← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 61

Sashe 44

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ta saki ta na qunshe dariyar ta ta shige band'aki ta yi wanka ta gyara Jikin ta yanda ya kamata sannan ta fito, gani ta yi ya gama kashe wutar da ta hura ya deb'i garwashi a kasko ya sanya masu turaren wuta sannan ya fito ya kama hannun ta ta sauka daga tudun band'akin, alwala ta yi sannan suka wuce d'aki tare ba tare da ta ce masa komai ba, sai dai wannan karon fuskar ta sake take babu wani b'acin rai a tattare da Ita.

Sai da Juwairiyyah ta shirya cikin kayan bacci sannan ta ɗora after dress d'in ta ta sanya hijabi ta tada sallahr ta, ta na idarwa ko azkar bata yi ba ta kalli Jabeer da ke zaune a gefen gado ya na latsa waya ta tashi da kyar ta kwanta a gefen shi ta hau kukan shagwab'a ta na fad'in,

" Baby ni agwaluma nake son sha fa, ka samo min agwaluma"

Cike da kasala Jabeer ya zuba mata idanun sa yana kallon ta, dan kuwa a gajiye yake amma ba yanda zai yi dole ya yi mata abinda take so ya san ba yin kanta bane,ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce mata,

"Kin tabbata ita kike so yanzu?"

Ya qarasa maganar shi yana shafa cikin ta, saurin kauda kai ta yi gefe,dan kuwa kallon nashi na ratsa ta da yawa,bata so ma ya bata tausayi tace ta fasa dan kuwa muguwar sha'awar agwalumar take yi, d'aga kai kawai ta yi alamar Eh agwalumar take so, murmushi ya yi ya miqe tare da ajiye mata wayar shi a gefen ta ya tashi ya ja rigar shi ya sanya ya na fad'in,

"Bari na je na kawo maki kada sai sun tashi ki sa min kuka ki ce baki hakura ba sai na nemo ta"

Murmushi ta yi na jin daɗi, Jabeer ya sunkuya ya sumbaci goshin ta sannan ya bar gidan dan zuwa nema mata abinda ranta yake so tun da akwai inda za a samu ɗin a unguwar tasu, jabeer na daga cikin irin mazan nan da ke bawa matan su mahimmanci sama da danna wayar su ko wani abu a rayuwar su.

Jabeer bai dawo ba sai da ya samo wa Juwairiyyah agwalumar kalar wadda take so mai zaqi,zama ta yi ta sha ta qoshi,shima ya ɗauki ɗaya ya sha ya na ta yamutsa fuska kamar an mare shi, kafin daga baya ya miqa mata duka ya ce,

"Gashi nan ki yi ta fama,"

Dariya ta yi ta karɓi abunta ta yi masa godiya,gidan ya je ya rufe tare da tofe ko ina da addu'a sannan ya dawo ya rufe qofar palourn su, ya na zama ta tashi ta nufi d'akin baccin su Jabeer Shima ya kashe fitila ya bi bayan ta.

******************************

Fad'uwar Goggo Sarai ce ta ja hankalin su Suwaiba suka yi kanta gaba ɗayan su da gudu,kwance take magashiyan a qasa ta na bin su suwaiba da kallo kamar waɗanda suka sake sabuwar halitta a Jikin su, (ai ba qarya Hajiya Goggo suwaiba kam ta sauya halitta lols) idonta a buɗe hawaye na zuba ya wanke mata fuskar ta take qoqarin yin magana amma ta kasa,da karfi ta sa hannun ta ta toshe bakin ta ta sake fashewa da sabon kuka sai kace wadda aka aiko wa da rasuwar iyayen ta a qauye.

Ganin halin da take ciki ne ya sanya Mama Balki daure wa ta isa wajen ta da sauri, dan ta kula gaba ɗaya yaran nata kallon ta kawai suke ba wanda ya yi yunqurin d'aga ta daga qasa, d'aga ta ta yi da kyar ta kai ta kan kujerar dake daf da bakin qofar shiga d'akin ta ta zaunar da ita,sannan ta tafi cikin hanzari ta ta deb'o ruwa a randar sanyin ta ta miqa mata a cup, kasa shan ruwan ta yi tana ta kallon Suwaiba da ta haɗe girar sama da qasa, qarshe ma sai ta yi hanyar d'akin Mama Bilki.

Kuka ne ya k'wace wa Goggo Sarai da ta ga gaba ɗaya yaran ta duk sun bar wajen ma sun yi dakin kishiyar ta da ta dasa musu tsanar ta a ransu tun suna 'yan qanana,sai gashi tun ba a je ko ina ba yau ita suke nuna wa soyayyar su, wani gululun baqin ciki ta hadiya ta kalli Mama Bilki da ita ɗaya ce a kanta ta kauda kai taci gaba da zubda hawaye har wannan lokacin ta kasa magana.

Baba ne ya yi sallama ya shiga gidan,Mama Balki ke da girki ranar dan haka can ya nufa zai shiga,sai dai kukan da ya ji ana yi a d'akin Goggo Sarai ne ya tsaida shi, sai da ya tabbatar da gaske kuka yake jiyo wa kuma da alama na Goggo ne sai ya wuce d'akin nata dan ya ji me ke faruwa.

