamiyya baki ɗayan su, dan kuwa yanzu Talle ya zama babban mutum har ya na yi wa wasu wa'azi musamman ta hanyar basu misali da rayuwar shi.

Saudat da mijin ta, sun fawwala ma Allah dukkan lamuran su game da rashin haihuwa suna ta baza soyayyar su kamar sabbin aure.

Alhamdulillahi anan na kawo ƙarshen labarin mu mai suna 'YAN ABUJA,kuskuren da na rubuta a cikin shi Allah ya gafarta min ya shafe shi a rubutu na da zuqatan duk wanda suka karanta,Allah ya sa wannan rubutu ya zame min sadaqatul jariya ko bayan babu raina, Allah ya yi wa dikkan masoya na masoya littafai na gafara da rahama da albarka.

Thank you so much my beautiful mutanen kwarai masu albarka.
Allah ya albarkaci rayuwar mu baki daya

*DAGA TASKAR HAERMEEBRAEH*❤️

1- WATA UWAR

2- 'YAN ABUJA

3- 'YAR RAWA

4- KALAN DANGI

5- DA SANIN SU

6- KAI NE JARUMI

7- MIJIN YA TA KO MIJI NA

8-  KUN MAKARO

9- MAHWISH

10- MAHREEN

11- BIYAYYAH

12 - A GARIN MU

13- DAGA TUSHE

14- MUGUN MIJI

15- MUGUN HALI

16- KYAKKYAWAR FAHIMTA

17- MAZAUNA GIDA

18- ALBASA BATAI HALIN RUWA BA

19- TAUBASHI

20 - ALMAJIRI NA

21-  AURI SAKI

22- SANADIN FYAD'E

23- RIKICIN KISHI

24-  AND NOW............

SHARHIN ASIYA HABIBU

Duk littafan nan na karantasu,kuma babu na Bari a cikin su wlh,saboda ko wanne Yana dauke d darrusa da ilimin daya shafi rayuwar duniya data lahira da kuma zamantakewa

Yan Abuja ya nuna mana illar kwadayi daga bangaren su suwaiba,ya nuna mana illar sakawa Yara dogon buri a rayuwarsu daga bangaren goggo
Ya nuna mana bangarori na zamantakewar aure tun daga gidan mama bilki har izuwa gidansu juwairere mun ilmantu da abubuwan gyaran jiki fannin iya tattali da kuma mace tazama me hikima

Taubashi y nuna mana illar barin sakewa sosai tsakanin cousin saboda komai na iya faruwa a tsakani (na dauki wannan ilimin kwarai d gaske)

Biyayya ya nuna mana muhimmancin yiwa iyaye biyayya akan abunda suka bamu umarni akai,domin duk dadewa zamuci ribar hakan

Kaine JARUMI ya nuna mana illar hassada sannan kuma y nusar damu muhimmancin zumunci

Mugun miji ya nuna mana halin wasu mazan mugaye irinsu abashe🙄🙄mazan da basa kishin matan su kuma basu dauki Mata wasu abun darajawa BA a rayuwarsu,daga karshe kuma suzo suna nadamar hakan

MAHREEN bantaba karanta littafin da komai na cikinsa y kasa barin zuciyata BA kamarsa wlh,na Jima kuma ina jinjina abubuwan d suka faru a cikin SA,
Hakuri
Juriya
Jajircewa
Addua
Kawaici
Zamantakewa
Komai de ya hada
Hakuri da duk Abinda Allah y jarrabeka dashi,d kuma hakuri d duk Abinda y sameka
Yarda d qaddara da karbar ta adik yanda tazo maka
Addua mahreen bata taba karaya BA wajan kaiwa Allah kukanta akan duk halin da ta tsinci kanta ta kasance me neman taimakon Allah akan duk halin data tsinci kanta
Takasance jajirtacciya kuma me tsayuwa akan raayinta me kuma bayyana gskyr ta ko a gaban waye bata taba kasa fadar gskyr Abinda yake ranta ba❤️.
Chapter 61 · 0% Book details