← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 61

Sashe 43

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matsawa ya yi zai riqe ta ta ko falla da mugun gudu ta yi d'aki ta na ihu, kan ya isa ta fara qoqarin rufe qofar,ya yi saurin saka qafa ya tokare, ihu ta zunduma tana bashi hakurin ya yi mata rai ta tuba, ya maida ma baban ta ita, dan yanzu ta tsani Goggo Sarai shi yasa ko tunanin ta bata yi ba, ya taimaka kar ya tsotse mata sauran jinin nata da ya rage, tura wa ya yi da qarfi ya janyo ta jikin shi cikin ɓacin rai ya ce,

" Ke! Ki nutsu dalla malama kar ki taran mutane ni, in da zan kai ki da tini  ban kai ki ba ko kuwa sauran duk sanin an je ki ka yi? ba sai yanzu dana sanar dake bane ki ka sani? Na faɗa maki ne saboda ina son na maida ki gidan ku da kaina, in yaso duk abinda zai min ya min, na sadaukar da rayuwa ta domin taki ta tsira, Suwaiba wannan shine iya adadin soyayyar da nake maki, ina son ki suwaiba zan iya sadaukar da rayuwa ta saboda taki ta tsira"

Ya qarasa maganar shi a hankali wanda ya sa jikin ta yin sanyi, qanqame shi ta yi tana kuka sosai,Itama ta ce,

"Ba na son na rasa ka Alhajina, nima ina son ka sosai, ban san sanda na fara son ka ba nima, a da kam tabbas kud'in ka nake so, amma yanzu kai nake so, bana son abinda zai raba mu"

Jin kalaman ta ne ya sanya Alhj Salihu kuka kamar wani yaro,haka so yake,shi  SO ba ruwan shi da girman ka ko qanqantar ka in ya shige ka yana saka aikata abinda ba hurumin ka bane aikatawa, haka suka yi ta kuka ba mai lallashin wani, ba su ankara ba sai kiran sallan farko suka ji na asuba, kasancewar dama bai dawo gidan da wuri ba tun safe da ya fita.

Suwaiba tashi ta yi daga jikin Alhajin nata jiki duk ba k'wari,yau ce rana ta farko a rayuwar ta da ta yi alwala dan wani abu na damun ta take son ta roqi Allah akai dan ya yaye mata damuwar ta.

Shima Alhaji daya ga haka alwalar ya yo, ya kabbara salla ta na bayan shi suka yi nafila,suka hau addu'a akan Allah ya yafe masu, ya gafarta masu zunuban su, ya kubutar da su daga wannan al'amari da suka tsinci kansu a ciki, bayan sun idar da addu'ar ne suka yi sallar subh  suka tashi suka hau gado, bacci mai nauyi ne ya dauke Alhj amma ita kuwa inaaaa yaushe taga na barci ana shirin kaiwa matsafi ita, lallabawa ta yi ta buɗe wajen da take aje kud'ad'en da yake bata ta d'iba, ta dakko akwatin ta ta loda kayan ta a ciki, ta fita ta dauki makullin mota babbar ciki a motocin shi,Saida ta loda kayan ta a ciki sannan ta hau ta nufi gate mai gadi ya buɗe mata ta fice ta bar gidan a guje.

Hanyar kano ta ɗauka duk da cewar bata gama gane hanyar ba ta tabbata zata iya kai kan ta gida,haka suwaiba ta dinga bin rubutun Sunayen garuruwan da ke kan hanya tana shara gudu a Saman titi har ta isa cikin garin Kano

Haka ta isa gida a firgice, Alhj kuwa bai farka ba sai azahar, miqa hannu ya yi dan ya tab'o Suwaiba yaji wayam, bai kawo komai ba a ran shi dan ya zaci ta shiga toilet ne, komar da kan shi ya yi ya lumshe ido,tunani yake ya kamata ya haɗa mata kaya ta tafi gida in yaso duk yanda suka yi da Oga Zaks daga baya ya dawo da matar shi, miqewa ya yi zai shiga toilet din in ma wanka take suyi tare ya na shiga yaga wayam ba kowa a ciki, fita ya yi palour nan ma bata nan, leqa kitchen da sauran dakunan ya yi yaji shiru bata nan, a hargitse ya fita waje wajen gate man ya ce,

"kai Audi ina Hajiya?"

" Alhj ta fita da kaya da motar ka babbar tun da sassafe"

Cike da damuwa ya hau shafa kanshi, komawa ciki ya yi zuciyar shi cunkushe da tunani kala kala,shin ya take a yanzu, ta samu nasarar isa Kano lafiya ? Tinda iya sanin sa bata gama kware a tuqi ba, gashi a yanzu tana cikin halin tsoro da firgici, kar wani abu ya je ya same ta a hanya.

Ɗaya bangaren na zuciyar shi ya ji haushin yanda ta iya guduwa ta bar shi ba tare da sun yi koda sallama bane,ta san ya na son ta ba zai bari wani abun cutarwa ya sake rabar ta ba, kuma Itama  ya ga soyayyar shi a tare da ita.

Wayar  shi ya dakko ya hau kiran ta dan ya ji ina take idan kanon ma ta gudu ya ji shin ta isa lafiya ko ta na hanya ne bata isa ba,wayar na ta ringing bata d'aga ba, hakura ya yi da Kiran ta ya je ya yi wanka ya yi sallahr da ya jima da dena yi sannan ya fita ya bar gidan.

