← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 61

Sashe 11

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A d'aki ma Juwairiyyah Bata bar jabeer ba sai da ta gyara mai jiki tare da feshe shi da tirare, palour ta dawo da shi yana biye da ita kamar raqumi da akala, abinci ta zaunar da shi ta bashi, yana ta santi

" kaiiiii amma ba qaramin birge ni ki kai ba, kin san rabona da faten wake har na manta kuwa?"

"Alhamdulillah na ji dad'i da yabawar ka Hubby"

kusa da ita ya matsa sannan ya ce,

"Ai dole in yaba saboda ke din ta daban ce, komai naki daban ne,Allah ya barmu tare har a aljannah"

Murmushi suka yi dikan su suka ci gaba da cin abincin su, kiran sallar magrib ne ya katse su suka tsaya suka saurara sannan suka bi kiran sallahr suma, bayan an idar ne suka yi addu'ar da ake yi ba yan idar da kiran sallah,wato

" Allahumma rabba hadhihidda'awatittammah, wassalatil qa'ima, a ti muhammadal wasilata wal fadeela waddarajatirrafee'a wab'athhu maqamam mahmudan lladhi wa adtah."

Sannan suka dora da salatin annabi ingantacce, addu'a suka d'aga hannayen su sama suka yi a tare ita da shi, suna idarwa suka tashi suka yi alwala, shi ya tafi masjid ita ta yi sallar ta a gida, bayan ta idar ne tayi azkar din bayan kowacce sallah ne, sai ta samu ta yi kuma azkar din yamma, tana idar wa ta miqe ta je d'akko dan ragowar abincin nasu ta juyo masu ta kawo ta had'o da ruwa da komai da ya dace ta ajiye a gefe, d'aki ta shiga ta saka rigar baccin ta mai matuqar kyau da daukan hankali, sai ta ɗora zani akai da hijab tana jiran sallar isha'i bayan tayi sallar ne da minti 15 Jabeer ya shigo,abinda ya tsayar da shi kuwa sai da ya biya wajen Innar mu ya gaida su, baban shi na ta sa mai albarka, ita ko ta cinkishe fuska tana hura hanci, daya tambaye ta ne ke damun ta sai ta yi qaryar kanta ke yi mata ciwo, dan yau wuni tai da yunwa bata ci abinci ba, can kuma sai ta saki fuska ta ce,

" kasan da yake bana son faten wake, kuma bana son bawa yar albarkar nan aiki shiyasa, amma da shinkafa zan bata ko gwangwani dayar nan ne ta dafa min, tinda Nafee ita har yau bata iya tsantseni irin na Juwairah ba"

" Ba komai Inmar mu kawo na kai mata za ta yi maki ai, ba zai yu ku kwan da yunwa ba"

Dan haka da sallama ya isa sashen su riqe da ledar shinkafar a hannun sa,daidai Juwairah ta fito daga d'akin ta ta cire zanin ta da hijab din ta, tana qarasa shafa mai a cinyar ta, ko da ya higo tini ta sauya salon shafawar, sake baki ya yi kamar dolo yana kallon ta, qarasa shigowa ya yi ya aje ledar shinkafar a qasa still idon shi na kan Juwairiyyah, juyawa ta yi ta koma d'aki tana tafe tana juya bayan ta tana waigowa tana masa wani mayen kallo da murmushi, ni dai tin da ya shiga suka ja qofar ban qara ganin me suke aikatawa ba sai dai kunnuwa na sun jiyo man Jabeer na sambatu da bana gane yaren da yake yi, sayyarar qafa ta na ja na yi waje, ji nake kamar na kai wa Innarmu gulmar me ke faruwa.

Qarfe hudu na asuba suka fito suka yi wanka tare da alwala mai kyau suka koma dakin su, bayan sun shirya ne suka fara gabatar da nawafeel, kowa ya fara addu'ar shi, Jabeer ne ke hango baqi, a gefen shi dan ba wuta sai ta wayar shi suka kunna, miqa hannu ya yi dan yaga meye a wajen, dagawar nan da zai yi sai ya ga shinkafar da Innarmu ta bashi ce jiya a dafa mata, cikin damuwa da tashin hankali ya ce,

" Ya salam ! Tab lallai da safe na shiga magana wajen innarmu, aiko ni ta yi fa jiya na kawo ki dafa mata wai yunwa take ji, tin safe bata ci komai ba, bata cin faten wake, shine gaba ɗaya na manta"

"Haba Yah Jabeer bai kamata ka manta da wannan mahimmin abu ba kuwa, domin yunwa ba ta da mahadi ai bayan haka Innarmu ce fa ta baka umarnin a yi abu be kamata ka shagala ba gaskiya ban ji daɗin abinda ka yi ba,"

