Sashe 30
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Oga Zaks ne ya yi gyaran murya, sannan ya fara magana kamar haka,
" A'a Salihu, wannan qorafin naku bai karb'u ba, kun san qa'idar qungiya, an baku damarmakin da ba kowa aka bawa irin su ba, ba dan komai ba sai dan babbar gudummawar da kuke bawa qungiya,ku kadai nake bawa damar da ban ba kowa ba a wajen nan,dan haka a wannan karon zan faɗa maku gaskiya kun bani kunya, kun karya dokar qungiya wanda ban yi zaton haka daga wajen ku ba, dan haka dole ne ku biya abinda ku ka yi,a matsayi na na shugaban wannan qungiya ina baku umarni ba shawara ba, ku je gida ku kawo matan ku nan wajen,dole ne a yanki abinda ake buqata daga wajen su, ba dan komai ba kuwa sai dan cika sharuddan Dodo, dan haka na baku nan da kwana uku, kuje ku gama sallama da su ku kawo su"
Miqewa ya yi cikin izza da fushin b'acin ran da su Alhaji Kallah suka sanya masa ya nufi hanyar waje, tafe yake dif dif dif ya na uban nishi tsabar qiba masu tsaron lafiyar shi na take masa baya,Alhj Salihu ne ya kife kan shi a Saman table ɗin gaban shi, dan a qashin gaskiya ya fara son Suwaiba duk da wautar ta da gab'untar ta,Alhj Kalla na kula da shi ya gano abinda ke cikin zuciyar abokin nashi tun ba yau ba dama ya jima ya na jin tsoron faruwar hakan dan shi Alhaji Salihu zuciyar shi bata kai ta Alhaji Kalla bushewa ba wasu lokutan ya na tausayi ko kuma ya ji ya na son mutum, wanda hakan ya sha kawo masu cikas wajen gudanar da ayyukan su, a wannan karon ba zai bari abokin nashi ya rusa masu ɗaukakar da suka jima su na ginawa ba dole ne ya taimaka masa ya kawar masa da duk wani so da qaunar Suwaiba da ya fara yi.
Taɓa abokin nashi ya yi, ya masa nuni da kofar fita daga babban hall ɗin alamar su tafi kenan, miqewa ya yi da kyar jikin shi a mace suka fice, tun kafin su bar wajen kuwa mutanen wajen ke ta 'yan gulmace gulmace , ko ina ba a raba mutane da gulma,bayan sun isa gidan Saudat ne, suka shiga inda suke tattauna matsala irin haka in ta taso musu suka zauna, Alhj Kalla ne ya fara magana, dan ya kula in bai yi ba Alhj Salihu ba zai ce uppan ba,
" Salihu ni ban ga abin d'aga hankali a maganar nan ba fa, duk da ni kaina a yanzu haka na fara son yarinyar can,koba komai duk matan da muke huld'a da su yaran nan na kula suna da na su sirrin daban a jikin su, ga yarin ta ga kyau, amma kasan bijirewa Oga Zaks na nufin qarewar arziqin mu, niko dana talauce gwanda na aikata abinda yake so, mu kaisu kawai,a yanke abinda za a yanke a jikin nasu kawai, naga dai ana ciwon cancer ma a yankewa wasu nan ɗin kuma su ci gaba da rayuwa"
"Ba zaka gane ba abokina, in ba wajen a ina mutum zai na hutawa? Kai ni fa bari kaji ba zan iya bane kawai, duk sokoncin yarinyar nan ina son ta, dan in tare kake da ita ta b'aro maka wani haukan sai ka ji kamar ka yi ta zane shegiya, amma kuma yarinyar tayi ta na da wani sirri na daban wanda ba kowacce mace ake samu da shi ba, banjin zan iya rabuwa da ita, yanzu ni dai shawarata shine su je gida kawai su ga gida na kwana ɗaya ko biyu in suka dawo munga ya za ayi, tinda kaga bai kamata har in ma mutuwa za su yi tsohon su bai gan su ba, dan ta uwar su ita ta jiyo banda case da ita ni"
"Haka ne kayi gaskiya, to bari na faɗa masu kawai gobe su shirya zasu gida ko ya kace, dan da kaina ma zan haɗa mata kayan ta dan ta tabbatar da gaske nake tunda a ganin ta ni ne bana so su je ganin gida dama,ahmmmm ai sai ka tashi ka tafi ko? dan kuwa ina so na yi sallama da iyali na, bamu san ya abubuwam zasu kaya ba"
Dariya suka yi suka tafa,Alhaji Salihu ya ce,
"Shegen sama nima ba ri na hanzarta na koma gida na taya ta haɗa kaya kuma mu yi sallama"
Yanda suka tsara hakan suka gudanar, washe gari da asussuba su suwaiba suka ɗauki hanyar kano kowa da drivern ta dan wadata, ga wata mota nan shaqe da kayan arziqi na bin su a baya, haka suka isa garin Kano direct gidan su Suwaiba suka isa, Goggo Sarai duk ta baza wa dangi da 'yan unguwa zuwan su Suwaiba dan haka gidan a cike yake da jama'a kowa ka gani ya na cikin doki da murnar ganin dawowar 'YAN ABUJAn,sanda motocin suka parker a qofar gidan nasu basu fita ba sai da drivers suka fita da sauri suka buɗe musu motar sannan kowaccen su ta fito hannun ta riqe da manyan wayoyi da jakunkuna masu tsada da kyau,a hankali suke takawa tare da d'aga wa mutane hannu suna sakin murmushi kamar wasu matan gwamnoni,da Salma suka fara yin tozali kanta a bisa cinyar Mama Bilki tana mata kitso a kwance kamar wata jaririyar ta, salati Suwaiba ta yi ta kalli Saudat sannan ta ce,
