Sashe 25
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan kwana biyu da sanin cewa basu da mahaifa,Suwaiba da Saudat sun fara sabawa da wannan mummunan labarin da suka juyo wa kansu, Saudat ta fara neman dalilin da zai sa ta san me ne ne silar rashin haihuwar su, watarana Alhj Kalla zasu tafi meeting gidan Oga Zaks shi da abokin cin mushen shi,already har an kusan fara tattaunawar da za a yi mutane duk an hallara, a cikin waɗannan kwanakin Sudat ta fahimci ko su Alhj Ƙalla su waye kuma ne suke boye masu,sai dai ta qi gayawa Suwaiba dan ita akwai wauta, da ta sani zata fasa kowa ya san sun sani, idan haka ta faru ta tabbata za ta jawo masu masifa ne kawai, sai da ta gama jin gaba ɗaya hirar tasu ta sabon member da suka samu da zai shiga qungiyar tasu amma bai san location ba, take Alhj Kalla ya fara bashi address, Saudat kuwa na boye tana kwafewa, ta gama kenan zata tura a riga Alhj Kalla ya fito, gaban ta ne ya yi mummunar faduwa amma sai ta yi qoqari ta dake, ta ci gaba da jan rigar ta kamar tana gyaran rigar ne tun farko,kallon ta ya yi ya na murmushi ya ce mata,
" Ohhh mata kenan, daga kwalliya sai saka kayan ado, sai gyare2 kawai kar dai aga munin ku"
Dariya suka yi gaba dayan su,kafe ta ya yi da ido sannan a hankali ya furta,
"D'azu ina ta kiran ki ina palour ban ji kin amsa ba min ba"
Take ta gane wayo yake son yi mata,dan haka sai ta ce,
" Ayya ka yi haƙuri ban jiba bane Alhj na, ni da nake nan kana can,wataqila ma da ka daga murya dana jiyo ka, tinda kai ba zaka yi amfani da waya kana kirana ba , sai ka yi ta kira in ban ji ba kace na yi laifi"
Murmushi ya yi a ranshi ya tabbatar bata ji komai ba na daga hirar su,
"Ok shikenan je ki dakko min ruwa na sha anjima kaɗan zan fita"
Tashi ta yi tana kad'a jiki tana yauqi ta fita, tana isa kitchen ta qarasa da hanzari ta ciro takardar ta wulla a bayan fridge din dan ya fi kusa da ita, motsin shi ta ji ya biyo ta Shima kitchen ɗin, bude fridge ta yi kan ya qaraso ta dakko ruwan da cup, yana isowa tace masa,
"Hmmmm Alhj na kana sona da yawa na kula 'yan kwanakin nan kamar ka maidani rigar sawa ko ina zaka sai dani"
Murmushi ya yi yace,
" Ai ke kk koma haka shiyasa na koma hakan nima"
Sannan ya karbi cup din ya haɗe da hannun ta ya matse saida ta yi qara, ya zaro mata idon shi jajaye yace,
"Ki kiyayi bincike domin yana kai maiyin shi ga halaka"
" Bannnn......ban ganee...baaa? Me ka ke nufi?"
"Dalla malama rufe min baki, ji kike ban san kina bin waya ta ba? Ko bibiyar inda na fita? Ina nake zuwa me nake yi a can ɗin? Me kike son sani yau na sanar dake? Dan ba tsoron ku muke ji ba? Auren kwad'ayi auren kuɗi ku ka yi da mu, kuma kuna samun kud'in ko ba ku samu? Basu ishe ku bane? to meye na sai kin ji kwakwaf?"
Jikin Saudat sai rawa yake wani ruwa2 tabji na tsattsafo mata ta qafart ta bata ii aune ba ta ji ya kwada mata mari sannan ya ce,
" Dan uban ki fitsari kika yi a tsaye? Ji yanda kika bata min takalmi ni da zan fita,Me kika sani game da mu?"
" Alhj ban san komai ba, sai dai zargi da nake yi"
Aje cup ɗin ya yi ya zaunar da ita a kujerar dinning dake kitchen din ya ce,
"Ehen ina jin ki zargin me kike yi?"
"Dama ina zarkin ko ku yan damfara ne, kai da Alhj Salihu"
" Kin tabbata zargin da kike yi kenan?"
"Allah shine"
" To bari ki ji, zargin ki ya tabbata, amma idan na ji wannan maganar ko a wajen waccan doluwar yayar taki da ba abinda ta sani sai b'arin zance, da son kuɗi ranar za ki mutu, kinji ko baki ji ba"
cikin tsawa ya qarasa zancen nashi, baki na rawa Saudat ta ce,
"Nnnnaaajii..."
" Da kyau,ni na fita miqon takardar da kk boye kan na karya ki"
Tashi ta yi ta dakko ta miqa masa ficewa ya yi ya barta a wajen,ya na fita ta durqushe tana ta kuka, lallai yau data gaya masa abin da ta gano game da shi da fa shikenan kashe ta zasu yi, yanzu ta gudu ma nan ma har gidan su zashi wataqila ma ta jawa uwar su a haɗa da ita a kashe, ta zauna ta yi shiru su yi ta cin kud'in haram kudin jini,
"kaiiiiii wannan Abuja ba ta yi ba, inaaaa"
Ni dama na sani a Damaturu na yi aure na huta"
Ta fada tana share majina.
