Sashe 48
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A haka Jabeer ya kashe bakin ta da zance ya mata wanka ta zauna a ruwan ta ji daɗi sosai, ya koma ya qaro wani ya saka ta a ciki, ya qara ruwan kal din a ciki.
( ma'ul kal, wato ruwan kal yana wanke datti shima sosai, ya fidda qarni da warin HQ sannan yana matse mace, ya gyara ta, sai dai ba a so in ba kamar yanzu da aka haihu ba a cika amfani da shi, da shi da bagaruwa, baya-baya ake son amfani da su, dan kar su yi illa ma wajen, kuma ana son in ana amfani da su a yawaita cin fruits da veges da kuma shan zuma mai kyau da zam-zam, dan su zama sun saukar da ni'ima)
Bayan sun gama wankan ne Jabeer ya fito daga band'akin sai ga Nafee ta dawo daga makaranta, shigowa ta yi da gudun ta, sakamakon kukan baby da ta jiyo, ai suna ido huɗu da Juwairah ta kwasa da gudu ta isa wajen ta ta rungume tana murna ta ce,
"Sannu matar Yayah Allah ya qara maki lafiya ya raya mana abinda muka samu"
"Ameen Nafee sannu da dawowa"
Jabeer ne cikin salon wasa ya ce wa Nafee,
"To malama sake ta haka ta ji da kanta"
Sakin ta ta yi ta na dariya, bakin ya qi rufuwa kamar gonar audiga, d'aki Jabeer ya wuce ya bar su tsaye Juwairiyyah na takawa a hankali suna hira da Nafee za su shiga d'aki,su na nan tsaye Jabeer ya fito hannun shi riqe da zanin haihuwar ya aje mahaifar a cikin leda zai wanke zanin,Nafee ce ta yi sauri ta yarda jakar ta a qasa ta ajiye mayafin ta a igiyar shanya tai wajen Jabeer zata karbe wankin,
"Yah Jabeer barmun na wanke ni ban yi komai ba ai"
" A'a sis basshi yanzu kika dawo daga school bana son ki wahal da kanki, kayan jini ne ke kuma baki son su suna sa ki jiri dan haka ki bari zanyi, bayan haka kin san Innarmu ta tsani wanki a kaf aikace-aikace ni me nake yi da ba zan wanke ba? Yanzu dai ita Juwaireren Mama ta yi me wuyar da ta haifo mana queen of beauties, shiga ki ga inda ake kyau yarinya barakallah Masha Allahu"
Ta na jin haka ta bar su a wajen ta yi d'aki dan kuwa sai ta ji ta qara kwadaita da ta ga yarinyar, tana isa ta zube gwaraf gaban Innarmu,Innarmu kuwa ta gyara yarinyar ta sha kwalli rambad'ad'au, ta yi matuqar kyau, idon ta bude fes kamar haihuwar sati, cikin zumud'i ta amshe ta tana yi mata addu'a Juwairah ce ta shigo da sallama d'aki,Idon ta na sauka akan jinjirar Itama ta hau tasbihi ga Allah tana matuqar godiya daya sauke ta lafiya ya bata Kyakkyawar yarinya kamar wannan, Mama Bilki ta sha addu'a yau a bakin Juwairah, kallon gefen ido take yi wa yarinyar saboda kunya,a ranta take ayyana;
'Ikon Allah ke nan yanzu da wanne ido zani gida na kalli Mama da Baba tinda dama dai su sun qi zuwa gidan nan saboda kunya, wai yau ni Juwairiyya ce na haihu"
Shafa cikin ta tayi da ya yi mata babba kamar bata haihu ba ga nankarwa da ta ji yayi rad'o-rad'o, murmushi ta yi ta qara gode Allah, nan da nan ta hau shiri ta d'akko man kad'en ta ta shafe cikin da shi sosai ta mulke shi da man har sai da ta ji ta daina jin maiqon shi sosai a hannun ta, murmushi ta yi dan tunawa da yanda cikin nata ya sha gashi wajen Yah Jabeer don jinin ya samu fita ita kan ta mamakin yanda duk ya iya abubuwan nan take yi duk da ta san yana karanta littafan ta na rainon ciki amma bata zaci ya riqe komai akan shi haka ba, bayan ta gama murje cikin ne ta kwalama Nafee kira dan ta zo ta d'aure mata cikin, zuwa ta yi ko ta tamke mata shi tsam, kayan ta ta saka atamfa riga da zani ya mata kyau sosai, kalar atamfar ruwan kwai ce dika, sannan ta feshe jikin ta da turarika masu daɗin qashi ta fito parlour zata zauna,a dai-dai wannan lokacin Jabeer ya gama komai ya yi wanka shima ya shigo, sannu ta yi masa da addu'ar Allah ya saka masa da alkairi, ya yi murmushi yace,
" Is my duty love, so ki daina damun kan ki da yi min godiya, amma fa bacci ya kamata ki yi bayan kin ci abinci yanzu"
Murmushi ta yi masa wanda tasan yana biyan komai a wajen Yayan nata, kad'a kai ya yi alamar zamu haɗu ne, ya wuce d'aki dan ya shirya.
