← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 61

Sashe 19

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun isa asibiti suka tarar mutane sun zo an cika suma dole suka bi  layi kamar kowa,sanda likita ya kira ta sai aka bata gwajin jini sannan aka yi mata scanning dan ta matasa ta ce abu na motsi dole a duba mata, a  gwajin farko aka gano tana dauke da cikin wata hudu da sati biyu, zaro idanu take kamar mara gaskiy, ga wata iriyar da farin  ciki da suka kama ta, kunyar jabeer da tunanin ya iyayen ta da surukan ta za su ɗauki wannan labarin duk sun ishe ta ta rasa ya zata yi, janyo hijab din ta ta yi ta sunne kan ta a ciki tana dariya qasa qasa, Jabeer ta gani ya tashi ya yi sujjadar godewa Allah yana kwallar murna, itama a cikin ranta take maimaita

' Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin, hamdan katherran ya rahman,'

Murna take yi sosai ta ji hannun jabeer a jikin  ta ya  ja ta jikin shi, hada fuskar su ya yi waje daya suna shaqar nunfashi junan su,cikin murya mai ɗauke da amon farin ciki Jabeer ya ce,

" Juwaireren mama kin ga ikon Allah akan mu ko,Allah ya yi mana kyauta mai daɗi da sanya farin ciki ba zato babu tsammani"

D'aga masa kai kawai take tana murmushi, Dr. ne ya ce,

"To  Lovey-Dovey sai a tsaya a saurare ni kuma in an je gida an qarasa murnar a can, ina da wasu masu jira na a waje"

Shi kan shi likitan cikin fara'a da jin sun burge shi yake maganar, shawarwarin da zasu taimaka masu wajen kula da cikin da lafiyar ta ya basu, sannan ya rubuta magani inda yace su je su nuna takardar kawai za a basu kyauta ne,godiya suka yi masa mai tarin yawa sika fita, Jabeer ne ya sarqafe hannayen su waje ɗaya ya na jin son Juwairiyyah na qara shiga zuciyar shi, dan ji yake kamar ya dauke ta karta wahala da tafiya, kula da hakan da ya yi ne yasa ta tsaida su a wani wajen da ba mutane sosai tace,

" Babe Dan Allah zan iya roqon ka wata alfarma?"

Cikin zumud'i Jabeer ya ce,

" Anything for u my love,just say it, inshaa Allahu in baifi qarfina ba i will do it for u"

Murmushi ta yi ta sunkuyar da kai qasa sannan ta ce,

" Yah pls don't tell anyone that i am pregnant plssss"

Ta faɗa tare da qara damqe hannayen su waje ɗaya,

" But why, abun murna ne fa ya same mu da ahalin mu baki ɗaya? Don't u want them to be happy for us, and must importantly to pray for us, and our baby"

Ya qarasa maganar shi cikin rad'a,

" Eh Ina so mana sosai amma ka fahimce ni, kawai ni kunya nake ji,  yanzu fa kowa sai ya san me na yi na samu cikin nan har fa Babana"

Kiran Baban ta da ta yi sai ya sa ta sake jin wata kunya ta qara kamata kamar yama ji labarin ta na da cikin, dariya Jabeer yake yi sosai yana riqe ciki,cikin dariyar ya ce,

"Amma dai gaskiya baki da wayo na kula, to bari kiji tin kan a kawo ki aka san in an maki aure zamu yi abin da zaki samu cikin,me yasa ake hana 'yammata biye wa samari kafin aure? Ai saboda gudun kar su samu zunubi sannan kuma kar su samu ciki kafin aure su haifi dan shege, come on wuce ni mu tafi gida rana na dukar min ke"

Maqale kafad'a ta yi tana turo baki,

"Yanzu menene kuma?"

" Yah Yunwa nake ji sosaiii"

"Amma dai naga bamu jima da cin abinci ba muka fito ko?"

"Eh na sani, ni dai ina jin yunwaaa"

Yatsina fuska take kamar in bata ci ba wani abu zai same ta ne,

"Ok to yanzu me kk so?"

" Yah ga me agwaluma can ita nake so, kuma ina son waccan zogalen dafaffe"

"Ikon Allah, ashe kwadayin da kk ta min kwanaki babyn mu ne ke saka ki"

"Yah ni dai agwaluma kuma dan Allah Yah ka taho mun da gyad'a mai gishiri, ka had'o min da rake, yauwa ka siyo agwalumar mai yawa fa",

Gani ta yi ya saki baki ya na kallo ikon Allah, daga baya ya fashe da dariya,kawai sai ta saka masa  kukan shagwaba,da sauri ya yi maza ya kama bakin shi alamar yayi shiru, sannan ya ce,

" Yi hakuri ba zan sake ba kin ga a titi muke duk da katangar nan ta kare mu kinga masu agwalumar zasu iya maki dariya"

Narke fuska ta yi sannan ta ce,

" Oh ni Juwairah yau naa ga tsokana da ranar Allah dan Allah ka yi sauri"

"Auuuuu kin fi son a tsokane ki da dare dama? Ohhh to kar ki damu wannan ma ba a barmu a baya ba ai bari mu koma gida"

Da sauri ya yi wajen masu agwaluma yana dariya dan ganin yanda take banka masa harara ,zura hannun ta ta yi a riga tana shafa cikin ta dayake a lafe kamar ba komai sai ɗan tudu da ya yi ta qasan marar ta, amma a haka tana jin motsawar shi kadan kadan,

