← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 61

Sashe 32

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duddubawa ya yi duk abinda bata ɗauka ba ya ɗaukar mata yana bata a hannun ta ita kuma tana riqewa, idon ta a tsaye suke kuma hawaye na zuba, haka ya gama ya sata gaba ya kulle qofar ya dauki wata jaka dan tsabar ya raina mata wayo ta zaci tare zasu bar gidan, mota suka ɗauka ya saka ta suka bar gidan kifa kanya ta yi a cinyar ta ta yi ta kuka.

Su na isa ta tasha ya yi parking a bakin tashar ya sauke ta ya yi gaba ko waiwaye bai yi ba balle ya ga a halin da ya bar ta,a haka ta samu ta isa cikin tashar bata ko ganin gaban ta da kyau tsabar hawayen da ke zuba a idanun ta, in da ta ji ana kiran Kano ! Kano ! nan ta isa ta shiga wata mota sauran mutum biyu ta cika ma,tana shiga wata arniya ta shiga itama, sunayen su aka basu su rubuta, amma ita ta yi shiru ta kasa rubutawa, kuɗi suka buqata ta miqa masu dika kud'in hannun ta ba tare da tace komai ba,ko da ya qirgi iya kud'in shi sai ya miqa mata sauran ta nade a hannun ta,ta jingina kan ta da jikin gilashin motar ta dinga raira kuka mai sauti ba tare da ta damu da kallo da qusqus ɗin da mutane ke ta yi akan ta ba, a haka har mota ta cika.

Har suka isa kano Salma bata daina zubda hawaye ba, adaidaita sahu ta ɗauka ya kaita har gida ta miqa masa kuɗi ta yi gaba shi kuma ya na neman canjin da zai bata,har ta yi gaba ya bita ya miqa mata a hannun ta, ya tafi yana fad'in,

" Allah ya kyauta"

Shiga gidan su ta yi babu ko sallama, Goggo Sarai tana zaune a kujerar da ke kallon duk wani mai shiga da fita a gidan tana kad'a qafa akan kujera, hango Salma a wani mawuyacin hali da ta yi sai da Goggon ta kusa tintsirawa qasa tsabar tashin hankali,da gudun ta zani na warwarewa tana gyarawa ta taro ta ta na fad'in,

" Lafiya Salma,Me nake gani haka? Ina mijin naki? Daga wace qasar kuka dawo haka? Fashi aka yi muku a hanyar ku ta shigowa Nigeria? "

Haka Goggo Sarai ta dinga jerawa Salma tambayoyin nan amma bata samu amsa ko ɗaya ba, d'aki ta ja ta suka shiga sai waige waige take da fatan babu wanda ya gan su, har Mama Bilki zata fita dan jin Goggo Sarai ta kira Sunan Salma amma Baba ya riqe ta, ya ce,

"Gimbiya bassu ni na je,yanzu da kin je sai abun ya koma tashin hankali kuma da. cewa za ta yi gulmace ta kai ki ba komai ba"

" To Baban su Allah ya jiyar da mu alkairi"

" Ameen"

Fita ya yi ya isa dakin, zaune Salma take a gefen gado idon ta na kallon waje ɗaya kawai ko qiftawa bata yi, kukan kuma ya tsaya cak kamar wadda aka cire wa batiri, tambayar duniya Goggo ta yi mata amma taqi magana, Goggo banda kuka ba abinda take yi a haka Baba ya shiga ya tadda su, cikin damuwa da jimanta lamarin Baba ya ce,

"Subhanallahi, me ke faruwa ne haka sarauta ki ka tasa yarinya a gaba kina ta kuka, Ke Salma ki yi mana bayani me akayi miki, ina mijin naki kuma? Daga ina kika fito a haka?"

Da jin murya da kalaman Baba Baballiya sai Salma ta saki wani kuka mai cin rai, nan take ta dakko takardar da Talle ya bata ta miqawa Abban nata, dan yanzu haushin Goggo take ji sosai, ta dalilin ta ta shiga wannan halin quncin da qananan shekarun ta tinda ai duk ita ce bata basu tarbiyya mai kyau ba, uban su kuma na son ya basu ta musu hudubar shed'an ta hana su saurara, wannan wace irin rayuwa ce haka, Salati suka ji Baba ya sake ya aje takardar ya zauna tare da dafe kan shi,cikin kuka Goggo Sarai ta ce,

" Malam me ya faru? Ku sanar dani ko hankalina ya kwanta dan Allah"

Cikin dakiya Baba ya kafe Goggo Sarai da idanun sa da suka yi jajawur saboda b'acin rai sannan ya ce mata,

"Mijin nata ne na can garin ABUJAN YA SAKE TA SAKI UKU"

Ɗora hannu a ka Goggo Sarai ta yi ta kurma uban ihu kamar wata qaura,sannan ta miqe a harzuqe ta hau jibgar Salma tana fad'in,

" Shegiyar yarinya me kika masa ya sakon ke, yanzu gashi kin yi mana asara, mutumin da ya fitar dake qasar waje Kuke shaqatawar ku cikin jin daɗin rayuwa, ki zalunce ni ki zalunci kan ki Salma ki sa ya sako ki, da dukkan alamu ma ciki ne da ke, amma shine tsabar baqin ciki ba zaki bar ɗan ki ya taso cikin jin daɗi ba sai da ki ka yi abinda ya maki sakin kare dangi"

kalmar ciki ne da ita da Goggo ta yi ba qaramin razana Salma ya yi ba,nan take ta sake tabbatar da Talle ya yi mata illa ba kaɗan ba,dan ko giyar wake ta sha a yanda ta san waye Talle ba ma zata yi gigin ta haihu ta kai dan ta qauyen su ba wanda shi yake ganin bata san Sunan qauyen ba amma a iya watannin da ta yi har qauyukan kusa da su ta san Sunan su, ai kamar yanda yace sun rabu ta manta da shi hakan za ta yi,ture hannun Goggo ta yi a jikin ta ta je gaban Baban ta ta durqusa ta ce,

