← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 61

Sashe 41

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk abinda take yi akan idanun Alhaji Salihu take aikata su, cikin rashin k'warin jiki ta koma ta kwanta a Saman gadon nata tare da nitsar da kan ta cikin pillow kuka take yi sosai mai taɓa zuciya, zama ya yi a gefen ta ya kama hannun ta ya na lallashin ta, a hankali ta d'aga kan ta ta na kallon shi,da kyar ta buɗe baki ta ce masa,

" Sweet wai me ya same ni ne, wanne mummunar qaddarar ce ta hau kirji na ni suwaiba ?"

" Shiiiiiiii kar ki na yin magana sosai, hatsari muka samu a gidan, yan fashi  ne suka suka shigo a ranar da ki ka dawo kina bacci suka yanke maki nono, ni kuma dana dawo na ganki kin suma shine na kai ki asibiti aka maki aiki daga nan na dawo da ke gida nake ta kula da ke"

A firgice ta miqe daga kwanciyar da take ta ce,

" Dama abinda ya faru kenan? Yanzu tsabar rashin imani su rasa me za su cire min sai wannan waje mai daraja?"

Ta fada tare da zaro idanun ta da ke ta zubar da zazzafan hawaye, cikin kukan nata ta ce,

"Na shiga uku ni Suwaiba,ya zan rayu ba mahaifa ba nono,yanzu nan gaba me zan rasa kuma, Alhj na fa san kai ne sanadin rasa nono na  ba wani 'yan fashi,Saudat ta fad'an min ban ji ba ban yarda ba, saboda ina son ka, ko da ina son kudin ka na yarda cewa a yanzu ina son ka so na gaskiya,zan iya rayuwa da kai ko ba mahaifa shine hakan  be ishe ka ba sai da ka qara da wata kadarar tawa yanzu ta ya zan rayu ba nono ba mahaifa"

Rushewa ta yi da wani irin kuka mai ban tausayi, cikin tausaya mata Alhj ya fara magana"

"ki yi hakuri Baby yau zan........"

katse shi ta yi cike da bala'i ta ce,

" Kar ka sake kira na da wata baby again, i hate u Alhaji, na tsane ka, na tsane ka da dikkan rayuwa ta"

Kukan ta ci gaba da yi mai ratsa zuciyar mai tausayi kai har da mara tausayin ma,matsawa ya yi ya kamo ta jikin shi, da sauri ta zame ta ci gaba da cewa,

" Kar ka taɓa ni azzalumi kawai,ka kuskura ka sake taɓa ni ni ma sai na yanke maka inda ba zaka taɓa amfanuwa ba a jikin ka"

Cike da matsanancin fushin da bai taɓa sanin suwaiban da yake wa kallon doluwa na da shi ba ta yi maganar,nan take wani irin shakkar ta ta shige shi, miqewa ta yi cike da jiri zata fita, cikin sassanyar murya Alhaji ya ce mata,

"Ina zaki je kuma"

"Gidan mu zani, na gama auren ka, na kuma gama aure a ABUJA har abada daga yau,daga rana mai kamar ta yau bani ba Abuja"

" Lallai ma Suwaiba, abinda baki sani ba shine, ba inda zaki qara fita ko nan da can ne kuwa sai da sani na, dan kuwa ni a yanzu ba zan iya rayuwa ba ke ba, kin ga kuwa sai ki shirya zama da masoyin ki na gaskiya, na amince ni zan jure rashin albarkatun qirjin naki tunda ni ne sanadi"

"Za kuwa ka mutu dan ba abinda zai hana ni barin gidannan, ko kana so ko baka so sai na bar gidan nan, in ka barni na tafi lafiya ba hukumar da zan haɗaka da ita, amma in ka hanani ba abinda zai hana ni haɗaka da hukuma zaɓi ya rage ya naka"

Wani shu'umin murmushin rainin hankali ya mata ya ce,

"To ai baki san wani abu ba, qungiyata babbar qungiya ce suwaiban,ni ɗin ba wai qaramin mutum bane ko baki gani bane?manyan gwamnati da yan kasuwa ba wanda babu a cikin qungiyar mu, ba yanda za ai ki had'a ni da hukuma kuma a samu hukunta ni din, mata kalar  ki da wanda suka fiki komai sun fi dubi kuma mun masu wannan aikin balle ke, dan haka hakuri zaki yi kawai mu qarasa rayuwa dake a haka, in kin tafi wa zai na baki abun daɗin da nake baki? wa zaina debe maki kewa? wa zai zauna dake babu nono? Hakura zaki yi kawai mu zauna a haka tun da kuɗi ki ke so ni kuma zan ci gaba da jiyar dake daɗi da dukiya ta"

Tallabo wuyan ta ya yi ya na kallon fuskar ta,iya kuwa gaba ɗaya ta qame ta dauke kan ta daga ganin shi hawaye kawai ke zuba mata, ga wani irin tsoron shi da ke kwance a qasan zuciyar ta, yau ya zata yi ta kub'uta daga hannun wannan azzalumin?

