← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 61

Sashe 4

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

An saka ranar auren su gaba ɗayan su nan da wata ɗaya, gori kam da baqaqen maganganu ba irin wanda Juwairah bata karb'a a ba wajen 'yan uwan ta, tin tana kuka har ta kai ta daina sai dai ta kauda kai su yi tayi ranta na quna, takan ji kamar ta ce Ya Jabeer ya fito ayi auren su tare amma ba za ta iya ba saboda kunya, kuma ko ba komai ai shi ne namiji shi ya kamata ya fara magana.

Wata rana ta na zaune tana yanka alayyahu wa Maman ta sai Adda Suwaiba ta fito ita da Salma,a tare suka kalli Juwairah suka sheqe  da dariyar shaqiyanci sannan Salmah ta ce wa suwaibah,

"Hhhhhhh Adda dan Allah ki ga yarinyar nan, a kyau dai duk gidanan albarka tafi kowa, amma wai ta tsaya ta mori kyawun na ta inaaa ba rabo, ta tsaya ta na yi wa kanta baqin ciki da mugunta , ban taba ganin irin wannan yarinya ba"

Suwaibah ce ta yatsine fuska kafin ta ce,

"Hhmmm ina ruwan ki uwar kinibibi taje ta auri wanda ta gadama ma ba Jabeer ba, danni bari ki ji, ba kyau ba, ba ilimi ba, in dai baka da farare bugun Abuja, sannan ba zaka aure ni ka kai ni Abuja ba kayi kyawun banza da kyawun halin wofi, dan ba su zan ci ba ah toh, ai ka auri me nera wanda za ka ci me kyau ka sha me kyau ka kwanta a qaton gida mai kyau shi ne magana"

Tafawa suka sake yi su na dariya tare da riqe baki kamar wasu 'yan daudu su a dole sun ma ta rashin mutunci, girgiza kai Juwairiyyah ta yi tace

" Adda Suwai kenan, ina kyautata zaton kun manta wa keyi, sannan kun manta dawa kuke jayayya, wanda duk zai wa wani gorin talauci to ya sani ba da wannan bawan yake ba da ubangijin bawan yake yi, bayan haka ba fa kusan sana'ar mazajen ku ba gaba ki dayan ku damuwar ku kawai a kai ku Abuja, ku kawai matan Abuja ne, matan manya, bana maku baqin ciki, zanfi murna ace kuna gidan hutu dan nima ina ma kaina fatan hutawa, amma zan baqin ciki ace baku da alkibla saita kudi da son abun duniya, Allah ya kyauta, ammmm for ur information, ni haka nake son Yah Jabeer ba dan dukiyar shi ba ba dan komai ba , Son shi ni kaina ba zan ce ga daga in da ya fito ba, na tsinci kaina ne da So da qaunar shi tun kafin na san menene so da qaunar kan su,dan haka wannan matsalar ku ce wai rashin kudin shi, tinda ya zama jinin jikina ba zan iya rayuwa ba shi ba kun ga ko ko a wanne hali yake zan iya zama da abu na mtwss"

Tafi ta ji ana yi mai cike da shauqi idon Jabeer tap kwallar dad'i da murna da farin ciki, Mama na d'aka tana mamakin yanda 'yarta ta ta iya zaro magana haka, lallai yau an kaita maqura kenan, Juwairiyyah ce ta d'aga kai ta ga Jabeer yana qarasowa gaban ta, wata irin kunya ta ji ta lullub'e ta da ko guduwa daga wajen ma kasawa ta yi, dan tinda suke bata taba zayyane masa yanda take son shi ba se dai ya na ganin alamu, kafad'un ta ya riqe ya juya ya kalli su suwaiba, inda suka qame qam suna wurga idanu alamun rashin gaskiya dan kuwa ya musu zuwan bazata, shi kan shi be san zai zo ba ya na komawa gida ne ya yi tunanin ya gan ta shi ne ya biyo,murmushi ya yi ya ce,

"Princess wad'annan kalaman naki sun qara dasa man zazzafar qaunar ki da son ki akan na da, ba zan iya rayuwa ba ke ba nima, dan haka nake roqon Abba da ya taimaka ya aura min ke nima a haɗa gaba ɗaya da na waɗannan fitsararrun marasa tarbiyyar, ba dan komai ba sai dan a kafa tarihi an yi auren ku tare kar muzo lissafi yana kwace mana Ko ba haka ba Suwai?"

Murguda baki Suwai ta yi ta na qunquni ta wuce d'aki, tsugunnawa Jabeer ya yi a gaban Juwairiyyah ya ci gaba da taya ta aikin yanka alayyahun,ita dai kunya ta ishe ta a haka suka gama yiwa mama girki ko leqawa gaida maman bai ba ita ma Maman ta kasa fitowa dan komai akan kunnen ta aka yi, Abba ne ya shigo da sallama bayan sun amsa ne yace,

" A'a Juwaira !Jabeer ! yau kune kuke mana abincin daren? "

Ya faɗa cikin dariya, sosa qeya Jabeer ya yi ita kuma Juwairyyah ta rufe fuska ta je ta amshi ledar hannun Abban, ta yi d'akin Mamar ta da shi, ta na shiga ta ga dakin ya sha gyara har da qamshin tiraren wuta irin na tsinke, Maman ce ta zo ta wuce su da ruwa a bokiti kanta a qasa dan yau dai yaran sun bata kunya sosai, Jabeer ya na dariya yace,