Ko da ya shiga sai ya tadda su Mama Balki a d'akin,ba kalar magana da lallashin da bai yi wa Goggo ba dan ya ji me ya sanya ta kuka amma ta ƙi magana,iyakar abinda Mama Balki ta sani ta sanar da shi sai kawai ya fita ya koma d'akin Mama Balkin dan ya tabbatar da maganar ta na cewar suwaiba ta dawo.

Ya na shiga ya tarar da suwaiba na kuka da sauran 'yan uwan ta,

" Suwaiba ke nake gani a gidan? Meke faruwa ne wai na ga kuna kuka? ku sanar dani damuwar ku yarana, duk da banda arziqin da zan maku maganin ta amma Allah ya hore min bakin yi maku addu'a akan ko meye matsalar ku"

Suwaiba ce ta je gareshi da gudun ta ta rungume shi, shima rungume ta ya yi a Jikin shi, nan da nan lokacin yarintar ta da tashin ta kafin ta girma ya dawo zuciyar mahaifin nasu,suwaiba kuka take mai ban tausayi,Baba ya kyale ta bai d'ago ta ba sai da ta yi kukan ta ya ishe ta sannan ya zame ta a Jikin shi ta zauna a qasa a gefen qafar shi,a hankali Baba ya ce,

"Sanar da ni damuwar ki d'iyata,ku zo duk ku fad'an damuwar ku na ji ko zan iya yi maku maganin ta"

Cikin shassheqar kuka suwaiba ta ce,

"Baba.... Baba ka yafe min, Baba ka yi hakuri akan qin jin maganar ka da na yi abaya,Baba nadama ta same ni a qurarren lokaci...."

Da sauri Baban su ya dakatar da Ita cikin tausayawa ya ce mata,

" Ah ah Suwaiba karki ce haka, lokaci bai qure maki ba 'yata"

Da sauri Itama ta katse shi ta hanyar d'aga rigar ta ta ce,

"Baba duba ka gani"

Cikin kukan da take yi ta juya wajen Saudat tace,

" Saudat nuna masa cikin ki kema ya gani"

Saudat ma nuna masa cikin ta ta yi dai-dai inda aka yi masu aiki aka cire masu mahaifa,.

"Me ke faruwa ne ku buɗe baki ku yi min bayani"

Baba ya faɗa cikin tashin hankali saboda ganin da ya yi Suwaiban su ta zama Nonoless,

"Baba mazajen da muka aura ta dalilin mugun son kud'i da abin duniyar tare da zuga da muka samu daga Goggo ashe 'yan qungiyar shan jini ne, Baba matsafa ne masu yin kuɗi da sassan jikin mutane"

Suwaiba ta qarashe maganar ta cikin qunar rai da d'acin da take ji a wuyan ta, a tsorace Baban su yace,

"Suwaiba ! Ki ka ce me? Shan jini fa Suwaiba, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Ya Allahu ya rahmanu wannan wace iriyar rayuwa muke ciki mai cike da rud'ani da tashin hankali? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel"

Zama ya yi ya dafe kan shi da yake jin ya yi masa nauyi sosai,ya jima a haka kafin daga baya ya ce,

" Sanar dani me ya sami qirjin ki da kuma gefen cikin ku gaba dayan ku ke da yar uwar ki?"

Kwashe duk abinda ya faru ta yi ta faɗa masa, cikin kid'ime wa da tashin hankali ya miqe ranshi ya gama ɓaci da jin abinda ya samu yaran shi, duk ta dalilin matar shi da ta kasa taimaka masa wajen ba yaran shi tarbiyya, ficewa ya yi a d'akin ya nufi d'akin Goggo cikin sauri kamar zai faɗi tsabar damuwa da tashin hankalin da yake ciki, da wata iriyar murya Baba ke wa Goggo Sarai magana ya ce,

"Shikenan yanzu hankalin ki ya kwanta, Saratu hankalin ki ya kwanta nace an maida min Yara marasa haihuwa, ba zan taba ganin jikokina ba ta bangaren su kenan,saratu bana manta wa ke da kan ki ki ka yi kutun-kutun ɗin da ya sa ki ka tsaida haihuwa, wai yaran sun ishe ki, wace irin mace ce ke? Da baki yi haka ba da na tabbata zuri'a ta tafi haka yawa a yanzu,Ki duba kiga Suwaiba an yanke mata nono gaba daya, banda jinin yaran nan da ake diba duk wata, tsahon wata takwas, ina zaki kai alhakin su saratu? Ga mahaifa an cire masu babu su babu haihuwa fa kenan"

kuka ne ya k'wace wa Baba bai san sanda hawaye suka fara zuba a idanun shi ba ya na kallon Goggo da kallon tsana da danasanin zaɓen ta a matsayin uwar Yaran shi,babu wanda baya kuka a gidan hatta Mama Bilki hawayen tausayin yanda rayuwar gidan na su cikin qanqanin lokaci ta koma take yi.

Goggo ta kasa cewa komai, bakin ta rawa kawai yake yi saboda kuka, sai zata yi magana sai ta ji bazata iya cewa komai ba sai ta sake rushe wa da kuka, Suwaiba ce ta katse su da cewar,

" Baba ina neman izini a wajen ka ka barni na yi mana d'aki a ta can wajen, dan ba zan iya ci gaba da zama da Goggo a d'aki daya ba ko kusa da d'akin ta"

Wani irin murmushin takaici Baban su ya yi yace,
Chapter 44 · 0% Book details