← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 61

Sashe 10

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata rana Juwairiyyah ta fito daga d'akin ta dan ta yi abinci sai ta fara da share madafin ta ta gyara shi tsaf,sannan ta qara dauraye tukunyar ta , ta haɗa wutar murhu ta dora ruwan zafi,sai ta deb'o waken ta ta fara gyarawa, ta gama gyara waken kenan ta wanke ta zuba sai ta yanka albasa a ciki dan ya yi laushi da qamshi, dama tasan ba su da kayan miya man da za ta yi miyar  kan shi manage za ta yi da shi bashi da yawa, kuma da dikkan alamu in suka ci wannan na dare sai dai ai hakuri, ta kammala dafa waken kenan sai nufi d'akin ta dan dakko shinkafa ta rege sai shinkafa tace ɗauke ni a inda ki ka ajiye,duban duniya Juwairiyyah ta yi amma haka ta nemi shinkafa ta rasa.

Hankalin ta ya tashi sakamakon duba lokaci da ta yi ta ga lokacin dawowar Yah Jabeer da ya kusa, cikin tsananin damuwa ta zauna ta zabga tagumi tare da fad'in,

" Oh ni Juwairah yanzu in ya dawo me zan bashi, ya wuni kasuwa bai ci komai ba, sannan ya bada kuɗin cefane daidai gwargwadon ikon sa a masa girki, kawai sai ya dawo ince shinkafar ta b'ata?" 

Tana tsaka da tunani da damuwa ne ta ji muryar Nafee na fad'in,

" kin kusa gama abincin ne ? Dan na fara jin yunwa , Innarmu ma na can tana neman abinci yunwa take ji sosai"

"Na shiga uku ni juwairah, kin ga Nafee anan na aje shinkafar daga kewayawa bayi kan na fito na rege na saka ban ganta ba, na neme ta sama ko wasa na rasa "

Cikin mamaki Nafeesah ta kalli Juwairiyyah ta ce,

"Baki ganta ba fa ki ka ce, to Ina zata ke ita ba qafa ba?"

kuka Juwairah ta fara ta koma daki ta yi tagumi ta rasa abin yi,ta na nan zaune dabara ta faɗo mata, tashi ta yi ta samu wannan waken ta rage masa ruwa sosai, ta samu dan man daya rage masu, da dan wani magi da take da guda uku, sai gishiri ta zuba a ciki ta qara albasa sosai, inda suke shuka alayyahu ta je ta yanko mai yawan gaske ta zauna ta cinke ta gyara ta wanke sosai ta zuba, nan da nan abinci ya haɗu murna ta dinga yi tana godewa Allah da wannan dabarar da ta yi, duk da qarancin shekaru irin nata amma hakan be sa ta tsaida tunanin ta waje ɗaya ba, sai ta faɗad'a tunanin ta ta yanda har sai da ta sama wa kan ta mafita, bayan ta gama ta zubawa kowa ta kai masu, ko da ta shiga d'akin Innarmu bata gan ta ba sai ta yi zaton ko ta na makewayi ne,kawai sai ta ajiye ta yi wa Nafee magana ta wuce sashen ta, kan ta fita daga sashe su Nafeen ne ta ji Innarmu da wani yaro tana ce masa,

"ka siyar shamusu nawa ya baka me shagon?"

Kasa kunne Juwairiyyah ta yi amma bta jin me yaron yace,sai ta sake jin muryar Innamu na fad'in,

" Amma dai bai kyauta ba gaskiya, a fa wajen shi Juwairah ta sai shinkafar amma shine ya rage har nera saba'in ɗan nema mai kan buta kawai sallamamme shi yasa shagon ya qi ci gaba gashi nan jiya iyau"

Kafin ta dawo Juwairiyyah ta bar wajen cike da mamakin da ya  cika mata ciki, dama Innamu ce ta dauke shinkafar? Me hakan yake nufi?dama Innarmu bata qaunar ta? Bata son zaman lafiyar da suke yi da Yah Jabeer?shin me yake faruwa ne?
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

Page 7:

Juwairiyyah na nan tsaye cike da tarin tambayoyi da mamaki ta ji Innarmu na fad'in,

"Shegiyar yarinya, daga zuwa komai na mu ya fara tabarbarewa, gaba ɗaya Jabeeru ya tare a qasan ta, ko shigowa gida ya yi da mun gaisa wuf ya tashi ya tafi wajen ta, ya dan zauna ma mu yi hira yanda muka saba sam ai yake yi,to an janye mai hankali, to ni ba zaki mulkar min d'a kamar yanda uwar ki ta yiwa uban ki ba in dai ina raye, haka kawai, ke na haifarwa dan? To mu zuba shege ka fasa tsakanin ni da ke"

Kuka ne ya kusa kwace ma Juwairah jin kalaman surikar ta, wannan wace irin rayuwace kuma?

