← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 61

Sashe 38

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta bayan shi ta lallab'o ta fito ta yi masa wata iriyar runguma wadda tasanya shi sauke ƙanƙk'arfar ajiyar zuciya, juyawa ya yi gaba ɗaya ya d'aga ta sama, suna ta dariya, sumbatar ta ya dinga yi ya na nuna tsantsar yanda ya yi kewar ta,daga baya ya tafi suka samu waje suka zauna a kujera,inda Jabeer bai bar Juwairiyyah ba sai da ya zaunar da ita a Saman cinyar shi, yana shafa cikin ta tare da yi wa cikin nata hira kamar wanda yake hira da mutum babba, dariya kawai take yi ita kam, daga baya ta rage sautin dariyar ta tace da shi,

"Sannu da zuwa fitilar da ke haske cikin gida na, a gaskiya dole na dinga godewa Allah da ya ban kai a matsayin miji, Yah Jabeer tafiyar nan ta kwana biyu da ka yi ya sa na tabbatar wa kai na ba zan iya rayuwa mai ma'ana ba idan babu kai, i missed u so very much"

Ta qarasa maganar ta tare da qanqame shi tana hawayen farin cikin dawowarsa lafiya kamar wani wanda ya shekara baya gari, d'ago ta ya yi yana jin wani sabon qaunar ta na ratsa shi, dan kuwa kalaman ta sun ratsa zuciyar shi sun samu wajen zama ya kuma tabbatar da iyakar gaskiyar ta ta faɗa masa,

"Yi shirun ki my princess, ki daina kuka, Yah Jabeer na Juwaireren Mama ne ita kaɗai har abada, bana fatan na wayi gari na ga baki kusa dani,ke ce farin ciki na Juwairiyyah ke ce komai na, dan haka kar ki taɓa jin tsoron rasa ni saboda ni naki ne har abada,na mallaka maki gangar jiki na, ruhi na da zuciya ta ki yi yanda ki ke so da su dika "

Wata sabuwar runguma ta qara yi mashi da ta saka shi jin daɗi sosai, d'aga shi ta yi ta ja hannun shi zuwa wanka ta taya shi ya yi wankan ya yi brush suka fito, sannan ta taya shi shiryawa.

Bayan sun gama ne  suka nufi kan shimfid'ar da suke cin abinci suka zauna, duk abinda take yi masa ba qaramin daɗi yake ji ba, qima daraja da mutuncin ta na qaruwa a idanun shi,ita mace ce mai yawan kyautatawa,shi kuma namiji ne mai son a kyautata masa kuma mai yaba kyautatawar da ake yi masa,dan haka binta kawai yake kamar raqumi da akala.

Ta na buɗe mazubi na farko idon shi ya sauka a kan d'an wake murmushi ya saki mai sauti sama ya kalla cikin ran shi ya na godewa Allah tare da tunanin shin me ya aikata mai kyau a rayuwar shi Allah ya bashi Juwairiyyah a matsayin mata ya ninka wannan aikin alkhairin dan Allah ya bar masa ita su yi ta rayuwa tare har abada?

Hadiyar yawu ya yi dan ganin ɗan waken da har wani kyalli yake dan santsi sannan ta zuba mai wannann hadin da ta yi na dankali, zobon da ta dafa da abarba, cittta kaninfari, cucumber, goruba da sugar ta zuba masa, kafin ta gama dubawa Jabeer ya fara ci yana lumshe ido kawai tsabar yanda abincin ya yi masa daɗi, sai wani sautin santi  yake fitar wa dan kuwa bata gane abinda yake faɗa, Juwairiyyah kuwa dariyar jin daɗi ta dinga yi.

Kowacce mace ta na so idan ta yi abun kwarai a Yaba mata, dan haka yabon Jabeer a wajen ta ba karamin abu bane, hannu ya miqar ya ɗauki zobon da aka saka a randar sanyi ya yi sanyi dan kuwa Juwairiyyah bata da fridge ya kai bakin sa ya kurba, saurin buɗe idon shi ya yi sannan ya mayar ya kulle, ya ci gaba da santin  da yake yi, a hankali Juwairiyya ta ce,

" Yah Jabeer menene, yayi d'aci ne ko wani abu ka ji da be yi maka ba a ciki na ga ka buɗe ido da sauri?"

Ta yi maganar tana zaro ido waje dan a tinanin ta ko ba yi masa bane,da hannu ya yafice ta ya ce,

"Matso kiji me ya yi"

Yana ɗan yatsina fuska saboda ya ja wasan da kyau,nan take ta ɗan ji zuciyar ta ba daɗi, saboda gani take ta b'ata zob'on garin iyayin yi  masa had'e-had'e, dan ba ta san dama ana saka cocumber ba qirqira ta yi, matsawa ta yi kanta a qasa, Jabeer ya ce,

"To ai sai kin rufe idon ki sannan zaki iya jin me na ji nima ba ido rufe ki ka ga na sha ba ? matso sosai na baki da kai na ki ji ya ya yi"

Matsawa ta sake yi ta rufe idon nata, ji ta yi ya hau sumbatar ta har sai da ta ga wasu taurari na gilmawa a idanun ta ta kasa motsawa, a hankali Jabeer ya ce mata,

"To buɗe idon naki mana Princess wannan tukuicin kyautatawar ki a gare ni na baki duk da na san ba zan taɓa iya biyan ki ba,ni ba mai kuɗi bane bare na maki kyautar kuɗi gida ko mota, albarka kawai zan yi ta sanya maki tare da fatan alkhairi,sannan zan yi qoqarin sanya ki farin ciki har qarshen rayuwar mu"

A tare suka kammala cin abincin su ya na ta santi tare da yaba mata, anan ne Juwairiyyah ta gane lallai mace ta yi sa'ar mijin da idan ta kyautata masa ya yaba mata ma ba qaramin abu bane, duk wahalar da za ta yi dan taga ta kyautata masa ba zata tashi a banza ba.

