← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 61

Sashe 26

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Makaranta na taqaice maku labari a ranar nan duk wanda ya yi gangancin shiga d'akin nan nema wa su Haule taimako sai ya karɓi nashi ɗaukan,idan ta na dukan wannan wani ya shiga sai ta saki na hannun ta ta kama sabo ta daka, haka ta dinga yi kamar wata mahaukaciya, sai da ta gaji jikin ta ya yi laushi sannan ta kwanta tana kukan baqin ciki kamar wani ne ya aike ta qulla wa kishiya sharri,cikin kukan ta ne ta ke fad'in,

"Wayyoo ni Allah na Marka yau na shiga uku na qulla sharri gashi ya zame mini bala'i,na yi abinda zai jawo wa kishiya baqin jini a wajen miji ni kuma sun tattara sun wuce binni sun barni a qauyen"............
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼   ' YAN ABUJA  💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 17:

Tun da Jabeer ya sai wa Juwairiyyah waya ba su samu suka haɗu da Nafee ba sai da aka kwana biyu,domin kuwa a washegarin ranar Nafee ta tafi gidan wata qanwar Innarmu ta yi masu kwana biyu, dawowar ta da yammar ranar ke da wuya Juwairiyyah ke nuna mata wayar cike da zumud'i da murna,cikin fara'a ta amsa sallamar Nafeen sannan ta qara da,

"Wa'alaikumussalam shigo shigo yar uwa kiga me yayana ya sai min da bakya nan"

Da sauri Nafeesah  ta qarasa shiga itama cike da d'okin ganin me za a nuna mata, sanda ta gani itama 'yar qaramar qarar murna ta yi ta haye kujerar da Juwairah take tare da fad'in ,

kaiiiii amma Allah ya saka ma Yah Jabeer da alkairi, ya sai mana waya mun daina leqen ta qawaye"

"To malama ba wai an sai mana waya ba na dinga neman ta ina rasawa"

"Hhhhhh Allah baki hakuri ai wannan wayar inna ɗauke ta kema  kin San zan ririta ta, yanda kk san jariri haka zan kula da iya sai kin neme ta sannan zan miqo maki, ko kuma idan tana buqatar a sa mata kudi"

Dariya suka yi a tare sosai, sannan Nafee ta ce wa Juwairiyyah,

" Yauwa wai ni ruwan meye wancan a butar qarfe na ga kin saka a garwashi? Tunda na shigo nake jin kamshin na tashi ko shayi za mu sha ne na musamman"

Dan dafe kirji Juwairiyyah ta yi sannan ta ce,

" Oh ashe ban cire ba dama? Dan je ki sauken dan Allah ki dawo na fada maki hajiya tambai"

" Ah tohhh dole ki min bayani dalla dalla dan kin san in baki fad'an ba baki da zaman lfy yau"

Fita ta yi ta sauke mata butar ta dora ruwan wankan ta , ta koma dakin, zama ta yi tare da tanqwashe qafa agaban Juwairah tace,

" To malama a bamu darasi, dan zama dake akwai diban ilimi"

" ke ko, ke ko, hmmm kina raina sanin da Allah ya baki ne amma kin fini ilimi ai, kefa duba ki gani yanzu ci gaba da karatun ki kike yi ni fa ina zaune a gida kullum ba wani ci gaba da karatun da na ke"

" kema zaki ci gaba ne watarana komai lokaci ne sis kar ki damu,oya ina jin ki meye wancan a butar qarfe?"

Dariya Juwairah ta yi sosai sannan tace,

" ke dai ba ki mantuwa to magani ne, maganin infection musamman na masu ciki, Mama Bilki naga ta yi lokacin cikin Ammar shine nayi, Oh har naji ina son ganin yaron nan "

"To na ji magani ne amma ai baki fad'an ya ake haɗa shi ba ko"

"Haka ne, kinga dai da fari zaki samu ganyen garahuni, da 'ya'yan hulba ki tafasa su sosai sai ki bari ya sha iska sai kina tsarki da shi, da yawan masu ciki suna fama da infection sosai, mai fidda ruwa kala2, amma da zasuna amfani da wannan zai masu magani duk da ba wai yana ɗauke shi dika bane kwata2 amma yana ragewa sosai, in aka hada da wasu magungunan na sanyin ana sha, kin ga na ciki na mutuwaaa na waje ma ana kashe shi, amma idan mace bata da ciki zata iya neman sassaqen sanya,bagaruwar mata,lemon tsami, d'anyar citta,kaninfari,masoro,kimba,danyen kurkur, ganyen magarya,sai ta haɗa su waje ɗaya ta dafa ta dinga shan ruwan, ta yi na sati biyu ita da mijin ta da kishiyar ta idan mai kishiya ce saboda su yi maganin abin a lokaci d'aya, in shaa Allahu Zaki ga an samu sauqi gefe d'aya ana tsarki da wancan ruwan garahunin,sannan wannan had'in ga masu neman haihuwa in dai matsalar ta danganci infection to da yardar Allah zai wanke mahaifa a samu ciki, sai dai kuma idan matsalar ba wannan bace sai a nemi maganin matsalar,"

"Yauwa 'yar albarkan Yah Jabeer ko ke fa, ba ga shi kin qara min ilimi ba ni ina ma na san wannan abun in ba yanzu ba, yauwa rannan ma na ji kina faɗa ma shamsiyya wani abu lokacin na fita ban ji me kuke cewa ba game da warin gaba dan Allah ki yi min bayani akwai wata a department din mu ba zaki so zama kusa da ita ba sam saboda wari"

