← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 61

Sashe 14

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nafeesa ke jiran Juwairah da ta gama girkin rana wajejen qarfe sha daya na safe,ta kammala gyaran gidan tsaf tana son yau ta je ganin Maman ta , Nafee tace zata yi mata rakiya, dan haka ita har ta shirya amma Juwairah na can na wanka, can bayan kamar minti takwas ta bude ta fito daga bayin ta na fad'in,

" kin san Allah, ba dan kina jirana ba sai na qara five minutes, ya zan na yi wanka jikina bai fita ba, kowanne bangare a jikin mace fa ana son amasa wanki mai kyau, musamman lunguna da saqon jikin mace ke har kunne da cikin kunne sai na wanke, haka kurum Yah yazo min soyayya a kunne ya ji d'acin datti"

Cike da tsokana Nafee ta ce,

"Inyyee iyayen love, aiko ba zan gangancin wanke kunne na ba ruwa ya shige min a banza a barni da zuwa asibiti da jin azaba"

"Hhhhhh dad'ina dake komai baki iya ba, in zaki yi ai dabara zaki yanda ruwa ba zai shiga ba, tinda kinga yawan goge kunnen nan likitoci na ta hanawa bai da kyau, to sai ki samu ki karkata kunnen ki gefe d'aya, ki wanke ta baki bakin da lungu da saqon shi, in kk gama kik d'auraye sai ki saka towel ko zani ki tsane ruwan tas, in kika gama da b'ari ɗaya sai ki wa bari ɗayan ma haka, kinga ba ruwan da zai shiga kuma kin wanke shi fesss"

" kaiii Juwairah wayon ki da sanin yakamatan ki na ban mamaki, dan na kula wataran Mama Bilki ma mamakin ki take sosai akan halayyar ki"

"Hmmm tashi to mu wuce na gama shirya wa"

Tashi suka yi suka tafi bayan sun leqa sun yi wa Su Innarmu sallama ita da Baba Balarabe, qara masu kud'in mota ya yi yace su gaida mutan gidan in sun je, kar su yi magariba a can su dawo gida amsawa suka yi suka yi godiya suka tafi.

Da sallama suka shiga gidan, cikin zumudi ta fada dakin nasu, Mama Bilki ce ta fito dauke da fara' a sakamakon gane mai sallamar da ta yi, a hanya suka haɗe suka rungume juna suna ta murna, Ammar ne a gefen maman, da sauri ta dauke shi tana masa kisses ko ta ina,cikin farin ciki ta ce,

" I missed u so much my baby brother, how ar u doing my love?"

Dariya yake ta yi kamar ya gane ta yana ta surutai irin na yara masu son yin magana, dariya ta yi ta aje shi a cinyar ta suka hau gaisawa, Nafee ma gaida Mama ta yi, tana mai jin daɗin yanda taga soyayyar 'ya da uwa a tsakanin Juwairiyyah da Mama Balki, Goggo ce ta fito ta na shewa ta na dariyar shaqiyanci ta ce,

" A'a mutanen kano ta dabo ci gari jalla babbar hausa, ne a gidan namu yau kuma?"

Goggon ta qarasa tana dariya,

Nafee da ta san irin zaman doya da manjan da ke tsakanin Goggo da su Mama Balki sai ta karɓe maganar ta ce,

" Kano ko da me kazo an fika ba, in mutum ya faɗi alkairi yanzu mu bashi amsa dan gidan ya tarar amma in ya kuskure nan ma sai muje maqota mu yi aron rashin mutunci mu bashi amsa da kalar yaren shi"

Nafee ce ta qarasa maganar ta ta na murgud'a baki da fari da idanun ta,

Mama ce ta kalli Nafee ta ce,

"Kul Nafeesa, ai uwa ce Goggo a wajen ku, kome zata yi kar ku tanka ta, ku barni da ita nice daidai ita"

Goggo Sarai ce ta buga cinya ta tafa hannu sannan ta ce,

"Hahaiiiiiiiiii Casssssss a hakan? A hakan ne kike daidai da ni? Daga shekaran jiya da yarana suka min waya zuwa yanzu kudin da suka shigo mun ta akawun ( account) ba qanana bane, ke kuma fa? Me ta kawo maki, tuwon dusa miyar lalle?"

Dariya ta kwashe da shi sosai harda riqe ciki,Baba Baballiya ne ya shigo ya ji abinda ke faruwa cikin ɓacin rai ya ce wa Goggo,

" ke dai anyi sallamammiyar mace saratu, yanzu me kike yi kenan? Kin tsaya kina rashin mutunci gaban yara, ke da baki da kamun kai, baki son a zauna a gidannan lafiya, kullum sai kin nemi tijarar da ki ka qirqira aka yi a gidan nan kar ki zaci ban sani ba ina sane da duk abinda ki ke yi, ashe yauma ba zaki sawa kanki salama ba?"

