← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 61

Sashe 33

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan uban ki to da haka ki ce ita ce ta haife ki ma mana? Ku tashi ku fice man a d'aki gaba ɗayan ku bana buqatar kowa, yaran da suka san daraja ta da qimata za su zo su kula dani, dama ke tinda aka yi auren ki me ki ka tsinana min? A wajen neman mijin me yasa baki tsaya kin nemi kamar na yan uwan naki ba ? Banda wahala me ki ka samo wa kan ki? Sai ku tattara ku je can ku qarata,jikoki kuma ko awajen yarannan biyu ba zan rasa su ba, dan ba zaman banza na aika su yi ba a gidan Mazan nasu"

Ganin cewar ita fa Goggo Sarai bama ta yi nadama ba sai suka miqe za su fita daga d'akin, Mama na yi mata addu'ar shiriya a ranta, dakin ta ta kai Salma sannan ta fita tsakar gida ta dakkowa Salman abinci ta bata, kamar mayya haka ta hau shi da ci kuwa tana hawaye, tana gama ci ta sha ruwa nan take kuwa bacci mai daɗi ya kawo mata ziyara.

Mama Bilki ce ta gyara mata kwanciya tana tsananin tausayin ta, Abba sai godiya yake mata da sanya albarka.

*****************************

Bangaren su suwaiba 'yan Abuja kuwa suna can Abuja su na cin duniyar su da tsinke hanakali kwance, su kuwa su Alhaji Kalla na can na shirya wani babban lamari akan su ba tare da sun sani ba.........[21/07, 7:46 pm] asiyahabibu93: 💅🏼   ' YAN ABUJA.  💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

*SANARWA*

*Makaranta ku yi min afuwa shekaran jiya na tura page 20 amma suka maqale basu tafi ba shi yasa kuka ji shiru na san na tura na zaci matsalar network ne za su iso daga baya,shiru basu zo ba kuma wayata kwana biyu ta na bani ciwon kai shi yasa,amma a yi hakuri za a ci gaba daga inda aka tsaya...masu nema daga farko ku yi haƙuri a gama editing a mayar document..kar ku manta wannan ba sabon rubutu bane tsoho ne na yi shi tun 2017 editing nake yi za a gama da wuri da yardar Allah...na gode*

Page 22:

Zaune suke gaba ɗaya 'yammatan Markan a d'akin ta ta sa su a gaba ta zabga uban tagumi hankalin ta a matuqar tashe,Huwaila na kwance da gwangwanin madara da suke yin alalen gwangwani ta zuba masa qasa sai zuba yawu take yi a ciki, wani wawan tsaki Marka ta zabga ta kauda kan ta ta na kallon Jummala da ke yatsuna fuska,kan ta kai ga tambayar bahasin yatsinar suka ga Jummala ta fita da gudu tsakar gida ta na kelaya amai, kukan da Marka ke ta riqewa ne ya kufce mata, Jummala ce ta dawo riqe da cikin ta ta zube a qasan simintin d'akin daidai inda ledar d'akin ta yage ta na bin sanyin wajen,a haukace Marka ta yi kan su da duka ta na fad'in

"Ina zaune da qananan 'yan iska ashe ni Marka ban sani ba,da uban wa ku ke lalata har dika ku biyu ace wai ciki ne da ku, yau in mahaifin ku ya ji wannan mugun labarin ni Marka ya zanyi da raina, wannan abun kunyar ina zan kai shi a garin nan?"

Kuka take tana share kwalla, shirun da suka yi mata ne ya qara b'ata mata rai matuqa, watakan sun ma mai da ta yar iska kenan ko,dukan ne da alama bai shiga jikin su ba, a haukace ta fita madafin su ta dakko zankad'ed'en maburgin  miyar ta ta yi d'akin ta rufe qofa ta rufe su da mahaukacin duka, ita dai Huwaila ba k'warin guduwa sai baki, nan take ta ko fara magana cikin kuka ta ce,

" Allah marka ki kyale mu ai iskanci ba kan mu farau ba, kuma naga iyayen yaran na gida ne ba bare ba su bangis ne fa, Baban su na gidannan shima yana zuwa lalubar ki duk daren duniya baku ko gajiya ko d'aga wa juna qafa ko ji kike bamu sani ba? Na san komai duk mun san ki na da hannu a qullawa Salame sharri ke da Baban Bangis dan asirin ku ya rufu  ku ci gaba da watsewa idan Baba baya gari,dan haka mu ki daina dukan mu kema ai duk ɗaya muke da ke gwanda ma mu bamu da aure, kuma shikenan dan naki bai fito ba namu ya fito ba za ki kashe mu a banza ba, kika qara dukan mu sai na faɗa ma Baban mu in ya dawo kuna kub'ewa keda yayan shi"

Da sauri Marka ta sa labccen hannun ta ta damqewa Huwaila da ke tona masu asiri baki,ta na ta zaro ido da waige waige tare da fatan Allah ya sa ba wanda ya ji wannan mummunan sirrin da suke b'oyewa, ashe dama yaran kallon su kawai suke yi sun san komai?

Ji suka yi an banko qofar da mugun qarfi, wani tsoro ne ya kama ta ba ta san sanda wata muguwar tusa ta kwace mata ba, zama ta yi kusa da yaran ta na jiran taga wanda ya ke son shigowa d'akin kamar aradu,yaran kuwa sai toshe hanci suke tsabar azabar warin tusar da ta sakar musu.