Qarfe uku na rana a qofar gidan su ta yi mata, hankali tashe ta kashe motar  ta buɗe ta fada gidan tana kuka, da sauri Salma da Saudat dake tsakar gidan suna murza meatpie din da Salma ke sana'ar shi a yanzu suka je za su taro ta, sai dai ganin ta shiga da uban gudu ne ya sa suma suka so kwasa da gudu amma suka yi ta maza suka tsaya, tsayawa suka yi suga me ya koro ta shiru ba wanda ya biyo ta,ta na qarasa shiga ta fada jikin Salma tana kuka tare da fad'in ,

"Na shiga uku Salma na halaka kai na da kai na, Saudat kinyi gaskiya Alhj da kanshi jiya ya tabbatar min shi ɗan qungiyar asiri ne masu shan jinin mutane da tsafi da sassan Jikin su, duba ku gani yanda aka maida ni mata maza"

D'aga masu rigar ta ta yi suka ga yanda qirjin ta ya koma babu komai fayau kamar filin ball,a daidai nan Goggo Sarai ta fito cike da tashin hankali sakamakon jin abinda Suwaiban ke fada............
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 ' YAN ABUJA 💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 26:

Kamar yanda mata da dama ke kokarin kyautata wa mazajen su ta fannin kula da gida, kula da kawunan su ta bangaren tsaftar Jikin su, mahallin su da ta Yaran su, ya na da kyau su ma maza a same su da kula da tsaftace Jikin su da duk abinda ya kamata su yi dan faranta wa matan su rai da tabbatar da cewar matan su sun dawwama cikin son su da qaunar su tare da burge su,ba ya daga cikin adalcin zamantakewar aure ace koda yaushe mace itace za ya yi ta kokarin faranta wa mijin ta rai tare da neman mallake shi shi kuma miji ya zauna ba ya wani yunqurin burge abokiyar rayuwar shi.

Wannan dalilin ne ya sanya Jabeer zuwa aski aka wanke masa qafar shi tass, duk da a baya kafin Juwairiyya ta samu ciki ita ke wanke masa qafafun da har sai sun yi karr da su kamar na jinjiri saboda ta na amfani da kayyakin da muke da su na yau da gobe wajen gyara qafa, kamar su lemon tsami,baking soda,gishiri kaɗan, toothpaste na kamfanin Colgate sai zuma, ta na haɗe su waje ɗaya ne ta juya ta shafe musu qafafun su da shi idan ya kai minti 15 sai ta wanke masu da soson wanka da ruwa mai d'umi ta tsane masu qafafun su idan sun tsane ta shafe su da man kad'anya da ta haɗa da man kwakwa da man zaitun.

Hannun shi riqe da qaramar ledar da ya siyo mata shaving stick da sweets ya shiga gidan,duba wa ya yi bai ganta a parlour ba,direct d'aki ya shiga dan ya san dole ta na can idan bata zaune a parlour ko tsakar gida ko kuma wajen Innarmu,ya na shiga kuwa ya gan ta a d'akin,cike da mamaki ya kalle ta ya ce,

"Yanzu baby idan ki ka yanke fa? Na ce ki jira a yi sallah na je aski na dawo zan taya ki tunda yanzu ba ki iya yi da kan ki amma kin kasa jira na, kuma kin san reza sai dai ta ji maki ciwo amma still ki ke yi da kan ki,ni ban san me yasa yanzu ki ke kin jin magana ta ba,bani nan"

Kwalla ce ta taru a Idon ta ta miqa masa rezar hannun ta ya Karb'a ya ajiye a gefe sannan ya rufe qofar dole na koma parlour na zauna zaman jiran masoyan.

Bayan mintinan da baza su wuce biyar ba Juwairiyyah da Jabeer suka fito sai tura baki take ita a dole fushi take yi an yi mata faɗa, ba tare da Jabeer ya kula ta ba ya wuce wajen murhu inda ta ɗora ruwan da ta ke haɗawa na tsarki shi ya ɗauka ya juye a babbar buta ya surka mata daidai yanda zai ɗauke ta ba tare da ta ji zafi ba ya miqa mata.

(Abinda ake tafasawar sune kaninfari ,ganyen magarya, lalle kaɗan da ɗan gishiri sai ganyen garahuni)

Jabeer gani ya yi ta karɓi butar kanta na kallon wani waje ta na tura ciki gaba da baki murmushi ya yi dan kuwa ya san ba halin ta bane, ta fara yi masa irin haka ne tun sanda suka gano ta na ɗauke da ciki, abu kaɗan za a yi mata ta yi Fushi,dan haka cikin sigar lallashi ya ce,

" Haba Juwaireren Mama Juwaireren Yah Jabeer, me kuma ya faru, me kk so na yi maki? Ni ne na yi maki faɗa? To yi hakuri kin San fa ni gaba ɗaya bana jin daɗin rasa murmushin nan naki mai kwantar min da hankali,ni fa da ki hana ni murmushin ki gwanda ki hana ni ruwan randar sanyin nan idan na dawo daga kasuwa a gajiye"
Chapter 43 · 0% Book details