" Ya Allah ka taimake ni na ci wannan jarabawar"

Abinda ta iya furtawa kenan ta share hawayen ta ta koma ban garen ta, qarasa gyara wajen ta yi tai wanka, ta yi brush sai ta koma daki ta tsaya cikin madubi ta gyara gashin ta da ta wanke ta shafa wa mai sannan ta taje shi ta daure a bayan ta, buɗe wardrobe ɗin ta tayi ta tsaya kallon kayan ta ta na nazarin wanda zata saka, kafin daga qarshe ta yanke shawarar dakko wasu riga da wando rigar pink wandon baqi siriri Wanda ake kira da pencil, Inna Deejee ce ta siyo mata su a 'yan gwanjo,tin su dai basu da halin siyan sabbi,kayan sun amshi jikin ta ba kadan ba, fita ta yi ta debo garwashi ta saka tiraren wuta, sannan ta feshe jikin ta da tirare ta qara da humra, kyautar Goggon ta Kareema kenan wato kayan qamshi, kafin kace me sai ga Juwairiyyah ta fito chass da ita,da ka kalle ta zaka dauka yar wani hamshaqin me kudin ce, ko matar wani attajirin, Nafeesa ce ta shigo tana murmushi ta ce,

"Dad'i na da ke matar Yaya ba dai tsafta da qamshi ba,kina burgeni fa ba kaɗan ba,ko ta wacce gab'a aka latsa ki kina nan kyam, a shekarun mu kina da kaifin hankalin da wani babban ma bai da shi, duba kiga yanda ki ka yi mana dabara d'azu, Innar mu da ta koma d'aki da ta ga abincin da ki ka kai mana ban san me ya razana ta ba, dan na ji harda ashar ta baza mana a dakin dazun"

Nafee ta qarasa maganar ta cikin dariya, Juwairiyyah ma dariya ta yi ta ce,

" kai sisto irin wannan fasa kai haka, in kk fashe man kan nawa yayan ki ya dawo kin masa bayani ai"

Sallamar shi suka ji da sauri Nafeesa ta fito zata bar wajen, tsayawa ta yi ta gaida shi sannan ta wuce, tana jin Nafee ta fita ta taso cikin yauqi da tafiya mai daukan hankalin masoyi,tare da wani lumshe ido kamar mai jin bacci ta isa wajen shi, ledar hannun shi ta Karb'a, sannan ta jawo hannun shi zuwa d'akin su, suna shiga kamar jira yake yi ya d'aga ta sama ya manna ta da jikin bango,dariya take mai sanyin sauti, ta zagaye wuyan shi da hannayen ta , dora fuskar ta ta yi a kan tashi, tare da hade bakin su waje ɗaya, sai da tayi masa kiss mai tsayawa a rai, sannan ta kai bakin ta wajen kunnen shi tana mai sannu da zuwa,

" Jarimin maza ina maka barka da dawowa, ina fatan yau kasuwa da mutanen cikin ta basu wahal min da kai ba ko? Dan in haka ta faru akwai hukunci mai tsanani akan su daga wajena"

Hura masa iskar bakin ta ta yi a kunnen tare da yin kiss a ciki ba shiri ya nemi wajen zama da ita a hannun shi suka zauna ya na sauke ajiyar zuciya,cikin kasalalliyar murya Jabeer ya furta,

" Agaskiya samun mace kamar ki Juwairiyyana akwai wahalake ɗaya ce tamkar ba iyaka, samun kamar ki a cikin mata million zai wahala, in zance zan tsaya fad'an wacece ke bakina zai rasa kalaman magana,so kawai ke kadai ce ba ta biyun ki , kuma ke ɗaya Yah Jabeer din ki ya ke so har abada ba na jin zan so wata kamar yanda nake son ki"

Wani irin daɗi ne ya lullube Juwairiyyah, kamar yanda kullum take son faranta mashi rai shima qoqarin shi kenan ya ga ya faranta mata rai, basu da arziqi, ba su da abubuwan more rayuwa, amma suna da junan su, tashi zata yi daga cinyar shi amma sai da ta goga mazaunan ta a jikin shi sannan ta miqe, gwalo ta masa ta tafi da sauri zata yi d'aki, binta ya yi a baya yana fad'in,

" Ai baki isa ba ki tsokanen ki gudu yarinya, tsayawa zaki ki qarasa ladan ki kawai"

Dariya take tana bashi hakuri,dan ta san tabbas ya na jin yunwa,

" Dan Allah Babe ka bari kaci abinci ka yi wanka, sai namaka tausa kamar kullum, in yaso in ka samu qarfin jiki yau sai abinda ka ce shi za a yi"

Tana kaiwa nan ta rufe fuska tana dariya ta zagaye shi ta fita da sauri, zuwa ta yi ta haɗa masa ruwan wanka,kafin ta dawo shi kuma ya shirya wanka, shiga suka yi bandakin a tare bayan ta je ta rufe qofar bangaren su, wanka ta masa da kyau ta sa masa toothpast a brush din shi ta bashi dan ya wanke bakin shi.

Mata da yawa suna cewa wai mijin su yana warin baki baya son yin brush da sauran su, shawara gare ki sister mai wannan matsala shine, ba a ce ma na miji je kai brush ko wani abu makamancin haka, dik da akwai mijin da in shaquwar ku ta kai qololuwa kina iya sanar da shi kuma ba zai damu ba dan yasan duk amfanin ku ne ke da shi, so in ba irin mijin nan gare ki ba dabara zaki yi, ki haɗa maku ruwan wanka tare kafin wankan ki tabbatar kin gama gigita shi yanda ba zai maki musu a ba, daga nan sai ku yi wankan tare, in ba ku yi tare ba ma saboda maybe yanayin gidan naku, sai ki saka masa ruwan ki kai masa da kayan wanka, sannan ki saka mai toothpast a brush ki aje mai a kusa, ba yanda za ai ya qi musamman yaga kin saka maku tare, kinga ba zai zargi kina jin wari bane daga wajen shi, har ya yi feeling bad kuzo kuna samun sabani.
Chapter 10 · 0% Book details