Sashe 51
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni bari naje na shirya zan wuce Abuja yau dan zuwa qarasa shirye-shiryen komawar mu bayan suna"
Anan ne ya sanar da su komai game da aikin da ya samu a Abujan, murna suka taya shi , da fatan alkairi suwaiba da saudat har ma da Salma suna jinjina iko na Allah, ko da suka auri mazajen da ke son su kuma masu kuɗi ba wadda ta taɓa samun irin kulawar da Juwairiyyah ke samu, gashi kuma yanzu Allah ya nufa ashe ita ce asalin 'YAR ABUJAN gasken,wanka ya shiga ya yi, ya dawo d'aki ya wuce su dan ya shirya,Juwairah ce ta tashi taje wajen shi ta zauna a gefen gado yana shiryawa suna hira tana haɗa masa kaya a jaka, duk da hana tan da yayi sai da ta haɗa masa, bayan ya gama ne ya dauki Abrar ya mata addu'a tare da sumbatar fuskar ta, sannan ya haɗe babyn da maman ya rungume, a bakin kofar fita daga d'akin su zuwa parlour suka gama Sallamar su ya yi wa su suwaiba sallama ya fita, bai jima da fita ba ya yi mantuwa dole ya dawo dan daukar mantuwar da ya yi,
" Af nayi mantuwa"
" Me ka manta honey?"
Matsawa ya yi kusa da ita ya janyo ta jikin shi yana mata kallo qasa-qasa cikin sauri da gane mantuwar da ya yi Juwairiyyah ta hau ja da baya ta na son kwace kan ta a hannun shi ta ce,
"Yah Jabeer ka bariiii su Addah Suwaiba na nan fa, ni dai dan Allah ka daina bani kunya a gaban mutane,"
Ta qarasa faɗa tana 'yar kwallar ta dan ya kyale ta, lakece mata hanci ya yi yace,
"Ina baki kunya fa ki ka ce? Ai shikenan mun kusa komawa gidan mu mu uku, mu yi abinda muke so ba tsoron zan kunyata ki a gaban mutane ko?"
Dariya ta yi na samun nasara akan shi ya hakura da yin abinda ya fake da mantuwa ya dawo domin sa, Juwairiyyah ta yi masa addu'a ta rako shi suna zuwa palour ta yi fuska ta zauna kamar ba tare suke ba, kunya ce da ita kamar me shi kuma duk abinda zai yi matsawar bai saɓa wa shari'a ba babu ruwan shi kowa ma ya gani, meye abin jin tsoron kar wani ya ga ya na kyautata wa matar shi? dariya suke yi mata Salma tace,
" kin ji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa, mu zaki layancewa?"
Dukan wasa ta kai wa salman tace,
" Adda Suwaiba kin ganta kooo"
Dariya suka yi, suwaiba ta ce,
"Juwaireren Mama ya kamata ki rage shagwab'a yanzu kin haihu," Nafee ce ta fashe da dariya,ita kuwa Juwairiyyah sai ta murguda mata baki sannan ta kauda kai, ranar a gidan Juwairiyyah su suwaiba suka wuni da yamma Suwaibah ta yi wa Juwairiyyah wanka, nan take Juwairiyya ta ce wankan ta ya fi na Jabeer daɗi ta dinga yi mata ko da ya dawo.
*******************************
Ahj Salihu ya iso kano lafiya, da kyar ya gane gidan su suwaiba saboda ko a da ba su zuwa zance gidan su sai dai su su suwaiban su je hotel su same su a can,a qofar gidan su ya tsaya.......
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 30:
Jingine yake a Jikin motar da ya je da ita saboda rasa ɗan aike da ya yi,bayan haka Alhaji Salihu yana matuqar jin nauyi, kunya, da tsoron wacce Karb'a za a yi masa a gidan su suwaiban,juyawa ya yi ya kife kan shi a Jikin motar ya na fidda wani irin numfashi wanda ke nuni da halin damuwar da yake ciki.
Mai adaidaita sahu ya na ajiye su ta gane mijin nata,domin kuwa da shi take kwana da shi take tashi a ran ta, Alhaji Salihu kuwa na nan tsaye wasu siraran hawayen nadamar rayuwar shi ta baya na bin kuncin shi, ga rashin babban aboki kuma ɗan uwan shi da ya yi, a gaban shi zakin nan ya kaiwa Oga Zaks cafka a wuya, da sauri ya d'aga kan shi cike da damuwa ya ke tunanin yanzu me zai faru idan Shima zakin ya biyo shi har nan dan ya hallaka shi?
Anya hakan ba zai jawo wa Suwaiba da iyayen ta da 'yan uwan ta matsala ba? maybe this is a bad idea for him to risk there life for his mistake,juyawa ya yi dan ya bar wajen cikin gaggawa kafin wani ya gan shi, cikin wata iriyar murya mai cike da shauqi da kewa ta kirawo Sunan da take Kiran shi da shi,
" Baby ! kai ne a qofar gidan mu da gaske? Me ka ke yi a nan?"
