← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 61

Sashe 6

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba a ce mace karta taimaka wa mijin ta ba a gudu tare a tsira tare, hakan abune mai kyau dan zai qara mata samun lada mai yawa, sannan zata samu soyayyar mijin ta da yawa, amma abinda ba a so miji ya sa son zuciya ya dinga expecting ɗin matar shi dole dai ta taimaka a gida financially,in bata yi ba a zo rai na baci, yana jin haushin ta, daga nan an samu matsala, ita kuma mace ta bangaren ta kwadayin abun da mijin ta baida halin yi ta ce dole sai ya yi mata, dan ta gani a maqota kama ko jikin qawaye,abun ya kama daga kan sutura, abinci, da abin hawa, sai ta fara nuna halaye na kwadayin abin duniya wataran har ya kai ga tana sabon Allah dan ta samu kudin wadannan abin da ya fi qarfin ta da mijin ta , kinga kenan ta biye wa son zuciya daga nan aure sai ya lalace azo ana samun matsaloli, zan barku anan saboda dare nayi kuma na san amarya ta gaji tana buqatar hutu ko ba haka ba?"

Murmushi ta yi kawai mai sauti tace,

"Mun gode Allah ya saka da alkairi"

" Ameen"

Suka amsa gaba daya, anan wani abokin su kuma ya amsa ya yi masu addu'a mai yawa wadda zata yi masu matuqar amfani a rayuwa in Allah ya amsa masu, a haka ne suka ce bari su tafi, ya tashi zai raka su, yana miqewa ya bige yar qara ya yi, Juwairiyyah ta yi sauri ta dago tana mai sannu, ido abokan shi suka zuba mata suna mamakin kyaun matar Jabeer ɗin, ganin haka ne yasanya kishin Jabeer motsa wa cikin haɗe fuska ya sauri ya yi gaba yana fad'in ,

"To kuzo mu tafi mana"

fita suka yi suna zuwa soron gidan yace

"To abokai na ni zan koma na gode Allah ya bar mana zumuncin mu da amana"

" Ameen" suka amsa, wani ne a cikin su cikin tsokana ya ce,

" kai dai ba sai ka kore mu ba muma sauri muke yi dare ya yi muna da mata kai da ma farin shiga ne a wannan lamari na aure,amma gaba ɗaya ka matsu ka koma ba zaka iya koda qara second ɗaya bane anan"

Dariya suka yi gaba ɗayan su Jabeer kuwa ya yi wuf ya shige yana daga masu hannu, sai da ya rufe gidan sannan ya leqa sashen iyayen shi ya ji shiru da alama sun kwanta bacci, direct sashen su ya wuce,ko da ya shiga sai ya tadda Juwairiyyah Zaune ta haɗe kai da quiwar qafar ta, bayan ya yi sallama ta amsa ne ya qarasa shiga ciki, kusa da Ita Jabeer ya je  ya tsugunna ya na bin dukkan jikin ta da kallo a hankali ya sa hannun shi ya riqe nata ya na murza wa, yanda nunfashin shi ke sauka a kan hannayen ta daya riqe ne ya sa zuciyar ta sauri wajen bugawa, ga wani irin tsoro shi da take ji a lokaci d'aya kuma  wani feelings sabo da bata taɓa jin irin shi ba ya na shigar ta,

" Princess kin ga yanda ki ka yi kyau kuwa? Ba dan kar na yi qarya ba da sai nace tinda nake a duniya ban taba ganin kyakkyawa irin ki ba"

Cikin sarqewar murya ta furta ,

"Kai Yah Jabeer wannan kowa ya ji ya san daɗin baki ne kawai ka ke min"

Matsawa ya qarayi sosai fuskokin su na daf da na junan su, sannan yace,

" Hmmm ke ki ka ga hakan amma ni iya gaskiya ta na fada"

Wani irin abu ta ji  a jikin ta wanda bata taba jin irin shi ba ya na mata yawo daga kanta zuwa qafafun ta,

'Dama wannan ne rayuwar auren da ake faɗa ana tsorata mutane?, da na zaci wata azabar ake sha kamar yanda shamsiyya da akai wa aure ta faɗa min ni da Nafee,

Dafa ta Jabeer ya yi sannan ya ce mata,

"Me ki ke tinani haka"

Ya qarasa faɗa ya na ɗora labb'an shi Saman nata,da sauri ta miqe tsaye ta yi breaking kiss din da yaso ya yi mata, ta hau kame2 tama rasa ina zata shiga, d'aki zata ko waje zata yi ne? kamo kafadun ta ya yi dika biyun ya miqar da ita tsaye a jikin bangon da kusa da bed room din su.