" Babana ka yafe min, ka ji tausayi na ba dan halayyata mummuna da na yi a baya ba, ka duba girman Allah da soyayyar ɗa da iyayen shi ka yafe min duk abinda na aikata mara kyau a baya, ka tausaya ma abinda ke ciki na in ya tabbata ina dauke da cikin kenan, kar ka yi fushi da mu, ka bamu wajen zama a gidannan karka kori abinda zan samu, zan yi wahala ta hanyar halal na kula da abinda Allah zai bani, amma kar ka ce za a sake d'aga zancen uban d'an nan na gama da shafin shi, sabon shafi nake son budewa Baba"

Kuka ne ya ci qarfin ta sosai, wanda ya sanya Babansu hawayen tausayawa diyar tashi, yarinya fara mai kyau duk 'ya'yan shi Juwairah ce kawai ta fisu komai, amma Salma na bayan ta, dubi yanda ta koma ta jeme ta d'ashe kamar mara isashhen jini a jikin ta, har yau Salma bata rufe shekara ashirin ba, d'aga ta ya yi tsaye ya rungume ta,aiko kamar jira take yi,tunda abubuwa marasa daɗi sukai ta faruwa da ita take neman kafad'ar da zata jingina kanta ta koka baƙin cikin ta amma ta rasa, sai yanzu ta samu strong and loving arms ɗin da suka yi huging ɗin ta,hakan ne ya bata k'warin guiwar fitar da duk wani b'acin ran ta, haka Baba ya bar ta a kafad'ar shi ta yi kukan ta ma'ishi,da kan ta ta hakura ta samu waje ta zauna a gefen shi ta na sauke ajiyar zuciya.

Cikin murya mai rauni Baba ya ce yace,

"Ina zuwa Salma bari na dawo"

Mama Bilki ya kira bayan ya faɗa mata duk abinda ya faru, a tare suka shiga d'akin Goggo Sarai wadda har a wannan lokacin kuka take tare da tambayar Salma me ta yi wa Alhaji Mansur ya sake ta,Salma kuwa ko qala ta qi ce mata,Mama Balki na qarasa shiga sai ta isa wajen Salma ta zauna tare da dafa kafad'ar ta, Salma na ganin Mama Balki sai ta rungume da sauri , tana neman gafarar ta, Mama Bilki kuwa nan take ta ce,

"Salma na yafe maki Allah ya yafe mana laifukan mu, faɗa mana me ya faru"

Mama Balki na gama rufe baki Goggo Sarai ta isa gaban Salma a guje ta damqe mata baki ta na zaro ido ta ce,

"Yi shirun ki wannan sirrin mu ne kar ki yi magana a gaban maqiya"

Wani irin kallo dukkan su suka watsa mata, Salma kuwa kwace kanta ta yi a hannun Goggo Sarai ta fara magana,nan take ta sanar da su komai da ya faru tin daga tafiyar ta har dawowar ta a yau din, kuka sosai Baba ke yi duk jarumtar shi sai da ya tausaya wa 'yar shi har ya zubar mata da hawayen tausayawa,Mama Bilki ma ta yi matuqar tausayawa Salma,ita kanta Goggo Sarai abun ya dake ta kwarai,ga tausayin Salma ga kuma kunyar mutanen da ke zaune a gaban ta, ita kanta kuka take kamar an mata duka, Salma ce ta juya ta kalle ta ta na murmushin takaici ta ce,

" Yanzu Goggo a wanne hali su Adda Suwaiba suke, suna Kiran ki a waya ? kin je kin ga muhallin su ko kuma baki sani ba, kawai suna aiko maki da kuɗi ne kina ajewa ki na kashe na kashewa? Goggo baki san ina ne Abuja ba, amma tin tasowar mu kika kimsa mana son ta, yanda kika saka mana son abun duniya da hutu, da haka kika saka mana son ku kaɗai da yi muku biyayya da duk inda mu ka je aure ko min talauci da za mu zauna mu samawa kammu farin ciki,amma baki yi wannnan ba, Bama a maganar ki yi qoqarin dasa mana tsoron Allah da son Allah da yi wa Annabin rahama biyayya akan saqon da ya zo mana da shi na gaskiya, Goggo kin ci amanar kiwon da Allah ya baki, Baba na iyakar qoqarin shi akan mu kina rusawa, ni yanzu ba zan zauna anan d'akin ba, Mama Bilki ina riqon arziqin komawa wajen ki na zauna, dan tabbas nima ina zargin ciki gareni a yanzu duba da rashin ganin al'ada ta da ban yi ba,ga yawan ciwon kai da mara sai zazzaɓi da nake yawan yi, Mama Balki dan Allah ki koyan dukkan irin tarbiyyar da ya kamata nima inna haifi nawa na basu,ba irin wannan tarbiyyar mara kyau da ma'ana ba"

Goggo Sarai ce ta kwad'e mata baki da qarfi har sai da jini ya fita daga bakin Salma sannan ta ce,
Chapter 32 · 0% Book details