Sashe 52
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Goggo Sarai ta fito dan ta yi wa Alhaji salihu masifa akan rufe su da suka yi da zaluncin da suka yi wa yaran ta ta ji abinda ke faruwa,nan da nan sai jikin ta ya yi sanyi,sai kawai ta koma kwallar tausayin yaran ta,tabbas wannan ba laifin kowa bane illa laifin ta, ba su taɓa sanin Saudat na son mijin ta haka ba sai yanzu, a zaton su tun da ta taho ta bar wata soyayya da duk wata rayuwa da ta yi a baya jira kawai take ya zo dan kan shi ya sake ta ta sake sabuwar rayuwa, taimaka mata Mama Balki ta yi ta kai ta d'akin su ta kwantar da ita, kuka kawai take yi ta na jin kamar a gaban ta komai ya faru da mijin nata,cikin tausayawa Mama Bilki ta ce;
" Saudat ki yi hakuri , na san rashin masoyi akwai zafi, amma soyayyar da zaki nuna wa kalla a matsayin shi na mijin ki shine addu'a, tinda bai sake ki ba ke ki ka qi komawa, dan haka daga yau zaki fara takaba, har tsawon jini huɗu da kwana goma,dan haka har abada mijin ki na buqatar addu'ar ki, baya buqatar kukan ki, kin ji"
Ta qarasa tare da shafa kan ta cike da tausayawa, cikin sakewar jiki ta dora kan ta a kan cinyar Mama Bilki hawaye masu zafi na fitowa daga idon ta, nan take ta hau kwarorowa mijin nata addu'a, mama Bilki na amsawa,a haka har ta samu sauqin zuciyar ta itama, Salma na maqale tana tina nata tsohon mijin tana hawaye, ga tausayin Addar ta ta da ya dame ta.
Alhaji salihu kuwa bayan ya yi alwala ya yi sallah ne ya zauna cin abinci Abba ya ce idan ya gama su je gidan Yayan shi za a zauna a yi magana wato gidan su Jabeer,a cikin motar Alhaji Salihu suka tafi,bayan sun isa ne suka samu Yaya Balarabe na gida, tabarma suka sa a waje suka zauna,Baba ya yiwa Yaya Balarabe bayanin komai,bayan jimanta wannan mummunan lamari tare da yi wa Alhaji Kalla addu'ar samun rahamar Allah sai ya amince da mijin Suwaiba zai zauna a shagon gidan har Allah yasa su Jabeer su koma Abuja sai su kuma su zauna a bangaren su Jabeer ɗin,Baba godiya ya yi wa yayan nashi, ya koma gida ya bar Alhaji Salihi a nan,Alhaji salihu ya musu godiya sosai musamman da Yaya Balarabe yace zai fara koya masa ilimi na addini dan ya kula yana da qarancin shi, godiya ya yi sosai kamar zai kwanta a wajen dan kuwa ba karamar alfarma da karramawa suka yi masa ba.
Nafee Baban su Jabeer ya kira ta gyara shagon, aka shimfida masa wata yaloluwar katifa da wankakken zanin gado da pillow, sai sallaya da buta da ruwa mai kyau a bokiti rufaffe saboda ko zai buqata, Abban su yace in yana buqatar zagawa zai iya shigowa cikin gidan, godiya ya yi ta musu kamar zai kwanta, zuciyar shi cike da tausayin rayuwar da zai koma, sannan qasan ta kuma cike da murnar ganar da shi gaskiya da Allah yayi.
**************
Yau kwana tara kenan da haihuwar Juwairah har an yi suna an gama lafiya kuma bikin suna ya qayatar, dan kuwa Jabeer ya yi qoqari sosai, ga akwati nan biyu da ya yi ma mai jego da jaririya, ɗaya babba ɗaya qarami, gobe suke son komawa Abuja, dan wajen aikin na buqatar Jabeer ɗin da gaggawa, sun gama kwasar duk wani abu da zasu dauka mai amfani sun gama, kayan d'akin ta kuma zata barwa Addan nata da mijin ta tun da ba su da shi, a haka taje gida ta yi wa Saudat ta'aziyya ta kuma yi wa iyayen ta sallama, Juwairiyyah ta sha kuka kamar wadda za ai wa auren dole,da kyar suka lallashe ta sai da taga Jabeer ran shi ya fara ɓaci da kukan ta sannan ta hakura, sun dawo gida bayan Isha'i,Nafee ma kan ta ta sha kuka har sai da idon ta ya kumbura saboda kukan rabuwa da bestyn ta kuma yar uwar ta, sannan matar yayan ta da ke son ta,Innarmu ma ba a barta a baya ba wajen matse kwalla,tana qara bawa Juwairah hakurin zaman da suka yi a baya tare da fad'in,
"Ashe ma ita duniyar ba matabbata bace, ba abinda ke tabbata sai iKon Allah, gashi dai mutuwa bata raba mu ba amma zaman a tare ya kare, Allah ya sa ku koma sabon wajen a sa'a,Allah ya yi maku albarka"
Baba Balarabe ma jikin shi duk ya yi sanyin saboda rabuwa da Jabeer da Juwairah,musamman Juwairiyya dan kuwa itan yarinya ce mai shiga rai matuqa,gashi ta na da kyawawan halaye da kuma iya zama da mutane, a haka aka kwana gidan kowa da abinda ke ran shi.