A qasan ranta kuwa jinjina wa Innar mu take wajen iya hada makirci, matar da taci ta tande kwano, har ta aiko wai a dad'a mata in akwai, tace babu shine take cewa ba ta ci, ikon Allah, lallai Allah mai jin qan bawan sa ne mai tinawa da shi a kowanne hali yake musamman idan bawan na yawan neman taimakon Allah a dikkan lamuran shi, da bata zama mai neman taimakon Allah a komai ba da bai taimaka mata jiya ba,gashi bata san me aka qulla mata ba Allahn ta ya kare ta, kiran sallar asuba ne ya katse su daga mayar da magana akan abinda ya faru jiyan Jabeer ya tashi ya fita masjid ana yin sallah ya dawo, ita kuma tayi tata a gida tayi azkar da karatun asuba da take yi kullum ba fashi komai aikin da ke gaban ta sai tayi ko rabin shafi ne kan ta tashi, tana rufe qur'ani ya shigo, lokacin gari ya dan waye, daki suka shige suka ɗan miqe dan su maida bacci,tund Nafeesa ke abin karyawa a gidan, in ba arziqin abin karyawan ma da dama koko kawai zasu dama su sha a ci gaba da rayuwa, har bacci mai nauyi ya fara ɗaukan su suka jiyo sallama daga bakin kofa.........
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA.  💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 8:

Nafeesa ce ta tsaya tun daga bakin kofar shiga sashen su Juwairiyyah ta kwankwasa tare da yin sallama,bayan an bata izinin shiga ne ta qarasa shiga ciki,gaishe da Jabeer da Juwairiyyah ta yi sannan ta kalli Jabeer ta ce,

" Yah Jabeer Innarmu tace wai ka bada shinkafar na kai mata tin da ta yi wuyar dahuwa"

"Inna lillahi,  kin gammu yanzu haka zancen shinkafar muke yi ni gaba daya mantawa na yi shaf dana shigo, dan Allah ki bata hakuri kice yanzu za a dafa mata a kawo"

Dariya Nafee ta yi sannan ta ce,

"Tace idan ka faɗi haka na ce ka bata ta fasa wataran an dafa mata"

"Oh my God yau ya zan yi na iya zuwa gaida Innar mu? Dan Allah Nafee ya kika ga fuskar ta ta yi fushi sosai ko?"

Cikin jimamta lamarin Nafee ta sauke ajiyar zuciya ta ce,

"Hmmmm ba kadan ba kuwa Yah Jabeer, amma tace kar na fada maka ta yi fushi"

Juwairah a ranta kuwa sai tace

'Ina fa zata so ya sani tinda tana son nakasani ta qarqashin qasa'

Ba yanda ya iya haka Jabeer ya ya miqa mata shinkafar yace ta bata hakuri sosai kan ya shigo, fita ta yi da ita tana masa dariyar zaka amsa ne in ka shigo kai da Innarmu ka san halin ta ba ta da sauqi.

Sai da su Juwairiyyah suka taɓa baccin su sannan suka tashi suka yi wanka tare da brush, d'aki suka shiga su ka shirya cikin shiga mai kyau da burge junan su ta qananan kaya, hijab Juwairiyyah ta ɗora akan kayan ta matsattsu da ta yi ma mijin ta kwalliya da su kafin ya fita kasuwa, a tare suka shiga bangaren na su Innar mu lokacin ta gama raba abin karyawa tace akai masu sai ga su sun shiga, duqawa Juwairah ta yi har qasa suka gaisa,

" Ya jikin naki Juwairah,ai Nafeesa ta ce min ba ki ji daɗi bane shi yasa ya ajiye shinkafar bai baki kin dafa min ba duk da tsananin yunwar da nake ji jiyan"

Zare ido Juwairiyyah ta yi cikin duqar da kai da sauri ta furta,

"Da sauqi Innarmu na ji dama sosai alhamdulillah"

" To Allah ya qara lfy, yasa amarya za ai min ko ango, danni na gaji da lafiya sa banga qaho ba aure wata na biyar kenan shiru ba magana?"

Innarmu ta fada a matsayin wasa take yi, amma duk wanda ya kula ya san magana take faɗa mata, murmushi Juwairiyyah ta yi sosai sannan tace,

" Innar mu karki damu komai lokaci ne amare za a samo maki masu yawa da masu kawo cefane har sai kince sun isa haka"

Tana fadar haka ta miqe ta yi wajen Baba Balarabe ta gaida shi, sake baki Innar mu ta yi ta na bin Juwairiyyah da kallon mamaki, shiko gogan be gane magana suka sakar wa juna ba, daɗi ma yake ji a ganin shi Innar shi da matar shi sun fahimci juna sosai akwai shaquwa ta musamman a tsakanin su, tun da har suke irin wannan maganar ga junan su, matsawa ya yi kusa da Innarmu ya ce,

"Akwai abinda zan taya ki ne Innata?"

Murmushin qarfin hali ta yi sannan ta furta,

"Eh toh ba a rasa ba ai,

A qoqarin ta na hana shi ya koma wajen da matar shi take,

Can bangaren kuma Juwairiyyah da Baba Balarabe ne ke gaisawa cikin sakewa da mutuntawa,

" Babana ina kwana?"

"Lafiya qalaou d'iyar albarka, kina lafiya dai ko?"

" lafiya qalaou nake babana"

"To madallah, Juwairah ina son ki yi ta hakuri da wannan Innar taku, wani hali ta d'akko  na daban wanda har ni kaina ta canja min kwata2 ba kamar yanda na santa ba, dan haka kema sai kinyi hakuri, abotakar ta da Goggon ku ba abu ne mai kyau ba, na yi nayi na raba su amma abun yaqi yuwuwa, da dukkan alamu daga can ta samo wadannan sabbin halayen dan kawai kar a zauna lafiya"
Chapter 11 · 0% Book details