Sashe 24
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" kaiiiii amma yar uwa na gode sosai, Allah ya saka miki da alkairi, Allah ya sauke ki lafiya, ya bamu bby mai albarka,"
Sunkuyar da kai ta yi a ranta ta amsa,
" Dalla in zaki amsa ki amsa ba ma son gulma karshe dai gaki nan ciki ne da ke dai"
" Sannu Nafeesa sarkin rashin kunya na gode dani kike wannan maganar tin da ni nayi abuna"
Cikin kad'uwa da tsoro Nafee ta hau zare ido ta na kallon ta inda maganar ta fito, gaba ɗaya ta tsorata ta kasa magana,su kuma dariya da kunya ce ta kama su musamman ma Juwairah ashe Yayan ta ya dawo su na ta surutu ba su ji ba gashi duk ya ji su.
Tashi ta yi ta ja labulen ta fita wajen shi kan ta a qasa ta ce,
" Sannu da zuwa mine"
"Yawwa princess, ya ki ke jin jikin naki yanzu?"
"To alhamdulillahi da sauqi gaskiya sosai,amma fa kaina yanajuyawa wani lokacin kuma cikina na motsawa sai na yi ta jin tsoro kuma abin na min daban haka"
"Ki yi ta hakuri kin ji princess u will be fine inshaa Allah, kawai hakurin nan naki dana san ki dashi zaki ci gaba zamu iya komai a tare Allah ya shige mana gaba"
Murmushi kawai ta yi dan kuwa ta amsa a ran ta shima murmuahin ya yi tare da sumbatar gefen kunnen ta a hankali,cikin sauri da kuma shagwab'a ta ce,
"Yayaaaahh"
Murmuahin ya sake yi mata sannan ya ce,
"Yanzu tinda shamsiyya ta zo bari na je wajen Innar mu na yi hirata nima"
Gaishe shi shamsiyya ta yi ya amsa tare da yi ma Farha wasa ya tafi, Nafeesa ta aika da abincin shi da komai da zai buqata can wajen Innarmu da kyar ta karba dan kunya da tsoron Yayan nata take ji ya kamata ta na surutu akan shi, dariya suka yi ta mata,bayan ta dawo ne ta ce,
"Laaa Matar Yayah na haɗa mana kwad'on zogalen da rama?"
Cikin tsinkewar yawu Juwairiyyah ta ce,
"Kaiii Nafee amma Allah ya yi miki albarka, dan Allah haɗa mana"
Ta shi ta yi suka fita tsakar gidan a tare Nafee na hadawa suna hira ta saka komai zata yanka albasa kenan, Juwairah ta dakatar da ita da sauri ta ce,
" Nafeesa kar ki sa mana albasa sai dai a naki dan mu muna da masu shinshinar bakunan mu kar su ji warin albasa na tashi,baki san ba a son in yamma ta yi mace ta ci albasa ba? Dan haka ki kiyaye ko dan gaba idan kin yi aure musamman idan miji na gida ki hakura da albasa kawai ,in ko kinci ki tabbatar kin wanke bakin ki tass yanda ba yanda za ai ya ji warin ta kuma ki qara da abinda zai qamsasa bakin naki"
Cikin farin ciki suka haɗa baki wajen gode mata,dan kuwa duk wanda ya zuba da ita sai ya qaru shamsiyya tace,
" Lallai zan yawaita zuwa gidannan don na samu sirrin da yasa baki taba faɗa da mijin ki ba kuma kk iya controlling din shi haka"
"Hhhh haba shamsiyya ai mace bata controlling miji sai dai ya zamar mata bawa a lokacin da itama ta zamar masa baiwa,shi kan shi na miji ba ya sanin ya zama maki bawa sai dai yaji mutane na cewa ya zama mijin hajiya, ko mijin kan tace, da sauran su, babban abinda ke jawo ma mace hakan kuwa shine, neman soyayyar Allah makadaici, in mace ta nemi soyayyar Allah, ta kuma samu, to tabbas zata samu soyayyar mijin ta cikin sauqi, wanda hakan ya yi qaranci a cikin mu mata, daga wajen boka sai dora rai akan maganin mata shi kaɗai ne maganin matsalar auren mu,bayan ba su kadai ne ke riqe zaman aure ba, wallahi in Allah ya so mace ta gama samun dacewar duniya da lahira, dan haka ni sirrina na zaman gidan aure shine son Allah da neman Allah ya so ni, saka soyayyar namiji a saman ta Allah shi ke saka mata fadawa halaka, daga zuwa wajen boka, zuwa zinace2, da dikkan abin da ya kauce hanya dan haka ina horon ku da neman soyayyar Allah kafin ta mazajen ku, sannan ba wai ba ma faɗa da junan mu bane, mu na yi, mun dai zaɓi soyayyar junan mu akan fushin mu ne shi yasa da mun yi fad'an muke shirya kammu ba wanda ya ji ko ya gani balle ya raba mu,"
Wani irin daɗi ne ke ratsa su dikkan su, musamman Jabeer da ya kawo kwanuka da niyyar yin alwala ya tafi masjid, godiya ya dinga yi wa Allah a zuciyar shi sosai da samun mace kamar Juwairah buta ya ɗauka ya fita ba tare da sun san ya shiga ba.