Talle ne ya bayyana a gaban su idon shi ya kada ya yi jawur akan wanda yake da shi, idan aka ce Talle zai iya kisa a wannan yanayin ba mai yin musu,nan take ya damqo wuyan Marka ya mata mummunar shaqa, ya ja ta suka fita har tsakar gida yaran su na biye da su cike da tsoro, qananan sai kuka suke yi,'Yan matasan kamar su Haule kuwa sai bin su suke suna mamakin abinda ke faruwa yau a gidan nasu , har qofar sashen yayan nashi ya je ya wurga Marka a jikin shi,shi kuma a daidai wannan lokacin ya fito da tabarma a hannun shi na dama  ɗaya hannun nashi na hagu riqe da buta za shi zaman qofar gida na safe da suke yi, janye jikin shi ya yi yana wani ja baya tare da fad'in ,

" Subhanallah,meye haka zaka rab'an matar ka a jikina, bayan kasan ba muharrama ta bace ba"

Wani gigitaccen mari Talle ya bankawa yayan nashi, buɗe baki ya yi zai yi magana Talle ya qara make shi Saida ya tintsira ya faɗi qasa tabarmar hannun shi da buta tini sun yi nasu waje,shiru ya yi ya damqe bakin sa saboda tsoron kada wata kalma ta fito a sake banka masa mari ya tabbata asirin su ne ya tonu dan shine kaɗai zai bawa Talle yi masa wannan rashin mutuncin,nan ya samu waje ya yi zaman 'yan bori a wajen ya hau kuka, Marka kuka Yaya kuka saboda nadama da kunyar abinda suka dinga aikatawa, wani haushi ne ya kama Talle kukan uban me suke yi kuma yanzu, kuka ai shi ya kama, miqewa ya yi a haukace ya bisu da duka, duk wanda ya samu ya maka har yayan nashi,wata iriyar tsanar su ke huda zuciyar shi, sai da ya yi masu lilis sannan ya fice ya bar gidan,jiki duk tsami baki kamar an liqa masu super glue haka suka kad'e jiki kowa ya yi d'aki dan kuwa yanda Talle ya jibge su ba tare da ya tona asirin abinda suka aikata masa ba suma haka za su yi gum da bakin su, to in ba su yi shiru baaa me za su ce wa yaran da ke ta koke koke saboda ganin yanda Talle ke jibgar su? Hannun Yayan Talle ne ya kumbura ta wajen tsintsiyar hannun haka ya karasa shigewa d'akin shi ya na numfarfashin wahala dan ya san tabbas sai ya ga mai dori a ja masa hannun.

******************************

Allurar bacci Alhaji Salihu ya yi wa Suwaiba da ya dawo ya tarar ta fara bacci,sai kawai ya tsaya akan ta yana qarewa qirjin ta kallo,duk kyan wajen nan yanzu haka za a je a yanke su ba ko d'igon imani? Alfarma ɗaya Oga zakas ya yarda zai yi masa, alfarmar kuwa itace tinda yana son matar shi to a yanke mata irin yankan da bazata mutu ba wajen yin shi, in an gama gudanar da tsafin za a yi mata operation yanda daga baya zata ji sauqi a hankali su ci gaba da rayuwar su, hawayen tausayin ta ne ya zubo masa, wanda hakan sabon abu ne a wajen Alhaji Salihu,bai taɓa zuwa gabatar da wani aiki ya ji tausayin da ya sanya shi zubar hawaye ba,hawa gadon ya yi ya rungumo ta ya ɗora kan shi a qirjin ta,hawaye ya dinga zubarwa tare da ɗora hannun shi a Saman qirjin ta cike da jimanta lamarin, ya jima a haka ya na zaune da kyar ya hakura ya dauke ta ya yi mota da ita,dajin da suke gudanar da tsafin su ya nufa ma'ana gidan Oga Zaks.

Hankalin Alhj Kalla a tashe yake ganin rashin dawowar Saudat,ta ina ma zai fara tunkarar shugaban qungiya ya ce matar shi bata dawo ba bayan ya san an yi masu duk wata alfarma da za a iya yi masu?

Ta ina zai fara samo wadda za su yi aikin akan ta a wannan qurarren lokacin? Anya ma zai iya kyale Saudat haka kuwa ba tare da ya lahanta rayuwar ta ba? Yanzu idan yace zai yi mata wani abu kuma asirin su ne zai tonu akan na da,dan tabbas tunda Saudat ta qi dawowa zargin shi ya tabbata ta san komai game da su kuma ba za ta kasa sanar da dangin ta ba.

Ya na nan ya lula duniyar tunani da damuwa tare da neman yanda zai ya shawo kan matsalar da yake ciki  Alhj Salihu ya yi masa waya yace shifa ya ɗauki hanyar zuwa wajen Oga zaks amma ya ji shiru bai ji daga gare shi ba,

"Ka na nufin Suwaiba ta dawo ita?"

"Kwarai da gaske,me yasa ka tambaye ni bayan a gaban ka muka yi waya da ita ta ce min suna hanyar dawowa? Ko dai Saudat bata dawo bane?"

"Ina fa ta dawo aboki na, ka je gani nan nima ina nan tafe yanzu nan"
Chapter 33 · 0% Book details