← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 61

Sashe 57

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wannan daddad'an labarin ya iske dangi kowa ya yi murna Juwairah ta roqi Jabeer akan ya barta har a gama hidimar tarewar Yan uwan nata kan ta koma, ya amince mata ta zauna amma shi da yamma zai koma Abuja sabida aikin shi, sun bari akan in ta kammala ta sanar da shi sai ya zo ya ɗauke ta, kuɗi ya bar mata mai yawa a hannun ta kan ya tafi saboda hidimar yau da gobe.

Haka Jabeer ya tafi suna jin kewar junan su dan kuwa  basu son abin da zai raba su sai dole,gashi bata san ma ranar tarewar amaren ba ta yi azarb'ab'in cewa a bar ta,haka Juwairiyyah ta dawo daga raka shi jiki ba kwari.

Ta na zama ta ji wayar ta na ringing a gefen ta, dauka ta yi taga Nafee ce cikin murna ta amsa suka yi wa junan su sallama tare da gaisuwa,cike da jin nauyi Nafee tace,

" Matar yaya kunyi min mantuwa fa, kun manta tsimi na ba a sako da shi ba"

" Subhanaka ya raheem, ai ko kinga har yanzu ba wanda ya kula, babu damuwa ai kinga yanda na haɗa maki wancan ko? ki haɗa wani kawai,idan yaso wannan na bawa su Adda Saudat, keee ! Ban faɗa maki ba, an daura auren su ma jiya, tarewa kuma ance ba yanzu ba sai sun shirya magana da mazajen su, iyayen sunce basu buqatar komai sai matan yaran su za a kai masu kawai kin ga kuwa Ina kyautata zaton ba za a ɗauki wani lokaci mai yawa ba za su tare"

Cikin murna Nafee ke addu'ar Allah ya basu zaman lafiya, bayan gama murnar ne tace,

"Ni fa matar Yaya na manta wasu abubuwan ɗan sake faɗan mana pls"

" kai Nafee ko dai angon ya kwashe har da basirar ki ne?"

Dariya suka yi Nafee tace cikin shauqin son mijin nata,

" Matar yaya wato My love daya ne tamkar da ba iyaka acikin mazajen wannan zamanin"

" Oh ni Juwarah yarinya ta fitsare bari nayi na gama faɗa maki na kashe wayata, ina nan ina tausayin ki ashe ke kin gama zama yar hannu ma abin ki,"

Dariya suka yi tayi kafin Juwairah ta ce;

"kanin fari Zaki sa a siyo maki kadan zaki saka ba mai yawa ba, saboda masu magungunan gargajiya da na asibiti na ji sun tabbatar da cewa shan shi da yawa na kawo ciwon hanta, dan haka ki saka kaɗan sai citta mai dan yawa,da minannas, sai ki matse ruwan rake mai yawa, ba a qara wani ruwan da wannan ruwan raken Zaki yi amfani, Zaki samu rake ne iya adadin yawan da ki ke so yawan tsimin ki ya kasance, sai ki samo zuma mai kyau sosai ki saka sai ki dake kayan qamshin nan ki saka a ciki, sai kin ga ya yi kauri kadan ma'ana bai yi irin ruwa tsululu ba, zumar ce zata saka ya yi kaurin, ki dinga sha da yamma,amma pls wajen nemo zumar ku tabbatar me kyau ce kin san yanzu an b'ata zuma sugar wasu ke saka wa,idan taso na baiwa su Adda saudat wannan nakin nima na dan sha kafin na koma nawa gidan"

"Na gode matar yaya sai an jima ki shafan min kan bbyna, ina gaida yaya"

" Ni ma ina gaida angon ki" .

Washe gari sallama ta yiwa Innarmu ta tafi gidan su ba zata dawo ba sai an gama tarewar yayun ta, ta kaiwa Yayun nata wannan tsumin, sannan tun da suka faɗa mata mazan su sun ce ai nan da kwana biyar za su tare, Juwairiyyah ta shiga hidimar taya su gyaran jikin su,sai ga su  Saudat sun fito fess da su fata na sheqi da kyalli , itama kanta uwar gyaran jiki sai da ta gyara dan a cewar ta itan ma amarya ce, tin da ta je gidan take ma su kwad'on zogalen daya sha timatir da cucumber,haka take wa zogalen tafasa ɗaya ta kwashe shi da ruwa-ruwa a babban mazubi,ta yanka manyan timatir masu yawan gaske sannan ta zuba masu qulin da ya ji kayan qamshi.

(Wannan haɗin ba k'aramin ƙara ni'ima yake yi ba sosai)

Duk daren duniya kuwa ta na samun kabewa ta yi ta haɗa masu da madara da zuma suna sha,( wannan haɗin yana gyara skin da qarin ni'ima)

Suna cikin lokaci na mangwaro ne, dan haka Juwairiyyah sai ta sa a siyo masu mangwaro mai yawa su zauna suna sha suna zuba hira abun su gwanin ban sha'awa.

Idan aka zo maganar tsarki da had'in ta na musamma da bata gajiya da haɗawa sai Salma ta yi ta jin kunya kar a gan su ace su na rawar kai,haka za su haɗu a d'akin su su yi ta mata faɗa musamman tunda ita ta haihu ta fi saudat bukatar wannan gyaran.

