← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 61

Sashe 7

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kukan da take son yi ta mayar ta had'iye, bata qaunar yin abinda da zai b'ata ranshi ya fasa cimma burin shi,amma daga qarshe dai dole da kuka da roqo da aka tashi wasan, har cewa ta yi tama fasa son nashi, tinda haka ne abin baya tausayin ta, bayan komai ya dawo masu daidai ne ya mannata da qirjin shi yana mata addu'o'i da saka albarkan da ya faranta ranta matuqa, hakan da ya yi mata ya nuna mata mahimmancin kawo budurcin ta da ta yi lafiya gidan auren ta , da kuma  illar abinda da zai same ta da bata kawo ba din, kuka take ta yi qasa qasa, Jabeer sai ya tashi ya saka kayan shi ya fita ya haɗa mata ruwa mai dumi ya dawo ya ɗauke ta ya kai ta bayin su da ya kewaye masu su kaɗai ya sata cikin roba mai faɗi da ya zuba ruwan.

Godiya Juwairiyyah ta yi masa dan kuwa ta ji daɗin ruwan sosai bayan sun gama suka yi wankan tsarki suka fito suna koma wa d'akin sai ta hau abin sallah ta tada sallah dan kuwa lokacin qarfe 3:30am ya yi, sallolin nafilar ta ta yi bayan ta idar ta kwanta ta na tasbihi bacci mai daɗi ya ɗauke ta a wajen,sai shi ya daga ta bayan ya idar da tashi nafilar suka yi baccin su tare da addu'ar Allah ya basu ikon tashi su samu sallar asuba akan lokacin ta......

Ɓangare'YAN ABUJA matan manya kuwa bayan sun sauka a filin jirgi  sai suka tarar da motoci na jiran su, nan aka kwashe su sai babban hotel ɗin da za a yi dinner mai suna Chelsea hotel.................
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

*SANARWA ! SANARWA !*
*Ina masu buqatar sanin yanda za su gyara jikin su ta ciki da waje? Ina nufin daga gashin  kan su zuwa yatsun qafar su da qarin ni'imar jikin su?*
*Ina masu son koyon sana'o'i dan samun taro da sisi? To 'yar uwa matso kusa ba sai kin biya maqudan kuɗi ba dan ki koyi yanda Zaki yi sana'ar da zata sama maki kuɗi da #1k kacal za ki mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA*

*Idan kuma ke ma'abociyar karanta littafan Hausa ce ki yi wa HAERMEEBRAEH ❤️magana kai tsaye ta wannan No 09031416423 kai tsaye, Zaki samu Littafin MAHREEN DA KYAKKYAWAR FAHIMTA a kan farashi #500 each*

*Please share*❤️

Page 5:

Tinda suka je farfajiyar hotel ɗin bakunan su Suwaiba yaqi rufuwa, ganin irin manyan motocin da suke ta gani an parker sai kwadayin arziqi da samun dukiyar su ya ninka na da,basu taɓa ganin manyan motoci haka ba a zahiri sai a American movies, wasu ma basu taba ji ko ganin su ba duk Yawon su da kallace kallacen fina-finan nasu, ( abun ku da masu idon cin nera ga Yawon tsiya gidaje da bukukuwan masu kuɗi) hankalin su ya kai qololuwa wajen kwadayin son suga mahallin su ma'ana wajen da za a kai su ya zama shi ne gidan su.

Sun shiga wajen da ake gabatar da dinner tare da angwayen su da abokan angon da suka masu rakiya, inda suka qarasa wajen hight table din da za su zauna, iyakar ganin idanuwan su iya ganin jajayen hulina  da fararen kaya da sirkin ja a jikin farin kayan ne, daga matan har mazan shigar kenan, sune kad'ai suka saka baqin lace da ratsin fari a jiki, mazan su ma farar shadda da jan aiki a jiki da jar hula ne akan su.

Wani mutum babba suka gani a gefe mutane kowa ya shiga sai ya gaida shi, ya hakimce a wata qatuwar kujera, suma tashi suka yi suka kai masa gaisuwa sannan suka koma mazaunin su an fara gudanar da dinner lfy, inda daga baya aka umarci kowa yaje ya yi serving kan shi abin da zai ci a wajen, wajen maza daban wajen mata daban,a bangaren Mazan akwai wani irin nama na daban da aka zo dafawa aka masa dahuwar laushi sosai duk abin mutum ba zai gane na meye ba,  matan kuwa kaji ne da sauran tarkace abinci kala2 a wajen har da na qasashen waje, sun ci sun sha, daga baya akai ta rabawa mazan wani ruwa a wata kwalba mai duhun kala, jikin su har rawa yake dan murna, kowa ana bashi yake kafa kai tas zai shanye ya ajiye kwalbar ya na lasar baki.