" Ohh wannan ai ta na tare ko da babbar matsala gaskiya,in ki na so ki yi maganin matsalar warin gaba dole sai kin san kala kalar shi,na farko dai akwai na lalura, akwai wanda mace da kanta take jawo wa kanta"

"Hhhhhh ka ji Matar yaya wai mace ta jawo wa kanta to kamar yaya? Kana sane kabar jiki ya yi ta tsami"

Dariya suka yi a tare sosai suka tafa, sannan Juwairiyyah ta ce,

" Allah da gaske nake yi, yanzu misali Nafee, ke ce kin tashi a rana kin wuni da pant ɗaya a jikin ki, kin je fitsari kin yi fitsari baki wanke wajen sosai ba kin maka pant kin mayar, kin yi bayan gida kin maka kin mayar, sannan da jiqar da komai ki ke mayar wa, ki fadan min shi pant din d'an uwan ku ne da zai qi yin wari?" 

Wata iriyar dariya Nafee take yi, cikin dariya ta ce,

" Whhhhhh alqur'an dole yayi wari, amma dai misalin nan dama ba dani aka buga shi ba a canja gaskiya a saka Salma"

" wulaqanci Yayar tawa, Allah sarki mutan Abuja ana can ana shan daɗi an manta da dangi"

" Hmmm ke dai bari buri ya cika, Allah muma ya sada mu da mafi alkairi"

" Ameen dai"

" To yanzu fad'an ya za ai ayi maganin wannan warin dan Allah dan akwai yar makarantar mu na faɗa maki, da kin zauna kusa da ita sai kin ji wannan warin,ni ba zan ji kunyar faɗa mata duk bayanin da Zaki yi min ba, da azo ana ta gulmar ta ko ana gudun ta ta na jin haushi ai gwanda a faɗa mata matsalar ta da maganin matsalar ta gyara ko? Wataqila bata samu iyayen da ke koya mata ba kin san wasu iyayen ba su koya wa yara su komai kin dai gane me nake nufi"

Ta faɗa tana nuna hanyar sashen Innarmu,qunshe dariya suka yi sannan Juwairiyyah ta ce

" Allah sarki, aiko gwanda ki sanar da ita, dan aboki na gari ke wayar da kan abokin shi idan ya ga irin haka na faruwa da shi,to kina ji ba,na son a rana a baki canja pant ba ki canja sau biyu, ya zama na kina da tsimma ko towel qarami a toilet din ki wanda in ki ka yi fitsari ko bayan gida zaki tsane wannan ruwan bayan kin yi tsarki tunda yanzu yawanci banɗakunan na masu da shi ne tsarin ginin za ka iya ajiye qaramin towel,sannan in kin zo tsarki ki fara da gaba ko da baki yi komai ba, sannan baya ya zama na qarshe, karki hade wajen a lokacin wankewa, in kika gama ki goge wajen sai ki maida pant din ki, in rana tayi kika yi wanka sai ki canja,in da hali da dare ma kan ki kwanta ki caja, ba yanda za yi a same ki da wari ko da baki shafa misk ba, balle a same ki kina wanke wajen da ruwa mai dumi da ki ka zuba musk, ko ki saka ruwan d'umi kaɗan bayan kin gama wanka ki tsiyaya zuma asalin mai kyau ki wanke gaban ki da shi,yana daga taskar magunguna da ya kamata  muna amfani da shi, bake ba warin gaba in dai kina wanke wa da ruwan zuma kina saka misk, kina tsanewa in kinyi bayan gida, ina fatan na amsa tambayoyin ki gaba ɗayan su yanzu Hajiya tambai"

"Hhhh kwarai da gaske Juwaireren Mama da Yah Jabeer kin biya ni kin amsa har da wanda ban ma zata ba ke dai Allah ya barki da yaya, ya sauke ki lafiya"

Cikin jin daɗin addu'ar Nafee ta hau shafa cikin ta sannan ta amsa, tashi ta yi ta shiga bayi dauke da butar ta a hannu, bayan ta fito ne take ce ma nafee,

" Nafee na ga kina zare ido, kar fa ki je ki yi fitsari ko ba haya ki hau tsarki da ruwan almiski kin dai san ba ya tsarki , ana tsarki ne da ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa,ah toh gwanda na yi maki bayani dalla dalla kamar yanda ki ka ce, yauwaa kin San fa gobe ne ranar gyaran jikina ina zan samu dankalin turawa pls na wa ya qare,dan Allah in an samu ki zo ki taya ni kin dai ga yanda na koma ba zan iya yi ba ni kaɗai"

"Haka ne bayanan ki, maganar dankali kuma kar ki damu zan samo maki kan goben in shaa Allah,in ba ke ba ma wa yake ta wani gyaran jiki a wannan yanayin,ji cikin ki fa ya girma amma kk maganar gyaran jiki, ki bari ki haihu mana"

" Tab a'a ni dai ki samo min, in babu ma ina da zuma da sugar sai na yi amfani da su kawai lemon zaqi ko ɗaya ne ko biyu Zaki samo min"

"To Allah ya kaimu da rai da lafiya bari na yi wanka na fita makaranta"

"To Allah ya bada sa'a, bari na dan huta nima".

*****************************
Chapter 26 · 0% Book details