Juwairiyyah ce ta tashi da sauri dan ta kauda maganar da Baban nasu ke yi ta ce,

"Oyoyo Baba na da gudu ta je wajen shi ta rungume shi, shima rungume ta ya yi ya kama hannun ta suka zauna, qasa ta duqa ta gaishe shi, Nafee ma haka amsawa ya yi cikin nishadi"

Ganin haka sai ran Goggo ya sisi, ta kalle su ta ce,

"Ehhhhh lallai ne yau 'yar so ta zo, ka balbale ni da bala'i a gaban su mana, yarana tunda suka tafi baka neme su ba, amma wannan nunar ranar kullum sai ka tambaye ta, yau kuma ji yanda kk rungumar yar cikin ka kamar a gidan qabila"

" Ke malama in baki da abin faɗa mai kyau fita ki ban waje, Jahila kawai wadda bata san me ake kira da musulunci ba balle ta san abin cikin shi"

Magana Goggo ta buɗe baki za ta yi,Baba ya daka mata tsawa, ba yanda ta iya dolen ta ta fita tana qunquni, ci gaba da gaisawa sukai yi sosai ya zauna suka yi ta hira da 'yar tashi,haka dai har lokacin tafiyar su yayi, Mama ta tashi ta hau dan harhad'a mata wasu abubuwan iya qarfin ta dai, sallama suka yi tana kuka suna lallashin ta suka rabu.

Su kuma su Juwairiyyah suka koma gida,ko da suka isa gidan sun zaci za su tarar Innarmu ta dora girkin dare sai suka ga sab'anin haka, murmushi Juwairah ta yi ta shiga ta canja kaya, sannan ta fito ta hura wuta ta dora taliya a cikin kayan da mama ta basu, ta hada da ganyen alayyahu da albasa, ta daka yar daddawa kaɗan dan ba isasshen maggi to daddawar zata taimaka abincin ya yi daɗi , nan da nan ta kammala ta fada wanka abunta kamar ma ba ta yi ba.

Hikimar gyara daki kenan a wajen mace kafin ta fita unguwa, in kika gyara gidan ki tsaf in da hali ma ki yi girki kan ku fita har na dare tunda baki sani ba ko ku jima musamman idan da mutane a gidan, da kin dawo to wanka zaki yi kawai ki zauna ki huta abinki, ba ruwan ki da zama cikin qazanta, da kuma taraddadin aiki a gaban ki,in dai da ran ki da lafiyar ki to ki qoqarta ki na tsafta.

Juwairiyyah na fitowa daga wanka Jabeer ya dawo, fita ta yi ta amshi ledar hannun shi ta ajiye suka yi barka da dawo war su yanda suka saba, sannan ta ja shi bayi, sabon wanka ta sake domin cewa ya yi bata fita ba sai ya sake yi mata, tana dariyar gano wayon shi da ta yi tace,

"To shikenan ka gama nima sai na maka naka muje muci abinci dan na gaji yau da wuri zan kwanta"

"Tab yarinya ki daina zancen bacci da wuri ma in zaki bari"

Yana maganar yana matsa cinyoyin ta da yake wankewa, yar qara ta yi ta shagwaba ta faɗa jikin shi, tana goga cinyar ta ta a jikin shi,ta ce,

" Yah Jabeer akwai zafi fa"

Yanda ta yi maganar a saitin kunnen shi ne ya sanya shi jin wani ya tsarga masa har tsakiyar kanshi , janye ta ya yi a jikin shi ya jiqa mata soson ya bata ya ce,

" Yi sauri ki wanke ni nima ba zan iya jira ba baccin nake ji"

Dariya ta yi ta amsa tana masa wankan cikin wani salon da ya amshe soson ya aje gefe ina ganin haka na ari qafafu wajen masoyan Juwaireren Mama na qara gaba a guje........
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼     'YAN ABUJA    💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 10

Dare ne yanzu a cikin garin Abuja,manyan Alhazawa ne masu ji da nera a wajen shaqatawa na wani babban hotel da ke cikin garin su na hutawa da 'yammata da samari, sai kai komo manyan 'yan mata masu ji da kan su suke yi a gaban Alhazawan saboda suma a dama da su wajen cin kud'in da aka samu na yaki halal yaki haram.

Alhj Salihu da Alhaji Kalla ma ba a bar su a baya ba, dan kuwa su ma suna tare da 'yan matan su da bazan iya tantancewa arna ne ko musulmai ba saboda shigar banzan da ke jikin su,watace a cikin 'yammatan da na ji an kira da 'yar Gwal na kalla da kyau,daga nan na gane hausawa ne ma ashe ba arna ba,amsawa ta yi ta juya ta na kallo 'yar uwar tata da ta kira Sunan ta, nuni ta yi mata da ido, bin inda aka nuna mata ta yi da ido suna murmushi,

"Mene ne na ga kuna wani dariya kamar wasu wadan da suka tsinci damin kudi a qasa?"

Inji Alhj Kallah kenan da ya ga sanda suka yi murmushin,

'Yar gwal ce ta hau cinyar Alhj Salihu tana wani karairaya tana shafa shi sannan ta ce,

" Alhaji na kuɗi muke so ne shi yasa, gaba ɗaya qawayen mu sun wuce mu a komai na more rayuwar duniya bayan duk tare muke wannan harkar kuma muna tare da manyan mutane kamar ku,gaskiya zai zama abin kunya ace ko motar hawa bamu da ita su da suke bin qananan kwari su na jan mota mu kuwa kullum sai dai mu yi waya ku aika a d'akko mu ko mu hau taxi, gaskiya yawa ne Alhaj"

Tana magana tana kai bakin ta jikin nashi ta na masa wani salo mai ɗaukar hankali,wani irin nunfashi Alhj ya fitar da bai san yana ruqe da shi ba,a hankali ya ce,

"Haba 'Yar gwal yanzu dan wannan qaddamar buqatar shine kuke wani abu kamar baqi, ai in kuna son abu kamar umarni zaku bamu kawai, dan haka,....."
Chapter 14 · 0% Book details