" Hajiya Maman mu yau kuma kunya ta kk ji ne? Shi yasa sai yanzu ki ke fitowa da kk ji Abba ko? Ai dana sani to tafiya na yi da muka gama hirar tamu"

Soson hannun ta ta wurga masa ta ce,

"Wannan d'anneman tsokannen dole se ya sa ni  magana duk kauda kaina da na ke yi wato dai sai ka nuna min kai ɗan zamani ne ko? Ai gashi kun ja min makara yin wanka sai da Abban nasu ya dawo"

Dariya suka yi dikan su, Abban ne ke tambayar me ya faru ne, da hanzari  Juwaira tace,

"Ba...ba..komai Abba hira kawai ake yi"

Dariya Mama da Jabeer sukai Mama ta wuce su Jabeer ne ya ce,

"Abba ka huta akwai magana a bakinnan nawa mai mahimmanci, ni dai in ke ba ki da abin cewa ni ina da shi yarinya,"

Roqon shi take da ido akan ya bari sai gobe yau kunyar zata mata yawa, amma se ya kanne ido ɗaya yana mata gwalo, shi fa ba ruwan shi sai ya faɗa a yau, tura baki ta yi ta wuce daki, bayan sun gama komai taa yi wanka sunci abinci, in da wajen cin abincin ma Jabeer rashin ta ido ya so yi ta qi bashi haɗin kai, wai shi da sai dai suci a kwano daya, da taqi sai ya zauna kusa da ita, in ya faki idon kowa sai ya zura hannu a nata ya d'iba ya kai bakin shi yana lumshe ido, can sai yace,

" Ke ni fa ban yarda ba ya akai naki ya fi dad'i? "

Cikin muryar shagwab'ar da ta zame mata jiki ta ce,

"Kai Ya Jabeer da rigima kk, ni duk d'aya ne kai ne  dai ka ji haka"

"To kawo mu yi canjen kwano in dai  ki na da gaskiya baki qara komai a naki ba"

Miqa masa nata ta yi ya bata nashi suka ci gaba da cin abincin su, can ya qara zura hannu a wancan da ya bata, ya debo  ya ci har ya na wani lumshe idanun shi ya Kalle ta ya ce,

" Tab in ba sai an qara canjawa ba me ki ke fakar idona ki ke sawa naki ne wai?"

Cike da muryar da ke nuna alamun ta na so ta yi kuka ta ce,

"Yahhhhh Jabeerrrr"

Ta qarasa tana turo baki cike da shagwaba,Abbah ne ya Kalle su ya ce,

"Wai ni da ka ke wannan maganar ta ya aka yi kasan nata yafi dadi?"

Saurin tashi zata yi daga wajen ya sa hannun shi ya danne hannun ta dole ta koma ta zauna kan ta a qasa saboda kunya,

" Abba loma d'ai-d'ai na yi a dikka kwanon na ji"

"Abbah yafi loma ɗaya ya yi"

" Hmmm Abban su dan Allah ka rabu da shirgin yaran nan mu ci abincin mu bana son kana wasa da cin abinci kar wani ciwon ya kama mana kai"

Jabeer  ne ya kashe wa Juwairyyah ido tare da matsa wa kusa da ita,ya kai bakin shi daidai kunnen ta ya ce,

" To kin ji yanda ake wa miji ko, sauran mu yi aure kina raba mana kwanon abinci irin haka"

Dariya ta gimtse, kamar daga sama suka ji muryar Goggo Sarai na faɗin,

"Hmmmmmm bariki kenan, watohar da 'Ya'yan ake zaune ake iskanci a tsakar gida, sannan in nawa yaran sun fita ace masu yan iska, to ai bahaushe yace, qazantar da baka gani ba tsafta ce"

Cikin jimanta maganar ta Abbah ya ce,

"Subhanallahi, me kk fada ne ke kuwa a gaban yara,kin wani tattaro su gaba ɗaya  kun taho, ina za ku je haka?"

" Eh abinda ka ji na faɗa mana ko maimaici ka ke buqata na qara karanto maka?"

"To bari kiji mara kunya, Jabeer ya tabbatar man da auren Juwaira yake son ya yi, yana son a haɗa dana sauran ayi baki daya kuma a rana ɗaya, dan haka wannan shiriritar taki da gore-goren taki ta tsaya haka,ya ishe ki haka, duk abinda ki ke a gidan nan ina sane da shi"

"Aiko ba wanda ya isa ya haɗa mana aure da wadannan yan maulan"

Kan suwaibah ta rufe baki ta ji duka fauuu an make bakin da qarfi, saida bakin ya yi jini, cikin masifa da bala'i Goggo ta ce,

" Kan uban nan Jabeer me suwaiban ta yi maka da zaka mata wannan dukan, ko uwar ka Hansai ba zata yi ma 'yata hukun ci ba  a gaba na balle Uban ka Balarabe"

Wani dukan ya sake  kai wa Saudat dake kusa da shi sosai mai qarfin da ya fi na Suwaibah dan kuwa sai da ta kifa ta yi taga taga za ta fadi Goggo ta taro ta, cikin ɓacin rai Jabeer ya nuna Goggo ya ce,

"Duk rashin kunyar da ki ka yi ma Abba kan 'Ya'yan ki marasa tarbiyya zan fanshe"

Salma cikin d'aga murya ta hayayyaqo wa Jabeer ta na faɗin,

"Sannu uban mu, se ka kashe mu idan ka tashi"
Chapter 4 · 0% Book details