" Sudat me nake gani haka ni Suwaiba? Yaushe gidan ya koma haka? Da jin muryar ta Salma ta miqe da gudun ta ta yi kansu tana ihun murna ta na fad'in,
" Goggo ! Goggo fito ga su Adda sun zo, Mama kinga su Adda sun zo, ina Baba? Baba fito ka ga ikon Allah su Addana ne a gidan yau"
Shanye mamakin ganin yanayin Salma suka yi aka ci gaba da murna ana gaisawa da jama'a amma cikin ransu akwai tambayoyi masu tarin yawa dangane da rayuwar qanwar tasu Allah Allah suke mutane su tafi su zauna su ji me ke faruwa, shi yasa da sun gaisa da mutum sai su bashi dubu d'aya ko biyu, su kuma mutane ana basu kuɗi sai su yi godiya su bar gidan dama su suka kawo su,dakin su da Goggo Sarai ta sake gyara masu suka shige su na shiga ciki suka tadda Goggo Sarai da ta danne murnar ganin yaran nata bata bazama ta taro su ba, ta yi hakan ne dan ta nuna wa mutane ita fa mai aji ce uwar matan manya,su na shiga kuwa Goggo ta fashe da kukan daɗi, bakin ta kuwa ya qi rufuwa saboda murna, su kan su su Suwaiba sai da suka zubar da kwallar farin cikin ganin mahaifan nasu basu san sun yi kewar su sosai ba sai yanzu da suka gan su, nan fa aka hau gaishe gaishe ana tambayar juna bayan rabuwa,wata shewa Goggo Sarai ta sanya ta daki cinya sannan ta ce,
" Ayyyuririri ! kai yau ni saratu na ji dad'i na,shiyasa nake son Allah dan kuwa akwai shi da biyan buqatar bawa Jama'a ku dubi yarana , san kowa baqin cikin marashi, ga kuɗi ga kyau, ga hutu, na ji daɗin zuwan ku yarannan, ya mazajen naku? Su na can an baro su a Abuja , waiwaiwaiiii Allah sarki garin daɗi na nesa"
Cikin murmushi da d'agun kai irin na mutanen da aka gama yi wa kirari suke jin kan su ya kumbura suke amsawa a cikin taqama,
"Suna lafiya suna gaida ku, ga abubuwan kayan abinci nan da kud'ad'e da suka aiko a baku ke da Baba"
Cikin murna kamar zata kifa ta dafe kudin dika har na Baban nasu, ta jibge su a gefen ta ta na ci gaba da washe baki ta na surutu,shi kuwa Baba ko wajen kud'in bai kalla ba, ya yi masu godiya, Mama Bilki ce ta shigo ɗauke da ruwan Pure water a plate ta doro masu sanyi ta kawo masu, ajewa ta yi ta zauna dan a gaisa,Goggo Sarai ce ta haɗe fuska ta ce,
"Wai ni shin gaisuwar nan dole ce ne, a bar yara su huta dan Allah, na ga dai duk baqin sun tafi dan a bar su su huta to a bar su su huta mana haba,kuma in banda abin talaka ma duba fa wa zai sha wannan ruwan, dan Allah ki je an yafe Allah ya bada lada"
Goggo Sarai na gama maganar ta suka haɗa baki da yaran cikin shewa suka furta,
" Hahaiiiiii Casssss sai Goggo, ashe ana nan ana ci gaba da gashi, Allah dai ya sassaka Goggon mu"
Dariya ta yi cikin isa tana wani d'aga hanci ita a dole uwar masu kuɗi ,Mama Bilki ce ta tashi ta ja hannun Ammar da ke son shigowa suka yi gaba, Salma ma tashi ta yi rai b'ace ta fita,cike da mamaki suka bi su da kallo dikan su, Saudat ta ce,
"Wai ni Goggo me ke faruwa ne me nake gani haka tun da muka zo? Salma da waccan matar a tare? Me kenan?"
Baba ne ya basu labarin duk abinda ya faru da salma nan da nan suka hau jin tsananin tausayin 'yar uwar su akan wahalar da ta sha, sannan ya qara masu da labari akan irin hukuncin da ta yanke na zama wajen Mama Balki, anan ne ransu ya baci sosai, suka k'wala mata kira, bayan ta shigo ne suka balbale ta da faɗa kowa da abinda yake faɗa, sai da ta tabbatar sun gama ta miqe ta yi waje ba ta tanka ma kowa ba a cikin su, da bala'i Suwaiba zata bita ta dake ta amma Goggo ta hana ta ta ce,
"Ai ni yanzu na cire ta a Yarana nima, taje can ta qarata, ina da ku kun ishen rayuwar zaman duniya har ma da qiyama, kuma yanda ku ka yi jan nan da alamar kuma kuna ɗauke da ciki, dan haka jika ne nake matuqar kwad'ayi yanzu a duniya fiye da komai, ta je ta yi ta fama, ita ta sani naku sun ishen zaman duniya dai ba na qiyama ba"