← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 61

Sashe 54

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duba Yaran suka yi suka ga kyawawan yara, sannan suka dawo da kallon su suka ce,

"Masha Allah ga yara kuwa kyawawa qannen ku ne?"

Murmushi Salma da Saudat suka yi a tare sannan Salma ta ci gaba da magana dan bata son abinda zai karya masu zuciya gaba ɗayan su, tunda har suka kasa haƙuri su samu wajen da ya fi wannan natsuwa su bayyana soyayyar su to fa ba za su bari abu ya yi nisa ba suma,gwanda a yi maganar gaskiya da gaskiya ,Salma ta kula dikkan su samari ne basu taɓa yin aure ba ma,cikin nuna masu gaskiyar da ke zuciyar ta ta ce,

" Waɗancan 'yan biyun nawa ne ni na haife su ba qannen mu bane, sai dai ni aure na ya mutu, ita kuma wannan yayar tawa mijin ta Allah ya yi masa rasuwa ne har ma ta fita a takaba,"

Cike da mamaki da tausaya wa a gare su suke kallon su,amma dai duk yanda aka yi mijin daya saki Salma na da tab'in hankali ko kuma shafar aljanu, hauka ne kawai zai sa kana da mace kamar wannan ka sake ta, nan take suka yi wa Saudat ta'aziyya sannan farouq yace,

" A gaskiya ni har yanzu ina ciki kai fa ɗan uwa? Dan ba zan taba barin wannan tsaleliyar ta wuce ni ba na yi asara, domin da dikkan alamu akwai tarbiyya awajen ku"

A sannan ne Saudat ta yi magana ta ce,

" Yanzu dai yanda za a yi ku yi hakuri zuwa har a gama biki da komai da komai sai kuje can gida ku samu mahaifin mu ku gabatar da kan ku,duk abinda mahaifin mu ya ce maku shikenan da shi za mu yi amfani dikan mu"

Godiya suka yi sosai kuma suka qara tabbatar da tarbiyyar su, karbar No wayar su suka yi tare da yi masu sallama suka tafi.

Adda Suwaiba ce ta dawo kusa da su ta zauna ita da Juwairah, suna zama Salma ta labarta masu duk abinda ya faru, suna cikin addu'ar neman zabin Allah Hussainar Salma ta hau kuka, kuka take sosai har Salma ta rude kamar za ta yi kukan itama,miqo masu hannu suka ga anyi ta sama;

"Hey baby how are you?"

Ibrahim ne ya karɓe ta ya na kallon kyan yarinyar ta yi kama sak da maman ta,jijjiga ta ya yi ya tafi wajen yayan shi suna ta hira da sauran abokai ko damuwa da yanda take zuba masa yawu a jiki bai yi ba,haka abokan ango suka dinga ɗaukan ta, daga wannan ya karbe ta sai wannan ya karbe ta, daga qarshe Ibrahim ya karɓe ta ya sanya ta a kafad'ar shi har ta yi bacci,cike da yabawa abinda ya yi Salma da yan uwan ta ke kallon shi.

An gama dinner za a tafi gida ne ya iso ya miqa wa Salma ita, godiya ta yi ta masa har sai da yace,

"Ya kike man godiya ne haka? A gani na dan uba ya kula da yar shi ai ba wani abu bane ba ko?"

Murmushin jin daɗi ta yi idon ta cike da kwalla ta gyad'a kai ta yi gaba, bayan sun fita ne suka fuskanci basu da abin hawa ga dare ya yi dama a adaidaita sahu suka zo, su Farouq ne suka zo a motocin su suka parker a gaban su salma,sun so matuqa Juwairiyyah ta bi su su sauke ta a gida amma ta qi ta ce Yah Jabeer na nan tafe ɗaukar ta.

Tafiyar su da wasu 'yan mintinan da ba za su wuce biyar ba kuwa ya iso ya ɗauke ta, a hanyar su ta komawa gida ne take sanar da shi labari mai daɗi game da samarin da suka nuna suna son su Salma.

Murmushi ya yi tare da fatan alkairi ya ce,

"Allah dai ya kaimu gida lafiya baki ji yanda na gaji ba sai kace ni ne angon wanka nake so na yi da ruwa mai dumi ko na warware"

Murmushin Itama ta mayar masa sannan tace,

"Hmmm Abu Abrar kenan na gane in da ka dosa, to yau kam dole a min hakuri dan kuwa ni kaina a mugun gajiye nake"

Dariya Jabeer ya yi yace,

"To za mu gani dai Allah ya kaimu gidan lafiya, ni da na san halin ki ai sai dai na ba wa wani labari ki 'yar mama"

Jabeer ya kashe mata ido ɗaya ya ci gaba da murmushi ya na tuqin shi, kauda kai ta yi tana murmushin itama a ran ta ta na fatan Allah ya kai su gida lafiya dan kuwa ita ɗin ma ta yi kewar shi.......
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 33:

Washe gari angwaye zasu zo dan tafiya da amaren su da kan su tsabar zumud'i, dan kuwa ji suke yi kamar sun auri sabbin 'yan mata duba da yanayin kyan jiki da su Salma ke da shi babu mai cewa sun taɓa yin aure idan ba an sanar da mutum ba, su Goggo Karima ana nan sune yan rakiya zuwa Abuja.

