← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 61

Sashe 40

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jummala ce ta fito daga d'akin su da rarrafe saboda azabar ciwon cikin da ya sako ta gaba sai  murqususu take yi, cikin tsawa Talle da ke zaune ya na sauraron rediyo ya na aswaki zaune Saman tabarma ya d'aga kai ya kalli Jummala ya ce,

"Ke meye hakan zaki zo kina ma mutane kuka, kin gama aikin da na saka ki ne?"

Cikin kuka da tashin hankalin da take ji a jikin ta ta buɗe baki zata yi magana sai maganar ta maqale ta kasa fita,wani abu ta ji ya taho da gudu zai fita ta qasan ta, jini ne ya tsinke mata, nan da nan ta faɗi a wajen tasuma tsabar azaba, a gigice Marka ta yi kan ta,shi kanshi uban gayyar ya tsorata da ganin jinin da ke zuba a jikin Jummalar,daukar ta ya yi a hannu ya ɗora ta a kan machin ɗin shi, marka ma ta hau ta riqe ta, asibitin qauyen suka kai ta, bayan bincike da gwaje gwaje likita ya tabbatar masu da b'ari ta yi, sakamakon ta sha wani magani na zubda ciki, ga kuma jini yaqi daina zuba a jikin ta, suna buqatar a sai mata jini a qara mata zasu yi iya qoqarin su su tsaida jinin, Talle ne ya kalli matar shi ya ce,

" Sai ki fito da kud'ad'en da kike ajewa na tarin auren su ai mata magani ko"

Ya qarasa maganar cikin haɗe fuska, kallon shi ta yi ta sunkuyar da kai da sauri, duk wanda ya hanta a wannan yanayin bai san halin ta ba zai ce zalintar ta mijin ta ke yi, a sanyaye ta ce,

"To bari na koma gida na d'akko"

Dan rashin mutuncin Talle ko duba halin da Jummala ke ciki bai yi ba haka ya na gani Marka ta taka a qafa ta d'ebi hanyan jiki duk ya mace mata ba wannan cikar da take yi da izzar nan.

Kafin ta isa gidan ne ma likitan ta fito, take sanar da Talle Jummala dai babu ita, sakamakon shan maganin zubda ciki da ta yi ba bisa qa'ida ba shi ne ya yi sanadin zub da jini mai tarin yawa a jikin ta, kuma sun kasa tsaida jinin har rayuwar ta ta qare, dafe kai Talle ya yi, nan take nadamar rayuwar shi ta baya ta baibaye shi, kuka yake kamar qaramin yaro, nan suka samu wani mai machine d'in ya taimaka masa ya nemo mai motar da zasu kai ta gida, mai machine d'in kuwa tasha yaje ya samo masa motar, Tallen ya biya shi kud'in ya masa godiya, a motar aka maida su gida shi da gawar Jummala, Marka na shirin fotowa ta koma asibiti taga an fito da gawar Jummala, zubewa ta yi a qasa ta hau kuka da bori tare da kururuwa.......

💅🏼    ' YAN ABUJA   💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 24:

Saudat ce zaune a tsakar gida bata jima da aiken yaro ya siyo mata gasasshen kifi mai haɗe da chips da ake gasawa ba a wani suya spot a farkon shigowa layin nasu da ta saba ci tun lokacin 'yammatancin su, Goggo Sarai kawai ta iya bawa ta sa saura a gaba ta na ci ta na kora maltina mai sanyi, Salma mai ɗauke da ciki ce ta haɗiyi yawu saboda ranta ba qaramin biyawa ya yi ba,amma haka ta danne kwad'ayin ta dan ta san ba bata Saudat za ta yi ba,sai da ta ga ta kammala ci ta wanke hannu ta koma ta zauna a kujera ta na latsa waya sannan ta isa wajen ta ta gaishe ta, a daqile ta amsa ta na karkad'a qafar ta ɗaya da ta ɗora Saman d'ayar,cikin wani maqasqancin kallo ta ce da Salma,

"Meye ki ka zo ki ka tsaya min a ka,idan gaisuwa ne ai mun gaisa ko sai a yi gaba tunda an sauya uwa,idan kuma wani abu ki ke da buqata ki yi gaggawar sanar da ni dan bana so a tsaya min aka"

Murmushin takaici Salma ta yi,nan take ta hau tuna baya yanda yayun nata ke ji da ita suke ɗora ta a hanyar karb'ar kud'in maza, ba su jin kunyar nuna mata yanda za ta yi wa namiji kwarkwasa da taɓa bikin shi san ya bata kuɗi shi ne yanzu dan ta zaɓi hanya mai kyau suke gudun ta, cikin magana mai cike da ladabi ta ce wa Saudat ɗin,

" Adda Saudat dan Allah zuwa na yi ki ɗan bani koda dubu d'aya ce ina son in ɗan ja jari ne ko Saida gishi da omo ɗan qulli ne in fara yi a cikin gida, saboda zaman haka baya min daɗi ba kud'in kashewa,ke ma kuma ina mai baki shawara da ki nemi abun yi da kud'in da ya rage maki tun kafin su qare saboda yanzu kin ga kin saba da kudi, randa kike da buqatar su kika rasa ba qaramin damuwa zaki shiga ba"

Tunani Saudat ta shiga yi mai zurfi, can ta nisa tace,

"Gaskiya kin ce wani abu kema, zan baki dubu biyar ki ja jarin, ni kuma zan fara kasuwanci ta waya da naga qawaye na da na yi a whatsapp da facebook suna yi, ana samu sosai in ka riqe amanar mutane, sai kaga ka samu riba mai yawa kana daga zaune"

"Yauwa Addana na gode sosai, sai wata magana kuma mai mahimmanci da nake so mu yi ni da ke, ina son ki gane Mama Bilki mace ce mai kirki tana matuqar son mu, sai dai tabbas tana kishi da Goggo, wanda wannan dole ne a zaman kishiyoyi dama,shiga wannan kuma ba hurumin mu bane mu kau da kai akan wannan mu bar su su yi kishin su after all miji ɗaya suka haɗa,abinda kawai za mu yi shine mu yi masu biyayya dikkan su a matsayin su na iyayen mu,"

Shiru Saudat ta yi domin maganar qanwar ta ta yau tana shigar ta dan gaba ɗaya ba qarya a ciki amma akwai nau'i na girman kai da taya Goggon su kishi a zuciyar ta,dan haka sai ta yatsuna fuska ta ce,

"Hmmmm zan duba maganganun ki na gani"

Sannan ta miqe ta d'akko mata kud'in da ta alqawarta zata bata ta bata, duk abinda ya faru akan idon Goggo Sarai ya faru, sai dai bata ji kalaman da suke yi ba ta dai ga an bawa Salma kuɗi,magana take cikin b'acin rai,

"Habaaaa Salma ai innice ke yanda na canja uwa, yan uwan ma canja su zan yi, auhoooo ba zaki iya canja yan uwa ba saboda su masu arziqi ne Zaki yi roqo za a baki , amma ita uwar ki tinda talaka ce shi yasa ki ka sauya ta"

" Ni fa Gogga ba haka bane, ya kamata ki buɗe idon ki ki gane inda gaskiya ta dosa, ki daina rufe idon ki ki na yin abinda bai kamata ba"

"Rufen baki sallamammiya kawai, an yi asiri da tuggu kala2 an raba ni dake, to ki je nima na huta da dawainiya da ɗan wani"

Juyawa ta yi tabar wajen Salma kuwa cikin qunan rai da baqin cikin halayya ta uwar ta ta shige d'akin Mama Bilki, wadda ta ji komai da ya faru, fad'awa kan cinyar ta  Salma ta yi tana kukan takaicin hali irin na uwar tasu, shafa kanta kawai Mama Bilki take, bata furta mata komai ba,cikin kuka Salma ta ce,

" Mama ni fa ba kwad'ayi ne ya sa na tambayi Adda Saudat kudi ba, na tambaye ta ne kawai saboda ki na ganin ko tirare bani da shi, ga shi yanzu sai da alimun ko lemon tsami nake amfani a hammata ta a madadin tiraren,da ace ina sana'a yaushe zan zauna haka? Tunanin da na yi na ina sana'a kudin zasu taimakan wajen kula da abinda ke ciki na da ni kai na shine ya sa na tambayi Addah Saudat kuma ta bani dubu biyar na ja jari, shine Goggo take fad'an maganganu marasa daɗi akai na da abinda ke ciki na"

" Hakuri zaki yi Salma uwa ba abin wasa bace, dole mu yi mata biyayya matsawar ba sab'on Allah a duk abinda ta sanya mu,dan haka ki yi hakuri, to tin da kin samu jarin yanzu me zaki na yi na siyarwa?"

Tashi zaune Salma ta yi ta share hawayen ta sannan ta ce,

" Mama Bilki ni da ina son na fara saida gishiri da omo da ɗan qulle qulle na gida, amma yanzu da na samu wannan kud'in mai yawa sai na ji ina son in fara Saida Meatpie, naga kina da injin yin taliya, kuma na kula kayan flour ana cinikin su, in ba su ba ban san me zan iya yin sana'a akai ba kuma"

Murmushi Mama Balki ta yi sannan ta ce,

" Hakan ma shawara ce mai kyau, Allah ya sanya albarka a ciki"

" Ameen mamana"

Kwantar da kanta ta sake yi a jikin ta ita kuma tana shafa gashin kan Salman a hankali.

******************************

Yau kusan sati ɗaya da kwana uku kenan Suwaiba na kwance tana jinyar qirjin ta da aka fafe wa albarkatun wajen, Alhj Salihu dayaga zata farka sai ya danna mata allurar bacci ta koma, ko ya shaqa mata wata powder ta koma baccin, a haka ta yi wadannan kwanakin,shine yake yi mata wanka ya canja mata kaya,sannan ya saka mata ruwa da allurai na kashe zafin ciwo da anti biotics,ya zama babban likita kawai a cikin gidan shi dan ya kula da Suwaiba, a haka sai da ya kula wajen ya warke tas sannan ya kyale ta da allurai na bacci da yake mata.

Ranar da ya bar ta kuwa bai yi mata allurar baccin ba da ta farka sai ta ji kan ta kamar an ɗora mata abu mai nauyi, da kyar ta tashi daga gadon ta ta isa gaban madubi a hankali ta d'aga rigar ta ta na kallon qirjin ta, nan take wasu hawaye masu azabar zafi suka hau zuba a kuncin ta, ina dukiyar Fulanin ta suke ne, me ya same ta?
Chapter 40 · 0% Book details