Washegari da sassafe Jabeer da Juwairah ɗauke da Abrar suka fito suka shiga sabuwar motar Jabeer zasu tafi Abuja, Nafee ta riqe hannun Juwairah tana matsar kwalla, Jabeer ne yace,
" My little sis ki yi hakuri,kwana nawa ne zamu qara dawowa, ranar fa da Saudat zata fita takaba ranar za a fara bikin ki ko kin manta ne? dan haka ki kwantar da hankalin ki, sannan wataqila ma Salma ta haihu kafin nan zamu zo, ki yi hakuri kin ji,"
Hawayen ta ta share, ta yi masu addu'ar tafiya lafiya da samun sa'a da nasara a rayuwar su baki ɗaya,Innarmu da Abbah Balarabe ma haka, sai mijin Adda Suwaiba dake gefe shima yana masu fatan alkairi, motar ya tayar suka yi gaba cike da kewar juna.
Salihu kuwa gaba ɗaya ya canja,fatar shi ta qara duhu saboda dama shi baƙi ne, irin baƙin nan mai haske kaɗan, Alhaji Salihu na da kyan shi dai-dai misali,tumbin nan na shi ya ragu,hakan ya ba wa kyan shi damar sake fitowa, ganin yanda ya faɗa ne ya bawa Baba Balarabe tausayi,a qasan ran shi kuma yana ayyana ko zasu fara zuwa kasuwa tare ne wajen gwanjon su da shi ne? Bayan su Innarmu sun shiga gida ne ya same shi ya masa wannan tayin, cikin jin daɗi ya amsa da zai yi ko meye in dai halal ne ba damuwa, qasa ya yi da murya da kan shi sannan ya ce,
"To Baba ai ban da jari kuma"
" kar ka ji komai akwai jari a wajena ,ko da dubu biyar zaka iya farawa mu gani"
Godiya ya yi ta zubawa sosai har Baba Balarabe yaga dai ba zata qare ba, dariya ya yi ya shige cikin gidan ya bar shi a nan, rayuwa kenan Alhaji Salihu da ko masu aikin gidan shi albashin su daga dubu ashirin ne zuwa sama yau shi ne zai kafa jari da dubu biyar.
Ba jimawa Suwaiba da mijin ta suka tare a sashen su Juwairiyyah,kuma kasuwanci ba laifi wataran a samu ya siyar da kayan dika har ma a samu ribar da ta kan kai dubu uku zuwa huɗu, wataran kuma ribar ba ta kaiwa haka, a haka ɗin shi da ya fara da jarin dubu biyar yanzu ya kai dubu goma,duk abinda aka samu na Saman ya yi wa iyalin sa hidima da su watarana ma har da su Innarmu.
Salma da Huwaila kuwa kusan a tare suka haihu, Salma ta haifi Yaran ta biyu mata masu matuqar kama da iya kyawawa, ita kuma Huwaila ta haifi yaro namiji mai kama da Bangis sak, kwana tara ne a tsakanin su ,dan kuwa yaran Salma sun girmi na Huwaila.
Ranar suna kuwa Salma sai da ta yi taron suna dangi suka zo suka taya ta murna da sanya albarka har ta samu kyauttuka,dan kuwa da dama an zata haihuwa ta dawo yi gida,ba wanda ya san mijin ta ya sake ta sai daga baya magana ta yaɗu a dangi, wasu suka yi mata fatan samun wanda ya fi Talle wasu kuma na Allah ya ƙara ai ga auren miji ɗan ABUJA inda ya Kaita ta zama bazawara da qananan shekarun ta.
Bangaren Huwaila kuwa komai qayau-qayau su ka yi shi, ga habaici da suke sha wajen 'yan gulmar da ke zuwar masu barka da kuma wanda suka je sunan, yaron Huwaila ya ci suna Bilal,haka rayuwa ta yi ta juyawa wadannan bayin Allah da daɗi ba daɗi.
Ta bangaren gidan Baba Balarabe kuwa al'amuran gidan su ya bunqasa da arziqi dan Salihu ya shiga gwanjo a sa'a, yanzu har dila biyu yake iya bud'ewa wata rana ma har uku,haka gidan Yah Jabeer ɗin Juwairere suma arziqi ya wadatu a gidan su dai-dai misali abun dai sai godiya ga Allah, gidan su da suka koma a Abuja mai kyau da shi d'aki uku ne da dinning area sai babban parlour mai ɗauke da manyan kujeru da kayan kallo, yarinyar ta sai wayo take yi cikin koshin lafiya.
****************************
Shirye-shiryen bikin Nafeesa ne ya kankama gadan-gadan,wanda ya kama sauran kwana uku saudat ta fita daga takaba, a yau din ne su Juwairah da Jabeer tare da diyar su Abrar za su zo baza su koma ba har sai an gama bikin Nafeesa, Jabeer ba qaramin qoqari ya yi ba a yan watanni huɗun nan, shi ya yi wa Nafee kayan d'aki Abbah Balarabe ya bada kuɗi su Suwaibah suka siyo mata kayan kitchen da wasu abubuwan buqatar.
Jabeer ya kashe kuɗi sosai dan ita Juwairah ma ba ta sani wasu abubuwan da yake yi ba, tinani take yi in sun je ina zasu sauka? Tunda bangaren su yanzu Adda Suwaiba ne a ciki da mijin ta,bata da masaniyar d'aki daya da bandaki da palour madaidaicin da Jabeer ya masu a filin dake gefen gidan su wanda yake kamar kango ne a da, sai yar tsakar gida madaidaiciya, ba laifi ginin ya yi kyau,sai wajen azahar suka iso, ta ce wa Jabeer ya fara kai ta ta gaida su Innarmu idan yaso sai ya maida ta gidan su ta kwana,shiru ya mata ya na murmushi har suka isa gidan nasu,wajen Innarmu ta shiga cike da kewar ta, Nafee da gudu ta je ta rungume ta suka hau murnar yaushe gamo.....
*Juwaireren mama na gayyatar dukkan fans din novel din 'YAN ABUJA zuwa wajen bikin Nafeesa, Allah ya bada ikon zuwa ameen😂*[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH