Sashe 50
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Oga ina son barin qungiya ba dan komai ba sai dan ina son na koma tsaftatacciyar rayuwa na tsira daga azabar da Allah zai yi min,sannan abinda ya faru yau da Kalla ya qara min son barin wannan qungiyar"
Nan take ya kwarorowa Oga Zaks duk abinda ya faru da Kalla da shi kafin hatsarin da ya yi, nan danan jikin Oga Zaks ya ɗauki rawa, qaton cikin nan kamar ana buga ganga haka yake qara da karkarwa, maganganun sun shige shi sosai sun bashi tsoro,cikin rawar murya Oga Zaks da ya zama shi ne ya qirqirar masu wannan ƙungiya ta shaid'an ya ce,
" To salihu ba za ai haka ba ka fita kai ɗaya? Ni kai na na wa'azantu da wannan abinda ya farun,yau kuma a yanzu zan tara mutanen mu na sanar da su abinda yake faruwa kuma ni da kai mun shirya barin wannan ƙungiya ko da za mu rasa ran mu kuwa, zaɓi ya rage wa sauran,wanda yaga zai fita ya biyo mu, wanda yaga zai zauna ga waje nan, amma zan so ace yanda ni ne na assasa wannan qungiya na rusa ta da kai na, dan ko na tafi zunubin zai ci gaba da bina"
Wani irin farin ciki ne ya lillibe Alhaji Salihu dan bai taɓa zaton hakan ba, ya zaci zai sha wahala kafin ya amince mai, waya yasa ya kira mutanen su baki ɗaya,kusan awa biyu suka ɗauka kafin kowa ya hallara, fuskar Alhaji Salihu da ta sha kuka ya ba wa kowa mamaki, nan take kuwa Oga Zaks ya fara zayyana masu komai, cikin qanqanin lokaci wasu da dama suka aje makaman yaqin su, wasu kuwa suna ganin ai su akwai sauran lokacin tuba,tsawar da Oga Zaks ya daka masu ce ta dawo dasu daga cece kucen da suke ta yi, cikin bada umarni ya ce,
" Na yanke hukunci wannan qungiya rushe ta zan yi da hannu na kamar yanda na kafa ta, wanda ya sake kafata shi ya sani, amma ni kam na gama , dan haka daga gobe zan rushe ta, tsakanina da dodo ko kashe ni ya yi babu komai fata na shine na kubuta daga cutarwar shi da ikon Allah,ina neman gafarar Allah ya yi min afuwa, ya ba wa wadan da na zalinta ikon yafe min a filin qiyama"
Nan da nan sai ga Oga Zaks na yin kukan nadama,tabbas Allah shi ne mai shiryar da duk wanda ya so a lokacin da ya so, basu rufe baki ba suka ji gidan na wani irin qara mai firgitarwa,da jin haka kuwa mazajen nan suka hau gudun ceton rai, Alhaji Salihu ne ya ke ta qoqarin taimaka wa Oga zaks su gudu ya kasa saboda tsabar qiba da nauyin shi,sai ya kamo shi su tashi sai ya koma shab'ar ya zauna,daga ƙarshe dai dole ya dakatar da shi ya ce,
" Salihu kai ta kan ka kawai, ni nasan tawa ta qare, da wannan uban tumbin nawa kake tsammanin samun gudu a gareni? Ka dube ni fa ka gani na ninka ka sau bakwai, ka barni kawai, abin da na aikata zan girba, a shirye nake dan na sadaukar da rayuwa ta na fanshi taku, saboda ni ne na fara komai, i think it has to end with me, just go now ! Ka gudu ! Kar ka juyo kar ka dawo baya, kar ka manta da ni ka dinga nema min gafarar Allah idan ka yi tsawon rayuwa,"
Tura Salihu ya yi da qarfi a dai-dai lokacin da wani qaton baqin zaki ya fito daga wani baqin d'akin da suke ajiye mutanen da suke tsafi da su yayo kansu, Salihu ɗiba ya yi da gudu ya bar wajen, Oga Zaks salati kawai yake ya na Kiran Sunan Allah tare da neman gafara a wajen Allah,tsabar tsoro da shiga tashin hankali har ya cika wandon shi da fitsari shataf bai sani ba, nan take ya hau tunanin ashe haka waɗanda suke bawa dodon tsafin nasu suke ji kafin su mutu, nan take ya ji qirjin shi na wata iriyar muguwar bugawa,cafka zakin nan ya kaiwa wuyan shi ya hau cinye shi,shure-shure ya hau yi na azabar fitar rai kafin daga qarshe ya yi shiru alamar ya mutu,Oga Zaks kam an tafi inda Kalla ya tafi, Salihu kuwa gudu yake kamar zai tashi sama , mota ya gani da makulli a jiki me ita wataqila tsabar tsorata ne ya hana shi ci gaba da tada ita ya gudu, dan harda takalmi qafa daya a cikin ta a ajiye, ruwa duk ya jiqe mazaunin driver maybe fitsarin shima ya sake kafin ya gudu,take Salihu ya tada motar ya debi hanyanyar kano dan bai ga ta zama a garin Abuja ba.
******************************
Tinda suka tashi daga bacci suka yi sallah suka hau gyaran gidan nasu tare da yin abincin safe zuwa rana, bayan sun gama ne suka yi wanka suka hau shirin zuwa ganin babyn tasu.