" calm down my princess, na ga kina tsoro na kamar wani dodo"

Murmushi ta yi na yaqe sannan  tace,

" Yah bacci nake ji jikina ciwo yake min"

" Ok to muje ki yi alwala mu yi nafila sai ki samu ki rage kayan jikin ki mu kwanta zan maki tausa ma in ki na so"

Baki na rawa cike da sauri  da in-ina tace,

" Aaaa..... bama....bama sai .. ka min tausaaa ba "

Dariya ya yi mata ganin yanda hankalin ta ya tashi kamar wadda ya yi wa wani abun, alwala suka yi sannan ya ja  su suka yi salla raka'a biyu bayan sun idar ne ya kama kanta, ya fara kwararo addu'o'in da suka zo a sunna ana yi wa amare,kamar haka,

" Allahumma innee as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha a laihi wa a'udhu bika min sharri ha wa sharri ma jabaltaha alaihi"

Bayan sun gama ne ya koma palour inda ya ga an jera mata plates a 'yar qaramar  kitchenware ɗin ta ya dakko sannan ya dauki ledar da abokan shi suka aje masa mai kaza a ciki ya shiga d'akin, zama ya yi a gefen ta ya juye masu kazar a plate wadda aka gasa  ta aka zuba soyayyan chips din da yasha hadin hanta da kayan kamshi, ga attaruhu da albasa sai tashin qamshi suke yi, kamshin ne duk ya karade d'akin har ya yi sanadiyyar motsa mata da yunwar da take tare da ita, madara mai sanyi ya zaro a Leda ya ajiye a gefe da jus ɗin exotic na kamfanin Dansa, niyyar ta ta qi ci, dan qawar ta Shamsiyya ta ce in an bata kar ta ci, in taci sai ta biya shi da jikin ta,amma ina Juwairiyyah ba zata iya jure kamshin fa ke dukan hanci ta ba har ya yi sanadiyyar farfaɗo mata da yunwar ba,cikin ran ta take ayyana,

'Yana bani zan amshe ba zan iya fulako  ba ina dalili? iyaka da ya ce na biya shi na fara kuka nasan zai hakura ya kyale ni tun da baya son ɓacin rai na'

Kamar Jabeer ya ji huɗubar da ta ke yi wa kan ta ya yanki wata tsoka mai gwab'i ya miqa mata bakin ta, ta kuwa buɗe bakin ya saka mata ta hau tauna wa cike da jin kunya,a haka ya na bata yana ci suka gama cinye wa tasa suka sha madara da jus ɗin su, bayan sun gama ne ya fara qoqarin rage mata kayan jikin ta dan ta ji daɗin bacci a cewar shi.

Dan kuwa da kan shi ya zaɓo mata rigar da zata sanya ya ajiye a gefen gadon ya na mata murmshi,wurga ido kawai Juwairiyyah  ke yi ko ta ina ta na mamakin lamarin da ke faruwa,a hankali idanun ta suka fara cikowa da ruwa, Jabeer na kula da haka ya sakar mata riga da ya kama zai taya ta cire wa, baƙin ta na rawa ta furta,

"Yah Ka bar ni na cire da kai na,"

" Ok cire ki kwanta dare ya yi"

Sai ya ja baya ya je ya fara cire nashi kayan ya saka na bacci a gaban ta, a lokacin da ya cire rigar da wandon shi a gaban ta ba ko kunya sai ta zaro ido waje ta na sake mamakin abubuwan da ta ga Jabeer na yi ba ya ko jin nauyin ta, hankalin ta ya yi mugun tashi dan ganin yanda jikin shi yake a murd'e kamar na masu ɗaukan qarfe,take jikin ta ya fara bari ta yi saurin kauda kai gefe, cike da tsokana kuwa Jabeer ya ce,

" Ki na son abinda ki ka gani ne? "

Da hanzari Juwairiyyah ta sake juya masa baya ta ce,

" No i don't, in fact banga komai bama ni, ba kuma na so na ga ni"

Muryar ta na rawa ta qarasa maganar,Jabeer kuwa cewa ya yi,

"A gskiya Naseer ya kyauta min da ya mata min na yi wanka kan mu zo amma da ban san ya zan ba yanzu dan a matse nake zuwa wankannan batan lokaci za yi"

Zaro ido ta qara yi kamar za su fado qasa, ta ce,

" Yah to ka tashi ka je toilet mana tinda ka matsu?"

Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce,

" Hmmmm gama ki ga me nake nufi"

Tare da kashe mata ido ɗaya ,take hankalin ta ya tashi dan ta gano me yake nufi yanzu, a hankali ta d'au kayan ta zata fita palour ta canjo ta dawo amma Jabeer ya hana ya ce anan a gaban shi zata sauya,ba yanda ta iya a dole haka ta sauya kayan ta a gaban shi, sai binta yake da kallo kamar wani maye,ta na gamawa ta zauna bakin gado ta yi addu'ar bacci ta shafa a jikina ta, ta kwanta a farkon gadon kamar a ce kyat ta zura da gudu,gashi basu baro gida an kawo ta d'akin miji ba sai da Inna Deeje ta sanya ta yi mata alqawarin bazata guji mijin ta ba , zata bashi duk abinda ya nema a wajen ta mudin bai sab'awa Allah ba, janyo ta ya yi jikin shi, yana shinshina qamshin ta,

Cikin dasasshiyar murya Jabeer ya ce,

" kaiii amma princess gaba ɗaya qamshin nan ya sa na qara qaguwa na kasance da ke"

Shafa ta ya fara yi yana mata salon da ita kanta ba zata so ya daina ba, a wannan lokacin Yah Jabeer ya fara qoqarin cika aiki, sai ta ji ya fara addu'a ta saduwa da iyali, kamar haka,

" Bismillahi Allahumma janibnash-shaidhana wa jannibash-shaidhana ma razaqtana"
Chapter 6 · 0% Book details