Ya na gamawa ya fita palour ya tadda su dika a zaune Juwairiyyah ta gama shan kunu da tuwon da ya sha man shanu, gyaran murya ya yi ya kalli Abban su ya gaida shi, dan kuwa yana shiryawa ya shigo shima a yi murnar zuwan jikar tasu da shi,Abbah ya yi ma yarinya addu'a, Nafee na ta masu tsiya shi da Innarmu akan tsufa ya qara kama su sun zama kakanni,miqa wa Jabeer babyn Abban su ya yi shima ya yi mata addu'a, sannan ya faɗi sunan da za a ana kiran ta da shi, wato Hafsat sunan Innarmu kenan, Innar mu har kukan daɗi sai da ta yi dan jin hakan, sannan yace ma Juwairah,
"To ai sai ku nema mata sunan ku na yan gayu da na san dole sai kun saka mata,"
Nafee ce ta kalli Juwairah tace,
"Matar yaya sai ki bamu suna ko?"
Juwairah murmushi ta yi sannan ta shiga tunani,daga baya tace,
" Na saka mata Abrar, wato mai tsoron Allah"
" Oh ni Hansai yanzu ina ni ina iya fad'an wata Abras fisabillahi"
Dariya suka kwashe da ita har Abbah, Abban ne yace,
"Haba Innarsu, yanzu Abrah ɗin ne zai gagare ki?"
Haba me zasu yi in ba dariya ba dan shima kan shi Abbah ya kwafsa, gyaran murya Jabeer ya yi ya fara magana cikin tsantsar farin ciki da annashuwa tare da son sanar da su abin farin cikin da ya same su yace,
" Abba, Innarmu,Juwaireren Mama, and my little sis Nafeesa, ina mai farin cikin sanar daku ci gaban da ya same mu, a yau kuma a d'azu dana dawo na zo da labari me dad'i na samun aikin da na yi a NNPC na can Abuja in da suka ban gida dake kusa da gidan man da zan yi aikin, a unguwar Jabi har ma da mota, sun dauke ni a matsayin Manager na wajen gaba ɗaya, sanan kuma ɓangaren kasuwanci na yau na biya ta kasuwa, Saifullahi dana kan bari ya min jiran wajen in bana nan ya d'akko min kud'ad'e masu tarin yawa, da kuma wasu jakunkunan da na saro ba su iso ba daga malaysia , to a yau suka iso, har wasu yan kasuwan sun yi sari ma, shine ya bani kud'in da suka kai dubu dari biyu da talatin cif a hannuna, nan take na bashi talatin ɗin nayo gida da sauran gasu"
Juye-juye ya fara yi yaga ina ya wurga ledar da yazo da ita, dubawa ya yi ya hango ta can hanyar shigowa inda ya yar ya iso wajen matar shi mai naquda, kasa kudin ya yi kashi biyu, sannan ya qara kasa kashi daya biyu, miqawa Abban shi ya yi kashi ɗaya, sai kuma ya ɗauki dubu goma ya bawa Nafeesa sauran dubu arba'in ya bawa Innarmu, yace gashi su sa mai albarka,Abbah ne ya ce,
" Lallai wannan yarinya ta zama mabudin alkairi a gidannan, muna ma Allah godiya, nayi murna da farin ciki sosai na jin wannan abun alkairin daya same mu, Allah ya taya ka ruqo da gaskiya da amana, Allah ya qaro maka arziqi mai yawa mai albarka,"
Amsawa suka yi gaba ɗaya da,
" Ameen"
Innarmu kuwa kukan daɗi take ta yi tin da aka fara maganar, dan bata taba tunanin riqe kuɗi rabin wannan bama a lokaci d'aya dan tasan ba ta dasu, bata bawa kowa ajiya ba,yau gashi an mallaka mata su,shi ya sanya take kukan farin ciki, ta ma kasa magana sai kukan murna take na ɗaukakar da Allah ya yi wa d'an ta a lokaci d'aya,Nafeesan ce ta ce,
" Innarmu ki bar yin kuka, addu'a da sanya albarkar ki Yah Jabeer ya roqa a wajen ki"
Juwairah ma sai murmushi take zabgawa a lokacin da ta sake kurbar shayin da Nafee ta hada mata mai kauri da d'umi, innarmu kuwa share hawayen ta ta yi tace,
" Jabeeru ba abinda zance sai dai nace Allah ya qara maka albarka ninkin ba ninkin akan wadda ya maka, ina alfahari da kai a matsayin ka na d'a na, Allah ya kare min kai daga sharrin maqiya"
Amsawa suka yi dikka, Nafeema ba a barta a baya ba wajen taya murna da godiya balle mai jego Juwairiyyah,kiran sallah ne ya karad'e wajen tare da duhun da ya bayyana hakan ya nuna masu cewar magrib ta yi, miqewa suka yi bayan sun gabatar da addu'a, suka yi alwala mazan suka tafi sallah matan suka yi a gida Juwairiyyah kuwa d'aki ta je ta kwanta, ana cewa ana bacci bayan an haihun ita dai gata nan ido biyu, bata sani ba ko dan ta na cikin matsanancin farin cikin samun aikin da Yah Jabeer ya yi ne ya sa ta kasa bacci? bayan ya dawo ne ya d'akko kaza a akurkin su, ya yanka guda biyu ya kaiwa Innarmu ya ce a dafa wa Juwairiyya,Nafeesa ce tace ita za ta yi dan ta san yanda take son ta.
D'auka ta yi ta koma ɓangaren Juwairah ta d'akko ridin da suka daka tare , da madarar shanun dake aje a randar sanyi,sannan ta dakko kayan qamshin da suka niqo harda minannas a ciki ta gyara kayan miya ta soya sama sama ta tsaida ruwan dahuwar kazar kasancewar ta ta Hausa to fa dole sai an qara ruwa kafin ta dahu da kyau.