" Ikon Rahman Ar-raheem kenan,wato wai ni Juwairah ke dauke da ciki ban sani ba, Allah na gode maka, kasa duk abin da zan haifa ya zama musulmi mumini salihi, Allah ka sani na bi dukkan yanda Annabin ka ya tsara mana don samun 'ya'ya na gari, tin kafin aure na har yanzu da ka ban wannan arziqi, Allah ka sa su zama wadan da muslunci da musulmai zasu yi alfahari da amfanuwa da haihuwar su, Allah na gode maka ka ba wadan da basu da shi, ka sauqaqa min wajen haihuwa"

Hannun shi yasaka a gaban fuskar ta ya ce,

" Shin me Juwaireren mama take tunani haka? Gani na dawo ina tsaye baki ji ina maki magana ba, wato har zaki fara manta ni ko saboda kin samu baby"

Ya fada yana shagwabe baki kamar yanda take yi,

" Ba komai muje gida na yi na sha abunnan yunwa ta qaruwa take yi"

Dariya ya yi suka kama hanyar fita suka samu abin hawa sai gida, lokacin da yake fadawa innarmu Juwairiyyah na da cikin gudu ta saka ta yi bangaren su tana dariya, kowa murna yake a gidan kamar me, labari nan danan ya bazu a dangi Juwairah na dauke da cikin wata hudu da sati biyu, kowa na murna da saka albarka, jin wannan labarin da Goggo Sarai ta yi ya daga mata hankali, domin tunanin ta ya tafi akan dama yaran ta ne suka sama mata jika, ko dan samun wani kaso na dukiyoyin surukan nata,nan take tinanin Salma ya faɗo mata a rai, wayar ta ta d'akko ta yi ta zabga kira ana mata turanci, hankalin ta ya tashi sosai musamman da ba gane ne ake faɗa take yi ba,mayafi ta yafa ta leqa ta kira Baban su, ta bashi ya ji me ake faɗa, ce mata ya yi

"Wai an ce layin baya aiki yanzu,"

"Wai ni wa kake kira ne malam Salma fa na ce ka kira min"

"Ita dai ki ka kawo waya na kira kuma aka ce No  ta ta daina aiki,"

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una me yake faruwa ne? Malam wannan Yarinyar Salma so take ta kashe ni da tashin hankali da damuwa, ka na gani dai duk 'Yan uwan ta sun yi waya gida an ji daga wajen su amma ita shiru yau wata kusan bakwai, ga wannan mummunan labarin da ya iske ni na samun cikin wannan kodadiyar"

  "Mummunan labari kuma, a wajen wa kenan? A wajen ki dai amma ko? Hmmmm Sarauta kenan a gabana ki ke son ki ciwa 'yata fuska wai kodaddiyar 'ya na gode, Allah zai raba su lafiya, ita kuma Salma Allah ya sa ki same ta a wayar, in kun yi magana kin sanar da ni"

Ya na gama maganar shi  ya yi shigewar shi cikin gidan, wayar suwaiba ta kira ,tana dauka itama tambayar ta ta yi tace bata ji daga wajen Salma ba ko ta kira iya Goggon sun gaisa? Nan dai Goggo Sarai ke sanar da Suwaiba abinda ke faruwa.

Saudat ma da ta kira ta amsa ɗaya ta bata da ta suwaiba,daga qarshe dai suka haɗu suka kwantar mata da hankali akan cewa ta yu ma sun fita qasar waje ne da mijin ta honeymoon shiyasa ba a samu ta,wani farin ciki ne ya maye damuwar ta suka ci gaba da hirar su wadda rabi da kwatan ta ta yanda suke cikin rayuwar jin daɗi da hutu ne a Abujan ita kuma ta na sukar su Mama Balki da Juwaireren ta.

**************************

Salma kuwa wadda yaran Talle suka mayar mata da suna Salame ana can qauye jikin ta qaura ya yi la'asar, ba kowa ne da yasan ta a da ba zai iya gane ta ba a yanzu, duk ta kode ta jeme ta rame, wahala daga ta gama wannan ta faɗa wannan,har kuma wannan lokacin Talle bai sake waiwayar su ba.

****************************

Watan karb'ar jini a wajen su Suwaiba ya zagayo,Oga Zaks ya buqaci ko a kai su, ya qara sa musu albarka irin tashi ko kuma akai jinin su kamar yanda qungiya ta bukata zaɓi ya rage ya na su Alhaji Salihu......
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼     'YAN ABUJA    💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

*Dan Allah masu tambaya daga farko ko wasu pages da ba su karanta ba ku yi haƙuri a gama dika a had'a document sai ku karanta, zan yi qoqari na yi saurin gama editing ɗin kamar yanda na yi na sauran,na gode*

page 13:

Alhj Salihu da Alhj Kalla Mazajen su suwaiba da Saudat ne ke zaune a wani wajen shan iska da suka tanada na musamman dan tattaunawar sirri,bayan doguwar shawara da neman mafita ne suka  samu nasarar tsayar da  hanya ɗaya da za su samu jinin su suwaiban da qungiyar asirin su ke da buqata a duk ƙarshen wata cikin sauqi,bayan samun mafita da nasara antattaunawar da suka yi sai suka bushe da dariy a tare suka tafa tare da furta kalmar

" 'YAN ABUJA"
Chapter 19 · 0% Book details