************************
A cikin garin Abuja kuwa bayan Talle ya dawo da salma gidan da yake aiki ya ajiye ta a dakin shi na masu aiki sai ya fice ya bar gidan , tun da ya fita take zaune a wajen take faman aikin kuka,idanun ta duk sun kumbure,a nan inda take zaune baccin wahala ya ɗauke ta,Talle kuwa ba shi ya dawo ba sai wajen la'asar hannun shi riqe da koko da qosai irin ɗan yamman nan da ake yi, sai wata leda mai kaya a ciki kala uku da takalmi kala biyu sai jaka daya, da yan kayan kwalliya da ba a rasa ba, miqa mata ya yi, ba musu ta tashi ta isa gaban shi ta Karb'a, leqawa ta yi ta yamutsa fuska,Talle na ganin abinda ta yi ran shi sai ya ɓaci, cikin haɗe fuska ya kalle ta ya ce,
"Baki daku ba kenan ko, har da zan baki abun da ban sai wa Marka ba na tsahon shekaru ke kin samu amma ki ke kyabe baki ko"
A tsorace tace,
"Na gode"
Ta Karb'a ta ajiye sannan ta shiga dan bandakin dake maqale a dakin ta yi wanka ta canja kayan ta fito, koko da qosan ta ɗauka ta ci ta sha, sannan ta koma ta zauna, kallon ta ya yi a wulaqance ya ce mata,
" kin iya cewa wani ya yi sallah amma ke bata dame ki ba, ji kike ban gane ki ba, wa'azi a baki amma ke baki aiki da shi munafuka, irin kune kuna da yara kuna sa su sallah su qi yi, to basu ga kuna yi ba"
Miqewa ta yi kamar munafuka da tsaho kamar raquma ta tafi,zalo zalo taje ta yi alwala ta
Yi sallar ta koma ta zauna,kallon ta ya yi ya kama kunnen sa alamar zai yi mata gargad'i,
" zuwa gobe ogana zai dawo shi kaɗai yake zama anan, matan shi suna maiduguri, aiki ke kawo shi nan, dan haka in ya dawo da yamma ki shirya muje mu gaida shi, in muka dawo na gan ki a waje ko kusa da wajen dakinnan kin mutu ranar, dan na san ki idon ki idon kuɗi, kice zaki maqale ma bawan Allahn da bai san neman mata ba, na kula akan kuɗi komai yi zaki yi, tinda an iya bin qattin qauye masu bada dari da hamsin"
Hawaye take zubar wa sosai saboda tausayin kanta a ganin ta ba abinda yafi sharrin zina da sata baqin ciki a duniya, haushin ta bai wuce yanda yama qi ya saurare ta ba sam, ya tsaya ta masa baya ni yaqi, kawai sai ta maida kanta ta kwanta, bata qara furta komai ba har ya shirya ya fice, kuka take mai ban tausayi,cikin kuka ta ce,
" Oh ni Salma na saiwa kaina wahala daga 'yar shawarma da motar dana gani duk na rud'e yi yau ga inda na kawo kaina, Abuja ko wahala?"
A can qauyen su Talle kuwa
da kyar Marka ta miqe ta je ta hada wuta ta shiga ruwan dumi ta gasa jikin ta,bayan ta gama ta zubar da ruwan ta yi daki, komawa ta yi ta ci gaba da kwanciya, wani qaramin yaro ne shafi'u daya d'aga cikin yaran tsofaffin matan Talle ne ya shiga d'akin ,yaron zai kai shekara goma, baya jurar yunwa shi, dan ko da su Huwaila na baccin gajiyar iskancin su da suke sheqewa da dare, ita Marka takan tashi ta yi abin kari da wuri, to yau sun ji shiru kowa dif a gidan, tura kai ya yi dakin ba sallama, to ba a Koya masu ba,Marka na kwance ta ware qafafu tana ta firfita da mafici,bata ji motsin yaron ba sai maganar shi ya na fad'in,
" Marka yunwa muke ji"
Da sauri ta sake zanin ta ta juyo kan shi,ta qanqance ido sannan ta ce,
"Me kace?"
Cikin dauriya yaron ya ce,
" cewa na yi yunwa muke ji"
Kiran shi ta yi tace ya je ya karba, yana isa data damqe shi ta hau duka, tare da fad'in,
" Yau sai na fanshe duka na da uban ka ya min a jikin ka ,baka da labarin ta'annutin da uban ka ya min shine har abinci ka zo ka na tambaya? Ga shi yanzu na san tinda ya dauke waccan jaja amaren sai na gan shi kuma, to kuwa yau zaka ci abinci har ka qoshi,"
D'im d'im d'im kawai ka ke ji na tashi a d'akin Marka ta na ta dukan dan mutane,
" Marka lafiya me ya yi miki haka ki ke dukan shi kamar kin samu jaki?"
Cewar wadda ta shiga d'akin ta na qoqarin kar bar yaron a hannun Marka da ta haukace da b'acin rai,ganin da gaske yarinyar take yi zata karɓe yaron a hannun ta gashi bata ji ta huce ba, kawai sai ta sakar wa Haulen wani mari itama a kuncin ta mai shiga ƙwaƙwalwa.