Qarasawa ta yi da gudu ta faɗa qirjin shi tana kukan kewar shi da ta yi, shima rungume ta ya yi kamar wani zai k'wace masa ita, gyaran murya Salma ta yi masu ta ce,
" Adda a waje kuke fa kin san halin mutanen mu, ba za a yi tunanin mijin ki bane za a fara qananan maganganu mu shiga daga ciki "
Janyewa suka yi daga yanda suke ta ja hannun shi zuwa cikin gidan su ta tsaida shi a soro, Saudat kam ta qame qam a wajen, dan zuciyar ta bugawa kawai take yi, ina nata mijin yake? Ya aka yi suka rabu yau bata gansu a tare ba bayan ta san ba sa rabuwa?
Wannan tambayoyin Salihu ne kawai zai amsa mata su bayan ya samu nutsuwa, dan ta kula shima ba a nitse yake ba, Salma da ta yi gaba ne ta dawo baya ta ja hannun yayar ta ta suka yi cikin gida, ta kula da cewar Saudat na cikin damuwa tin safe yanzu kuma data ga Salihu shi ɗaya ba nata mijin damuwar ta ta qaru akan ta da, ko ba komai tana son mijin ta kawai halayen shi ne yasa ta gudowa ta qi komawa gare shi dan ba zata zauna a kashe ta a banza ba.
Sun riga da sunyi Sallahr la'asar a gidan Juwairah dan haka bayan sun shiga sanar da Baban su suka yi zuwan Alhaji Salihu ga kuma a yanayin da suka gan shi a ciki, da fari Baba ya hasala ganin rashin kunyar Alhaji Salihu na zuwa gidan shi bayan abinda suka yi wa yaran shi,da suka samu ma bai kai ƙarar su ba shi ne har zai zo to ya ce musu me? amma da Mama Bilki ta taushe shi sai fushin nashi ya sauka, ta shawarce shi da ya tafi cikin nutsuwa ya buɗe ma Salihu zuciyar shi ya ji me ke tafe dashi, in yazo da rainin hankali gidan su yazo duk abinda Baba ke so zai iya yi masa ya huce haushin shi, ta bashi goyon baya ya yi masa duk abin da yaso, kad'a kai ya yi cikin qunan rai ya fita amma sai ya danne bacin ran nashi, kamar yanda matar tashi ta bashi shawara.
Sallama ya yi masa ya miqa masa hannu dan su gaisa,amma sai Alhaji Salihu ya noqe ya qi miqa nashi hannun ya durqusa qasa yana mai sakin kuka mai ban tausayi tsakanin kukan shi ya fara magana,
"Baba ni mai laifi ne babba a wajen Allah da kuma ku, babban mai zunubi ne ni Baba,na taso ban san menene ilimin addini ba, duniya kawai na saka a gaba, bani da ilimin addini daya ratsa zuciya ta da zai hana ni aikata dukkan abubuwan dana aikata a baya, dan son ka da Allah da Annabin shi ka yafen abinda na yi wa Suwaiba, ka yafewa abokina d'iban jini da cire wa Saudat mahaifa da ya yi domin ya mutu a yau, a dazun nan ta hanyar hatsarin mota"
Wani qara kunnuwan saudat suka ɗauka shuuuuuu, tabarmar da ta d'akko dan ta kawo wa Alhaji salihu da ruwa a jug ne suka zube a qasa, kafin ta qara d'aga qafar ta ta isa wajen su Baba ta yanki jiki ta faɗi, da gudu Baban su ya yi kanta, ya d'aga ta ya yi ya shige ciki da ita, ruwa suka yayyafa mata ta sauke ajiyar zuciya mai karfi daga nan kuma a hankali ta fara buɗe idanun ta,a kan Alhaji Salihu idanun ta suka zuba wanda ya shiga gidan ba tare da izini ba dan ganin halin da matar abokin nashi ta shiga, kuka ta saka ta kai masa wani wawan naushi a baki tare da fad'in ,
"Mugaye azzalimai kawai, wato kashe shi kuka yi ko? Dan na san yanda Kalla ke sona zai biyo bayana ko bajima ko ba dad'e, shine kuka kashe shi saboda ba ku son ya bar azzalumar ƙungiyar ku ya zo gare ni,"
" Saudat ya kamata ki natsu,abinda ki ke zargi ba shi bane ya faru,ni da ki ka ganni ni na shawarce shi akan mu fita daga qungiya dan son da muke maku, da kuma tsoron Allah daya shige ni a wannan lokacin, amma Kalla ya qi ya mun bayanin shi akwai sauran lokacin tuba ba zai fita ba, na masa nasiha da in mutuwa ta riske mu kan tuban fa, yace akwai lokaci, yana fita ya yi hatsari mummuna, kan shi ya fashe qafarshi ta......."
" Stop it ! Stop ! Ba na son ji..bana so..bana son ji"
Fashewa da kuka ta yi mai ban tausayi, a nan dai Alhaji Salihu ya qarasa labarta masu komai daya faru har da shugaban qungiyar tasu wato Oga Zaks.