Suma sallahr la'asar suka yi, suka raka Shamsiyya ta hau abin hawa ta tafi, tana cike da farin cikin samun qawa kamar Juwairiyya.......
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 16:
Hannayen shi biyu boye a bayan shi ya qarasa sashen na su da ke share kwal, yashin wajen har wani zanen tsintsiyar kwakwa ya yi gwanin sha'awa, duk da cikin da Juwairiyyah ke da shi bai sa ta zama qazama ba, sanda ba ta da lafiya ba za ta iya aiki ba sai ta zauna ta huta,da Jabeer ya kula shi kuma zai taya ta, lokacin da take da lafiya kuwa zata haɗe gidan dika ta yi masa gyara na musamman.
Juwairiyyah kuwa ta sowa ta yi da niyyar mishi sannu da zuwa yanda suka saba, sai taga ya maqale a jikin gini yana mata dariya, daga girar ta ɗaya ta yi tare da lumshe su cikin wani salon daukar hankali ta ce,
"Yayana me kake boyewa baka son na ganiiii"
Kwaikwayon yanda ta yi masa ya yi sannan ya ce mata,
"Matso kusa ki gani manaaa"
Matsawa ta yi, kusa da shi sosai idan ta matsa sai yace ta qara matsawa kusa kaɗan, haka ya dinga yi mata har sai da jikin ta ya zama gaba daya a nashi sannan ya fidda hanneyen shi ta bayan ta ya rungume ta ya sumbaci kuncin ta da goshin ta, sannan ya kama ta suka zauna, miqa mata leda ya yi ya tallabe fuskar shi yana kallon ta da murmushi, bude ledar ta yi itama tana murmushi tana kallon shi tana kuma kallon ledar, tana budewa taga wayar da zata kai ta dubu sha biyar a ledar, buɗe baki ta yi cikin murna da tsalle, ta dane shi tana ma sumbatar shi ko ta ina, kama ta yai ya riqe kafadun ta sannan ya ce,
" My princess ki nutsu kina girgiza mana baby, so kike ku ji ciwo?"
" Kaiiii amma mine na gode, na gode , na gode, Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya sama dukiyar ka albarka da rayuwar ka gaba ɗaya, Allah ya jiqan iyayen ka ya sa su cika da imani"
Hannu ya sanya a Saman labb'an ta ya ce,
" Shhhhhhh wai wannan godiya haka kamar na sai maki mota?"
"Hmmmm kai ka ga bai kai na yi wannan godiyar ba amma ni na san ya wuce haka ma, kai ma kasan ina da son waya, a matsayina na wacce ba ta taba riqewa ba yau na samu ai sai godiya ko, bayan haka ma macen kwarai dole ne ko tsinke mijin ta ya kawo ya bata ta nuna masa godiya da murnar ta akan abinda ya bata, in ba haka ba ta yiwa kanta baqin ciki dan gaba ba zai ji qwarin guiwar kawo mata komai ba"
" wannan haka yake macen kwarai, macen da zata zamo daga cikin matan aljanna in shaa Allah, Juwairah in dai ta dalilin miji ake shiga aljanna na maki alqawarin na yarje maki ina fatan Allah ya karb'i roqo na ya sanya min ke a aljannah"
Wasu irin hawaye ne masu dumi ke bin fuskar ta, wanda duk ya kalle ta a wannan lokacin ya san ta na cikin tsantsar farin ciki da nishadi, ga wani sabon son Jabeer ɗin da ke ratsa ta,a hankali ta furta,
" Yah Jabeer, na gode sosai Allah ya bar mu tare , mu je aljannar tare, domin kaima ka shiga cikin alqawarin Allah duk mai kyautata wa iyalin shi zai shiga aljanna, kana ɗaya daga cikin mazan da suke koyi da halayen Annabin rahama da sahabban shi na tabbata nima Allah zai amsa addu'a ta mu shiga aljannah a tare"
Haka suka yi ta yi ma junan su dad'ad'an kalamai wanda suka tabbatar da har abada ba za su taɓa manta wannan ran mai cike da farin ciki ba.
Kusan abinda aka rasa kenan a wannan zamanin,sai ka ga saurayi zai je zance ko ta waya ya yi ta yi wa budurwar shi dad'ad'an zance kafin a yi aure, amma da anyi auren aka yi kwanaki ko watanni ko shekara ɗaya zuwa biyu ya daina kenan, itama kuma haka sai a dawo kowa na dana sanin auren dan uwan shi, auren duk da muke ganin yana dad'ewa wallahi ba sa dai na yabon junan su kamar ranar suka fara haɗuwa, kowa a kullum yana son ya fidda sabon salon da zai faran ta ran ɗan uwan shi ne, dan haka mu ci gaba da nemawa juna farin ciki sai auren mu ya yi qarko, idan ki na yi wa mijin ki ko ka na yi wa matar ka abubuwan alkhairi da soyayya bata kulawa to da wato da hikima da dabara ake nuna masu sai suma su koya, duk taurin namiji ko mace kyautatawa na karkato da hankalin su ga junan su,haka su juwairiyya suka kwana suka hantse cike da farin ciki bata huta ba sai da ta dinga kiraye kirayen waya bayan ta nuna wa Innarmu ta sanya mata albarka.
****************************