← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 61

Sashe 31

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallon kallo suka hau yi wa junan su,nan take Saudat ta faɗa jikin Goggo tana kuka, Suwaiba ma idon ta ya cika da kwalla sosai,cikin kuka Saudat ta ce,

"Adda Suwaiba akwai abinda nake so dama in faɗa maki tun da jimawa amma na qi sanar da ke dan nasan halin ki tona mana asiri kawai za ki yi ki jawo su kashe mu a banza"

Cikin zaro ido Goggo tace wa Saudat,

" Suwa..... suwaye zasu kashen ku?"

Kuka saudat ta ci gaba da yi ta ce,

"Mazajen mu Goggo yan qungiyar shan jini ne,na gano hakan da jimawa, yanzu haka bamu da mahaifa da ni da Adda Suwaiba kuma ina zargin su ne sanadi"

Wani irin mari ta ji guda biyu sun sauka a fuskar ta suna neman dasa mata toshewar majiya,da ido ta ke bin inda marukan suka fito ɗaya daga Hajiya suwaiba ɗaya daga hannun Hajiya Goggo Sarai ne (uffararan ashe basu sauke faralin ba),cikin matsanancin Fushi Goggo ta fara magana,

"Dan ubanki sharri kuma zaki yi masu, mutanen da suke kasuwanci a qasashe ko ta ina, arziqi ya wadata ya bunqasa shine zaki ce haka, so kike kema ki dawo ki zauna ki jamin asara, na haifi yarinya zankad'ed'iya kamar ki da zan samu dukiya amma sai ki dankwafe kan ki ki hana arziqi rab'ar ki? To ki bude kunnen ki da kyau ki ji, ko ya ake ciki gobe zaku koma ai an ga juna ba zan lamunci asara ba shashasha kawai, ina ganin ki kamar mai hankali ashe ba ki da hankali"

Cikin kuka ta rarrafa wajen Baban su ta ce,

" Baba ka yarda da ni,na rantse gaskiya na faɗa, ba sharri nake yi musu ba 'yan shan jini ne, na ji da kunne na Alhaji na magana akan qungiyar su ta asiri"

"Na yarda dake 'ya ta, dan baki taba fad'an hakan ba kuma da dikkan alamu akwai gaskiya a zancen ki, wannan kud'in nasu yayi yawa"

"Baba ya zaka yarda da wannan maqaryaciyar ? Qarya ne fa kawai dan sun taɓa dukan mu sau biyu, shine fa ta qullaci abun take son ta gudu, to in ke ba zaki koma ba ni zan koma d'akina, ina son miji na ya na so na da kyar ma ya hakura ya bari na zo saboda baya so ina yin nesa da shi, dan haka ke ki zauna duk abinda na tsakuro na sammaki tunda haka ki ka zab'awa rayuwar ki ta qare a wahale"

Cikin washe baki da jin Suwaiba ta share mata hawayen baqin cikin da Saudat ke so ta saka mata Goggo Sarai ta ce,

"Yauwa 'yar albarka, ai nasan in kowa zai juya min baya ke kin haifu cikin Saratu ba za ki juya min baya ba"

Duk yanda Baba ya so ya nusar da suwaiba da goggo kin ganewa suka yi dan haka haka aka tashi  kowa zuciya ba daɗi, Saudat ta kafe bazata koma ba, inda Suwaiba tace ita zata koma, Salma da Mama Bilki kuma suna jiyo duk abinda ke faruwa,hankalin Salma ya tashi amma tasan bata da abinda za ta ce su saurare ta a wannan lamarin,Mama Bilkince ta shawarce ta akan ta musu addu'a kawai, hakan aka yi kuwa ta kwantar da hankalin ta suka hau yankan farce bayan sun gama kitson.

" Babyna wai ni yaushe zaki je gaida su Mama ne ga cikin nan ya yi girma kar a Kai minzalin da  baza ki iya fita unguwa ba kuma, tinda ita tana abunnan na mutanen da har yanzu taqi zuwa ta ga dakin ki,"

"Hmmmm kaidai bari abunnan na min zafi ace wai uwa ba zata je taga d'akin 'yar ta ba? Ba komai zan je ko gobe ne na ji dazu Nafee tace su Adda sun zo, kuma Salma ta dad'e a gida ma zan so zuwa duk mu gaisa da su,"

" Eh haka ne, randa na je gaida su ma na ganta ai, Allah ya kaimu goben sai na samu na kai ki da kai na ko?..........❤
[21/07, 7:46 pm] asiyahabibu93: 💅🏼     'YAN ABUJA   💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Sis Ramlat
Baba larens
Aunty Ummu sokoto
Cute one

*Waɗannan sunayen na sama na kasa goge su a cikin sunaye kusan guda goma da na yi wa dedicating page ɗin nan, da can da ana yawan yi wa mutane dedication sai mutum ya jera Sunan mutane da yawa wanda a zaton shi masoyan shi ne na gaskiya na haqiqa😂 ashe inaaa kowa da abinda ya kawo shi rayuwar ka,dama bahaushe yace ba a San maci tuwo ba sai miya ta qare, tabbas rayuwa cike take da qalubale kala kala, wanda ya baka dariya watarana zai saka kuka, wanda ya sa ka kuka watarana zai saka dariya,Ya Allah ka ci gaba da yi mana zaɓi na alkhairi ka haɗa mu da mutanen kirki ka nesanta mu da na banza, Allah ka sa mu zamanto mutanen kirki a wajen mutane ka tsare mu cin amanar wanda suka yarda damu Ameeen...*