Kuka ne ya kwace mata sosai, key din motar shi ya ɗauka ya fice ya bar mata gidan, anan inda take tsaye ta durqushe tana kuka mai ban tausayi.
*****************************

Talle kam ya saka marka a tsaka mai wuya ita da yayan shi, dan baya son maganar ta fita waje shi yasa bai ce masu qala ba,sai kawai ya fito da wata mugunta, gonar shi ta daji mai shegen nisa ya ke sa su zuwa gyaran ta, duba da cewar damuna ta kusan zuwa, a cewar shi ya na da majiya qarfin zuciyar cim amana irin su ba abinda zai sanya shi biyan kud'in gyaran gona,in sun ga dama in sun shiga dajin ma su ci amanar shi ya yafe masu amma tabbas sai sun gyara masa gona kafin damina ta sauka.

kullum can suke tafiya ba abinci ba ruwa, amma shi zai je a machine din shi da abincin shi da ruwan shi ya yi shawagi ya sa ido ya ga ya aikin yake tafiya,su kuma su Baban gida gonar shi ta can wani qauyen dake kusa da su ya tura su, saboda ya yi yarjejeniya da su akan hakan, in ba haka ba ya kaisu birni ga hukuma a huhunta su akan yi wa 'ya'yan shi ciki da suka yi,da jin haka suka amince suka yi biyayya suma.

Kan kuce me Marka ta fita hayyacin ta, 'yan mazaunan nan da ake kad'awa ana jan hankali da su duk sun zube, duk ta dame qashi ya fito mata ko ta ina,mutanen gari kuwa sai gulmammaki suke yi akan abinda ke faruwa a gidan Talle, kowa da ruwayar shi akan abinda ke faruwa amma ba wanda ya san gaskiyar lamari.

Kowa ya rasa gane dalilin Talle na aikata haka, da damar mutane sai suka alaqanta hakan da tsantsar rashin mutuncin shi, su Huwaila kuwa kullum sai sun yi surfen abinda za ai tuwo da shi sun dake da hannun su sun mayar dashi gari, sannan su yi tuwon da za a ci a gidan, ga aikin qannen su da ya ɗora masu, walaka ta yi masu yawa kamar zata kashe su,ga qaramin ciki suna fama da shi.

Jummala ce ta fito daga d'akin su da rarrafe saboda azabar ciwon cikin da ya sako ta gaba sai  murqususu take yi, cikin tsawa Talle da ke zaune ya na sauraron rediyo ya na aswaki zaune Saman tabarma ya d'aga kai ya kalli Jummala ya ce,

"Ke meye hakan zaki zo kina ma mutane kuka, kin gama aikin da na saka ki ne?"

Cikin kuka da tashin hankalin da take ji a jikin ta ta buɗe baki zata yi magana sai maganar ta maqale ta kasa fita,wani abu ta ji ya taho da gudu zai fita ta qasan ta, jini ne ya tsinke mata, nan da nan ta faɗi a wajen tasuma tsabar azaba, a gigice Marka ta yi kan ta,shi kanshi uban gayyar ya tsorata da ganin jinin da ke zuba a jikin Jummalar,daukar ta ya yi a hannu ya ɗora ta a kan machin ɗin shi, marka ma ta hau ta riqe ta, asibitin qauyen suka kai ta, bayan bincike da gwaje gwaje likita ya tabbatar masu da b'ari ta yi, sakamakon ta sha wani magani na zubda ciki, ga kuma jini yaqi daina zuba a jikin ta, suna buqatar a sai mata jini a qara mata zasu yi iya qoqarin su su tsaida jinin, Talle ne ya kalli matar shi ya ce,

" Sai ki fito da kud'ad'en da kike ajewa na tarin auren su ai mata magani ko"

Ya qarasa maganar cikin haɗe fuska, kallon shi ta yi ta sunkuyar da kai da sauri, duk wanda ya hanta a wannan yanayin bai san halin ta ba zai ce zalintar ta mijin ta ke yi, a sanyaye ta ce,

"To bari na koma gida na d'akko"

Dan rashin mutuncin Talle ko duba halin da Jummala ke ciki bai yi ba haka ya na gani Marka ta taka a qafa ta d'ebi hanyan jiki duk ya mace mata ba wannan cikar da take yi da izzar nan.

Kafin ta isa gidan ne ma likitan ta fito, take sanar da Talle Jummala dai babu ita, sakamakon shan maganin zubda ciki da ta yi ba bisa qa'ida ba shi ne ya yi sanadin zub da jini mai tarin yawa a jikin ta, kuma sun kasa tsaida jinin har rayuwar ta ta qare, dafe kai Talle ya yi, nan take nadamar rayuwar shi ta baya ta baibaye shi, kuka yake kamar qaramin yaro, nan suka samu wani mai machine d'in ya taimaka masa ya nemo mai motar da zasu kai ta gida, mai machine d'in kuwa tasha yaje ya samo masa motar, Tallen ya biya shi kud'in ya masa godiya, a motar aka maida su gida shi da gawar Jummala, Marka na shirin fotowa ta koma asibiti taga an fito da gawar Jummala, zubewa ta yi a qasa ta hau kuka da bori tare da kururuwa.......
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 25:
Chapter 41 · 0% Book details