Suwaiba aiki kawai take yi amma Jikin ta duk babu kwari,sannan ga wata iriyar fad'uwar gaba da take ji,Saudat ma in banda sharar d'akin su ba abinda ta tsinana, Salma da Suwaiba ne suka fi yin aikin gidan, ta rasa dalilin da ya sa take jin wani yanayi a tare da ita,ko da ta sanar da Mama Balki sai ta koyar da ita wasu addu'o'i, nan take ta yi ta maimaita addu'o'in a bakin ta, bayan sun gama shiryawa ne suka yi wa su Goggo Sarai Sallama su ka ɗauki hanyar gidan Juwairah me jego, sun isa dai-dai Jabeer ya fito riqe da towel din da yake gasa mata jiki da shi sai suka tsaya kallon shi,daga bayan shi kuma Juwairah ce ta fito tana fad'in,
" Ni dai gaskiya a canja min me yi min wanka a gidan nan kai gaba ɗaya mugunta ka ke yi min, ni ban ma taɓa jin inda aka ce namiji ke yi wa mace wankan jego ba dan h.......... "
Maganar ta ce ta maqale dan ganin yayun nata na shigowa, niyyar ta ta koma bandakin dan juyawa ta yi tare da damqe bakin ta zata shige bayin, cikin dariya Saudat ta yi sauri ta isa ta ruqo ta,
" Me Yah Jabeer din ya ke maki? In kina son a canja maki mai wanka sai na dinga yi maki, amma ni sai ruwan ya tafasa sau uku sannan zan yi amfani da shi"
Zaro ido waje Juwairiyyah ta yi sannan tace,
" A'a Adda Saudat a barmin Yah Jabeer ɗin mu lallaba a hakan"
Dariya suka kwashe da shi, Jabeer yace,
" ku ji yarinyar nan fa, wai zata lallab'a a haka sai kace wani muguntar nake yi mata"
Nafee ce ta amshe da cewa,
" Hmmmm Yah ayi shiru kawai da wannan maganar amma ko d'azu na jiyo qarar ta"
Hararar ta ya yi yace,
" Suwaiba ku shiga ciki mana kuka tsaya a waje"
shiga suka yi har me jegon, Nafee ce ta bar d'akin sakamakon kiran ta da Innarmu ke yi, zuwa ta yi ta bata wani kwanika biyu ɗauke da abinci ta kawo wa juwairah, amsa ta yi ta tafi bangaren juwairah, sallama ta yi musu kafin ta shiga suna ta hira kowa na yaba kyaun jaririyar da sunan ta,
"Wannan suna na :yan gayu anya kowa zai iya fada kuwa kar a je a b'ata mata suna kin san halin mutanen mu"
Cewar Salma, dariya Nafee ta yi da ta qarasa aje kwanon gaban Juwairah dake shafa man kad'e a cikin ta ta ce,
"Ai jiya sai kun sha dariya dan daga Innarmu har Abban mu basu iya fada ba, Innarmu Abaras take cewa Abbah kuma Abra"
"Ai ko wannan suna zan so jin shi a bakin Goggo"
Cewar suwaiba da ta tuna da Goggo Sarai, dariya suka bushe da ita dikkan su sun san a kwai case din fad'an Abrar a bakin Goggo sarai, Juwairah ce ta gama shiryawa Suwaiba ta d'aure mata cikin ta, sannan Jabeer ya shigo ɗauke da plate da Spoon da cup sai tea spoon, gaishe shi suka yi dikan su ya amsa su cikin sakewa, nan dai suka yi masa barka da samun wannan qaruwar da aka yi mai albarka, godiya ya yi ya isa gun kwanukan ya buɗe, farfesu ne na naman qaramar dabba, yasha kayan qamshi irin na jiya harda rid'i a ciki, gefe kuma kabewa ce innar mu ta dafe ta ta yi laushi ta dame ta ta yi kamar kunu, sannan ta zuba masa madarar shanu mai matuqar yawa sai zuma, zuba mata ya yi a cup din ya zuba mata naman a plate ya haɗe fuska alamar ba wasa ya ce,
" Gashi maza taso ki ci ki shanye, dan bana son kina zama da yunwa"
Turo baki ta yi gaba ta ce,
"Ni fa na qoshi Yah Jabeer,dazu da asussuba na qarasa cinye naman jiya saboda yunwar dana tashi da ita, yarinyar nan ci gare ta kamar Innar ta Salma"
Dariya suka sanya dikkan su, Jabeer ne ya ce,
" Ai kuwa baki isa qoshi ba da dan ragowar naman nan, in baki matso kin fara ci ba zan maki d'ura a gaban su," zaro ido ta yi waje sai gata a qasa ta saka pilo ta haɗe qafafun ta waje ɗaya ta miqe su tare da danna hannun ta a plate ɗin naman.
( haka ake so mai haihuwa tana zama, kai ko ba haihuwa ba ma, ba a son zaman nan na ware qafa da wasu matan ke yi, kabewa kuma da madarar shanu da zuma duk wadda ta haɗa ta sha zata bada labari bazan ce komai akai ba)
Kaiwa baki ta yi ta fara ci, wani daɗin da ya ziyarce ta ne ya sa bata san sanda ta cinye ba ta shanye kabewar dika,murmushi Jabeer ya yi da suke ta hira da qannen na shi ya ce,
"Da kyau yarinyar kirki"
Sumbatar Saman kan ta ya yi sannan ya dauke kwanukan zai fitar Salma ta yi saurin Karb'a dan ta fitar da su cikin jin nauyin shi ta ce,
"Haba yayah muna nan ai sai ka bar mana aikin in mun tafi ka ci gaba"
Murmushi ya yi ya sakar mata yace tare da cewa,