Page 19:

Yau Salma tun asuba ta tashi da matsanancin ciwon kai da mara, in da Talle hankalin shi ya tashi ba kadan ba,tsoron shi bai wuce a ce yau 'Yar mutane ta mutu a hannun shi ba,shi dai tun farko dama ba wani son ta yake ba kyan ta da dirin tane ya rud'e shi,ko ba komai ya more ta yanda ya kamata,yanzu haka ya k'yalla ido ya hango wata shi yasa ya fara tara 'yan kud'ad'en da zai yaudaro ta, ba zai yu kuwa ya kashe kud'in sa a jinyar Salma ba, tun da dama wa'adi ya debar mata lokaci na cika zai auna ta tai gaba,zaune yake a kujerar shi ta aiki a farfajiyar gidan ya lula duniyar tunani a hankali ya fara magana ya na fad'in,

"Anya zan iya jiran lokacin da na ɗebar mata ya cika kuwa ? kawai bari Alhj ya fita nan dai da Kano na auna ta gida, nace sai nazo ba shikenan ba ta zauna ta jira ni idan auren da nake nema be samu ba na d'akko ta kan nan ta ji sauqi, idan kuma auren ya yuwu na aika mata takardar ta kowa ya huta, ko kuma yanzu in na shiga na sallame ta a rabu gaba ɗaya,"

Ya na nan zaune ya na magana da kan shi ya ji Alhjn na kiran shi, da gudu ya fita, ya je ya durqusa ya gaida Alhaji sannan ya ce

"Gani Alhaji," Alhaji ya ce,

" To ga wannan a kula da gida, ni zan tafi wannan karon zan ɗan kwana biyu gaskiya a gida ban dawo ba, dan kasan na faɗa maka amarya ta ta samu qaruwar d'iya mace, so ina ganin zan ɗan jima kaɗan fiye da yanda aka saba, a kula da gida, kar na dawo na ji shigen labaran dana saba ji, ba zamu kwashe da kyau ba Talle"

Gyada kai yake kamar qadangare alamun ya ji gargad'in uban gidan nashi,can qasan zuciyar shi kuwa Allah Allah kawai yake yi ya tafi shi kuma ya ɗauki mota ya kai Salma tasha ya dawo, kar ta mutu a hannun shi.

" Allah ya kiyaye Oga ba zaka taɓa samun wani labari mara daɗi ba"

D'aga kafad'a Alhj ya yi sannan ya ce,

"Ruwan ka Talle kowa ya yi da kyau zai ga da kyau ai"

Alhaji na fita Talle ya rufe gate ya koma d'akin da gudu,samu ya yi Salma ta dan samu dama ba kamar yanda ya barta ba, ta fito daga toilet da alama amai ta yi,cikin hanzari da d'aure fuska ya ce mata,

" Ke haɗa kayan ki yau zaki je ganin gida"

Cikin kad'uwa tare da murna, a gefe d'aya kuma kunya da tashin hankalin da wanne ido zata kalli su Juwairah da Mama Bilki ne suka mamaye ta, Uwa uba kuma Goggon ta, tace mata waye mijin ta idan ta je gida driver ne ko mai gadi? Zubewa ta yi a katifa cike da wani irin had'ad'd'un yanayi mabanbanta da suka cud'e mata, a hankali ta furta,

" Nikam Sweet na fasa ba yanzu ba ka bari na murmure, sannan mu dan samu kuɗi, ko a haka zan tafi ganin gida, ai sai a zage ka a ce baka kula da ni" 

"Ah ah a zage ki dai yo ni meye nawa a ciki? in zaki miqe ki miqe ki kwashi dan abinda zaki iya dan kin ga ni daga yanzu ma barin gidanan nan zan ko kin dawo ba ganina zaki yi ba nima na bar aiki anan daga yau, dan na kwashi rabona wajen Alhj, qauye zan koma, na ji da iyalina, kuma dai ba sanin Sunan qauyen mu ki kai ba, ba kuma ki san hanyar bama, dan haka in kin tafi ki manta da wani mai suna Talle, ko in ce Alhj Mansur da kika taba aura, ki manta kin sanni, sai dai in kin tashi tuna ni ki min godiya a ranki na sama maki hanyar zuwa ABUJA, harda qauyen ta ma, dan haka ga wannan"

Takarda da kuɗi dubu goma cass ya miqa mata, a zaunen ta daskare, bata gaskata me yake faɗa mata ba sai da ta ji tsawar shi yana maimaita mata da kuma bata umarnin ta tashi su gudu dan kuwa tana b'ata masa lokaci zai fita ya gudu nashi waje shima, wanda qarya Talle yake mata ba inda zai gudu kawai sanin bata ko san sunan inda suke ba shi ya sa shi fad'in haka, baya son ta yi tinanin dawowa rayuwar shi kwata kwata.

Miqewa ta yi da taimakon shi saboda wani irin jiri da tashin hankali da ta ji ya mamaye jin ta da ganin ta,nan take ciwon kan ta ya dawo sabo dal,da kyar ta samu natsuwa ta ɗan shige ta ta fara haɗa kayan ta a haka ta gama komai, ta kasa tambayar shi dalilin yi mata wannan wulaqancin, ta kasa cewa uffan saboda kalamai sun qauracewa bakin ta.
Chapter 31 · 0% Book details