(Abinda ya yi qaranci kenan yanzu ya na wahala maza su yaba wa matan su, mace sai ta jima ta na wahala dan faranta ran namiji amma kallo ma bata ishe shi ba balle ya yaba mata,amma idan ya ga wata a waje wadda ba muharramar shi ba ya dinga yaba mata ta na gwale shi, kuma haka zai ci gaba da yabawar wataqila ma har da tukuici kamar wani mara zuciya, ya bar halal ya tafi yabon haram)

Sad'af sad'af na miqe zan bisu amma 'yar nan ta banko qohwa ta ruhe wai kar na bi su sai gobe mun haɗu.............
[22/07, 8:44 am] asiyahabibu93: 💅🏼    ' YAN ABUJA   💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 24:

Saudat ce zaune a tsakar gida bata jima da aiken yaro ya siyo mata gasasshen kifi mai haɗe da chips da ake gasawa ba a wani suya spot a farkon shigowa layin nasu da ta saba ci tun lokacin 'yammatancin su, Goggo Sarai kawai ta iya bawa ta sa saura a gaba ta na ci ta na kora maltina mai sanyi, Salma mai ɗauke da ciki ce ta haɗiyi yawu saboda ranta ba qaramin biyawa ya yi ba,amma haka ta danne kwad'ayin ta dan ta san ba bata Saudat za ta yi ba,sai da ta ga ta kammala ci ta wanke hannu ta koma ta zauna a kujera ta na latsa waya sannan ta isa wajen ta ta gaishe ta, a daqile ta amsa ta na karkad'a qafar ta ɗaya da ta ɗora Saman d'ayar,cikin wani maqasqancin kallo ta ce da Salma,

"Meye ki ka zo ki ka tsaya min a ka,idan gaisuwa ne ai mun gaisa ko sai a yi gaba tunda an sauya uwa,idan kuma wani abu ki ke da buqata ki yi gaggawar sanar da ni dan bana so a tsaya min aka"

Murmushin takaici Salma ta yi,nan take ta hau tuna baya yanda yayun nata ke ji da ita suke ɗora ta a hanyar karb'ar kud'in maza, ba su jin kunyar nuna mata yanda za ta yi wa namiji kwarkwasa da taɓa bikin shi san ya bata kuɗi shi ne yanzu dan ta zaɓi hanya mai kyau suke gudun ta, cikin magana mai cike da ladabi ta ce wa Saudat ɗin,

" Adda Saudat dan Allah zuwa na yi ki ɗan bani koda dubu d'aya ce ina son in ɗan ja jari ne ko Saida gishi da omo ɗan qulli ne in fara yi a cikin gida, saboda zaman haka baya min daɗi ba kud'in kashewa,ke ma kuma ina mai baki shawara da ki nemi abun yi da kud'in da ya rage maki tun kafin su qare saboda yanzu kin ga kin saba da kudi, randa kike da buqatar su kika rasa ba qaramin damuwa zaki shiga ba"

Tunani Saudat ta shiga yi mai zurfi, can ta nisa tace,

"Gaskiya kin ce wani abu kema, zan baki dubu biyar ki ja jarin, ni kuma zan fara kasuwanci ta waya da naga qawaye na da na yi a whatsapp da facebook suna yi, ana samu sosai in ka riqe amanar mutane, sai kaga ka samu riba mai yawa kana daga zaune"

"Yauwa Addana na gode sosai, sai wata magana kuma mai mahimmanci da nake so mu yi ni da ke, ina son ki gane Mama Bilki mace ce mai kirki tana matuqar son mu, sai dai tabbas tana kishi da Goggo, wanda wannan dole ne a zaman kishiyoyi dama,shiga wannan kuma ba hurumin mu bane mu kau da kai akan wannan mu bar su su yi kishin su after all miji ɗaya suka haɗa,abinda kawai za mu yi shine mu yi masu biyayya dikkan su a matsayin su na iyayen mu,"

Shiru Saudat ta yi domin maganar qanwar ta ta yau tana shigar ta dan gaba ɗaya ba qarya a ciki amma akwai nau'i na girman kai da taya Goggon su kishi a zuciyar ta,dan haka sai ta yatsuna fuska ta ce,

"Hmmmm zan duba maganganun ki na gani"

Sannan ta miqe ta d'akko mata kud'in da ta alqawarta zata bata ta bata, duk abinda ya faru akan idon Goggo Sarai ya faru, sai dai bata ji kalaman da suke yi ba ta dai ga an bawa Salma kuɗi,magana take cikin b'acin rai,

"Habaaaa Salma ai innice ke yanda na canja uwa, yan uwan ma canja su zan yi, auhoooo ba zaki iya canja yan uwa ba saboda su masu arziqi ne Zaki yi roqo za a baki , amma ita uwar ki tinda talaka ce shi yasa ki ka sauya ta"

" Ni fa Gogga ba haka bane, ya kamata ki buɗe idon ki ki gane inda gaskiya ta dosa, ki daina rufe idon ki ki na yin abinda bai kamata ba"
Chapter 38 · 0% Book details