Goggo Sarai gaba ɗaya jikin ta ya yi sanyi qalou da lamuran gidan ganin yanda Mama Balki da 'yarta ke k'ok'arin ganin nata yaran sun je gidan Mazajen su da martaba da k'ima, tabbas Allah shine mai azurtawa ba mutum ba, duba da cewar gashi dai duk bala'in son kuɗin ta ta kai yaran Abujar kuma sun wahala babbar 'yarta ma har da nakasa, finally gashi yanzu Allah ya basu inda za su huta ɗin cikin sauqi ba tare da sun wahala ba sannan mazan nasu ' YAN ABUJAn ne dai ba wani garin na daban ba, hawayen da take qoqarin mayar wa ne wani ya gangaro,Mama Balki ta kalle ta ta ce,

" Yaya ki daina kuka, in yaran nan suka gani zaki d'aga masu hankali"

" Hmmm Bilki dole abun ya dame ni, ban zamo uwa ta gari ba sam sam a gare su, na tsani rayuwa da turbar dana ɗora yarana akai a baya"

"Hakane Yaya kinyi kuskure babba a baya, amma yanzu ai ya wuce ya zama tarihi,kuma in shaa Allah hutun da kike nema masu a rayuwa zasu same shi, kai sun ma same shi da iKon Allah"

Cikin gyad'a kai da yarda da maganar ta ta ɗauki kwanon abinci ta isa d'akin su ta miqa masu ta fice..........
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 34:

Labarin kyautar Abrar zuwa ga Suwaibah da mijin ta babu inda bai shiga ba a dangin nasu baki ɗaya har ma da mutanen unguwa, inda kowa yake farin ciki da irin wannan kyautar da Juwairiyyah ta yi wanda ba kowa ke iya yin irin ta ba, banda sanya albarka da fatan alkhairi ba ka jin komai a wajen mutane, sai kuma addu'ar Allah ya ba wa su Suwaibah iKon kula da tarbiyyar yarinyar.

Ya ku masu yi wa wanda Allah bai ba wa haihuwa ba gori ku ji tsoron Allah ku bari dan kuwa shi ke bayarwa ba mutum ne zai ba wa kan shi ba, da mutum ne yake ba wa kan shi da wata ba zata haifi yaro mai kalar baqi ba fari zata ba wa kan ta, da mutum ke ba wa kan shi da wata ba zata haifi fari ba baqi za ta baiwa kan ta, kun ga kenan Allah shi ne yake bawa wanda ya so ya hana wanda ya so ba dan baya son shi ba.

A yanzu wai mutane idan baka haihu ba ka zama mutum mara daraja a idanun su har kalmar juya za su dinga Kiran ka da shi, wannan matsala tafi fitowa daga dangin miji, musamman idan aka yi rashin sa'a basu da ilimin addini da wayewar ilimin zamani, jahilci ya musu yawa to daga ranar ka shiga uku in baka haihu ba, ba sa tinanin cewar ma ko laifin daga ɗan su ne? Ko kuma jinkiri daga Allah ne, ko wata rashin lafiyar da za a nemi maganin da ya dace da an samu haihuwar,su na mantawa komai himmar ma'aurata ba za su samu haihuwa ba sai da izinin Allah,mata masu gorin haihuwa mu sani kowacce mace dangin miji ce, ki kyautata kema sai a kyautata maki.

Da yawan gorin ma idan ki na da yaran wata bata da su ne zai hana ki zama kamar Juwairah? Ba zaki iya ba ko? To kar ki sake shiga hurumin Allah,idan kuma ba haka ba ki sa a ran ki ba da wadda bata haihun ba ki ke yi da Ubangijin ku da ya baki ita kuma bai bata ba da shi ki ke yi, sai ki jira amsawar shi domin kin tab'o shi.

Satin su Juwairiyyah uku da komawa Abuja har ta fara sabawa da rashin Abrar a tare da ita,ta bi duk wani process na yaye dan ta samu jikin ta ya zauna da kyan shi,ta yi had'in Sabaya wanda ta qara masa da dankalin hausan da ta busar aka niqa mata da sauran kayan had'in, sannan idan ta tashi sha ta na zuba madara sosai ta shanu,da yamma kuma ta markad'e ayaba da gyad'a ta zuba madara ta shanye,gefe ga man kaɗanyar ta da ta kwaba shi da man hulba da na Habbatussauda ta na shafawa a qirjin nata,cikin qanqanin lokaci ta yi wani irin kyau ta yi fresh ga cikakkiyar ni'ima da had'in ya qara mata,Jabeer ba ya gajiya da hidimta mata da ya ji ta ce Yah Jabeer siyo min kaza a guje yake siyowa dan ya san karshe shi zai amfana da hakan.

( Dan Allah maza ku sauya hali ku gyara matan ku na gida sai ku jima kuna morar su,ko da za ku ƙara aure ba zaku wulakanta na gida ba saboda duk abinda wadda Zaku kawo gidan Itama ta gida ta na da shi,duk abinda zaku yi wa matan na kyautata wa wallahi ba ku faɗi ba riba ce a wajen ku duniya da lahira, kai kuma saurayi da ka ke shirin yin aure ka dai ji yanda Jabeerun Innarmu ke kula da matar shi,ke kuwa uwar gida ko amarya kin ga yanda Juwairiyyah ke qoqarin gyaran jiki, tsafta, shagwab'a,iya girki,kula da miji a azaroom da duk wani abu da ya dace, dan Allah kowa ya gyara saboda rayuwar aure ta yi kyau ta yi qarko)
Chapter 57 · 0% Book details