Da wuri suka shirya dan su shiga kasuwa Juwairiyyah ce ta dage sai sun je sun yi siyayyar lefen su saudat ɗin da mazan su suka damqa masu kud'ad'en a hannun su anan garin kano,sannan su sai wasu abubuwan amfanin gida dan kuwa a ɗan zaman da ta yi a Abuja har yanzu bata gano inda ake Saida wasu abubuwan da take buqata ba,akwatuna masu kyau da sha'awa suka siya suka cika da kayayyaki masu kyau da tsada, Suwaibah ce ta haɗa su da manyan shagunan 'yan kasuwan da ke haɗa wa mutum lefe idan ya na da buqata a farashi mai sauqi saboda yanzu sana'ar da take yi kenan kuma ta na samun riba sosai.

Cikin abinda bai fi awanni huɗu ba suka kammala da bangaren lefe suka shiga kasuwar kurmi suka sayi kayan qamshi na girki sannan aka yi masu haɗi na musamman da za su niqa su dinga sanya wa a cikin madara da zuma su na sha dan qarin ni'ima da d'umin jiki.

Juwairah bata manta da Yah Jabeer ɗin ta ba dan kuwa ta lodar wa mijin ta kayayyaki dangin qanan kaya irin su vest, boxers, turaruka, takalma, da huluna guda biyu masu kyau sosai, mamaki ne ya kama yayun nata sai suka kasa jurewa sai da Saudat tace mata,

"Ke kuma ya naga kina ta siyan kayan maza baki saiwa kanki komai ba sai tirare da kayan bacci,"

" Adda Saudat Yah Jabeer na d'ebarwa ai, ba dan komai ba sai dan yanda shima yake kyautata min yake min dukkan wata hidima da ta taso min da jikin shi da aljihun shi, na sani komai zan masa ba zan yi kamar yanda yake yi min ba, sannan wannan abun da na siya already yana da su, amma kyautata wa juna na qara danqon soyayya, kyauta tsakanin miji da mata musamman irin wannan ta tiraren da miji ya fi so, tana da matuqar tasiri a zuciyar namiji, shiyasa naga ya dace tinda ya wadata ni da kuɗi shima na sai mashi"

"Lallai Juwairere ke kin ma fi Mama Bilki iya tattalin miji, na rasa waya koya maki duk wadannan dabarun da ki ke da su, ko kayan baccin ki da tiraren ki da ki ka siya duk shi za su amfana ai"

Dariya sukayi, Juwairiyyah ta ce,

" Salma ai gaba kin ga in ya tashi bani zai bani wanda yafi wannan tinda yasan ko me zan siya duk inda aka je aka dawo zai amfana shima ta kowanne fanni"

Tafiya suke suna jinjina wayo irin na qanwar tasu,cikin jin daɗin had'in kan da ta samu da yayun nata ta ce masu,

"Adda Saudat ku daina mamaki na, kowacce mace tana da kaifin hankali da basirar zaman gidan miji, bambancin mu shine wata tana shiga kwakwalwa da zuciyar ta ta yi tinani ta sama wa kan ta mafita a kan duk wata matsala da ta tunkare ta ta na tsayawa ta yi abinda zata amafana da baiwar ta wasu ma su amfana, wata kuma dunkufe kanta take yi bata son yin dogon tinani sam, bama ta son tana zurfafa tinanin ta akan komai, da matsala ta same ta sai tace sai ta nemi shawarar qawa, wani lokacin a yi sa'a ta samu shawar qwarai wani lokacin kuma ayi rashin sa'a ta samu muguwar qawa ta bata gurguwar shawara, amma in da zamuna bude zuqatan mu da maza sun ji daɗin zama damu, aure kuma daya rage mutuwa, da hakuri da sanin ya kamata ya wanzu a gidan auren mu, Adda muna a garin da ba mu da iyaye acan mu ne iyayen junan mu mu zamu taimaki kan mu, dole sai mun zama masu irin wannan tinanin gudun shiga matsala kan dayan mu ya kai mana agaji"

Wani kallon so da qaunar qanwar tasu ke yawo a idanu zuwa zuqatan su, a haka suka samu abin hawa bayan an masu niqan kayan qamshin suka wuce gida a gajiye da kaya masu mugun yawa, alwala suka yi sukai sallah azahar da la'asar da basu samu damar yi ba suka bar Goggonayen su da su Mama Balki suna kallon kayan lefen daga qarshe ma maqota aka aikawa duk suka shigo suka ga kayan alkhairi,su kuwa ganin ana ta cika ne ya sa suka yi wanka suka ci abinci, sai baccin gajiya ya ɗauke su.
Chapter 54 · 0% Book details