Bayan an yanka cake ne da sauran bidi'o'i aka tashi daga wajen dinner din,daga nan angwayen suka kama matan su suka shigar mota sannan suka ba su wani ruwa a cups masu kyau da sirkin wani magani a ciki, suna sha take bacci ya dauke su, madadin su yi gidajen su na aure da matan sai naga sun ɗauki wata hanya kamar za a bar garin basu tsaya ba sai a dokar daji, wani katafaren gida ne suka isa mai gate guda uku manya, katangar gidan duk maitar mutum na ya gudu ba zai samu dama ba saboda tsayin su, suna isa wasu qattai ne naga sun fito murdaddu sun sha baqaqen kaya da neck tie red, daukar su Suwaiba suka yi a hannu suka shiga da su gidan, a wani qaton parlour suka aje su kan kujeru suka juya suka fita,angwaye kuwa na tsaye su na jiran fitowar Ogan nasu su ji wanne umarni kuma zai basu, ji suka yi wata qatuwar murya ta yi magana,

"A kai min ko wacce d'aki, a haɗa su a gado daya,"

Ko da na duba sai na ga wannan turmusheshen mutumin ne na wajen dinner ya fito ba riga daga shi sai gajeren wando, nan take tunanin inda aka samu telan da ya iya dinka masa wannan wargajejen wandon ya faɗo rai na, ba karamin qaton mutum bane shi ɗin ,gaba ɗaya ya haɗa komai na zama qato ga tsaho ga qiba, ga tumbi, da sanqo, ga gashin baki, gana hammata nan cunkus, ga idonnan jawur, kamar gauta, ba zan taba iya kwatanta girma da yanda yake ba abin sai wanda ya gani kawai, haka ya tako da fataken qafafun shi ya kalli mazajen sukuma sai suka duqa masa alamun gaisuwa, d'aga masu kai ya yi ya ce,

" kuje sai nan da sati biyu ku dawo,dan ban taba ganin mata masu kyau irin wannan ba," ya qarasa yana lashe baki, d'aga masa kai suka yi suka amsa da,

" Tah oga zaks,"

Suka furta a tare, fita suka yi kowa hankalin shi kwance dan sun san samun su zai rubanyu da yawa, Nicon hotel suka wuce su hole abun su, dan su dama sunyi auren ne dan gudun maganar mutane, amma ba dan sun damu da auren ba, tinda a cewar su mata na nan kamar jamfa a jos.

Shigar Oga Zaks dakin keda wuya ya isa gaban gadon, yana lashe baki, kashe wutar ya yi ya kunna bed side lamp, cire masu kaya ya yi ya dakko wani magani ya shaqa masu, maganin bacci ne, wanda zai kai su kwana bakwai cif suna bacci ba tashi, ina ganin zai zame rugegen gajeren wandonnan nai gaba da gudu, ba dani za ai kallon tashin hankali ba.

Oga Zaks ba shi ya fito daga dakin nan ba tin daren sai qarfe tara na safe hamma yake yana miqa ya wani bangare ya shiga wani daki, waya ya yi naji yana,

" ku shigo, "

Sannan ya aje wayar ya shiga wanka, wasu mata ne dattijai suka shigo, dakin da su Suwaiba suke nan suka shiga, suna gyara su suna tausaya masu, ɗaya daga cikin matan ne tace,

"Hmmmm wama ya sani ko garin shegen son abun duniyar su ne suka haɗu da su, ai kinga ban ga laifin mazan da suka kawo su ba kwadayi mabudin wahala"

Jikin ajiyar zuciya d'ayar ta furta,

"Haka ne kuma Allah dai ya kyauta"

Bayan sun gama shirya su ne suka tafi suka bar su suna ta shaqar bacci, a palour suka haɗu da Oga Zaks yana zaune, ya baza uban tumbi yana kwasar girki,cikin qatuwar muryar shi ya furta,

" Daga yau duk wata shegiyar tsohuwa a cikin ku da ta qara gulma akan matan da suke shigowa gidannan sai na mai da ita matata kuma ta inda baku tsammata ba tanan zan na amfani da ita, munafukan banza da wofi ku bace min da gani,"

Jiki na rawa baki na kyarma suka hau bashi hakuri, korar su ya yi ya barke da wata mahaukaciyar dariya.

**************************

Salma kuwa matar Alhaji me saida motoci,wani qaton gida ya kaita a wata unguwa a gwarinpa, gidan ya haɗu iyakar haɗuwa dan kuwa tun daga baƙin gate d'in gidan za ka san cewa nera ta zauna, bayan ya tsaida motar a bakin gate d'in ne ya fita da kan shi ya je ya bude gate sannan ya koma ya shigar da motar cikin harabar gidan,a tare suka fito daga motar sannan ya daga ya riqe ta a jikin shi, bayan sun shiga cikin gidan ne Salma ta hau zare ido dan ganin uwar  dukiyar dake gidan.

Wani d'aki ya kaita mai kyau, suna shiga ba tare da aikata komai da ya kamata amarya da ango sun gabatar ba a daren su na farko ya ja ta gare shi ya fara aika mata saqonnin shi da ya jima ya na jiran irin wannan ranar ya isar da su gare ta, dan kuwa shi dama bai wani more ta ba sosai, kuma babu laifi Salma bata yi irin wayewar su Suwaiba ba ko ya je soyayyar tasu bata wuce kiss da shafe shafe bata taɓa bashi dama ya kusance ta ba,haka angon Salma ya fara qoqarin cika burin shi a kan ta babu sallah ba salati ba godiya ga Allah na daren farko na ma'aurata ba adduar komai haka ya maida ita cikakkiyar mace,ai kuwa yasha kuka da zagi a wajen Salma, dan ashar sai wanda ta manta, bayan sun kammala komai ne ya yi ta rarrashin ta,a qasan zuciyar shi yana ayyana,

'Zakici uban ki ne wannan zagin da dukan da kk mun duk sai na rama na fanshe abuna, yar me kwadayin tsiya'
Chapter 7 · 0% Book details