Sashe 56
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da misalin ƙarfe goma na safe su Juwairiyyah ne suka gama shirin tafiya Abuja sun shirya kayan Abrar da komai da take da buqata a wani akwati,Sallama suka je yi ma su Innarmu tare da qudirin sanar da su hukuncin da suka yanke suna zama su suwaiba da Salihu suka shiga,cike da fara'a suka gaggaisa, Abrar na ganin Suwaiba ta hau yunqarin zuwa wajen ta, cikin shauqi da kewar yau zata rabu da Abrar ɗin ta ta ɗauke ta ta rungume tana kissing din ta, ita kuma sai dariya take yi ta zaci wasa ake yi mata, k'walla Juwairah ta share ta tsananin son 'yar ta ta amma haka zata bawa Addan nata ita dan kuwa gaba ɗayan su sun san matsalar da take ɗauke da shi na rashin haihuwa,cikin murmushi Juwairiyyah ta miqa wa Addah Suwaibah akwatin yarinyar tace,
" Addana daga yau kin zama Ummu Abrar, dan Yah Jabeer ya miki kyautar ta gaba ɗayan ta, kin cancanci zama uwa a gareta, dan haka ga ta nan dama ita ba wai ta damu da nono bane, kunun nan da kike bata shi yakamata ki ci gaba da bata, Allah ya raya maku ita da imani mu zamu wuce muna yi maku fatan alkhairi"
Ta ja baya Suwaibah da Salihu tare da Innarmu da kuma Abbah Balarabe sai suka shiga wani irin yanayi na tsakanin mamaki da ta'ajibi, Abbah ne ya iya magana ya ce,
"A gaskiya Juwairah ke alkairi ce ga rayuwar zuri'ar mu baki ɗaya daga birni har qauye, tabbas Qanina da Bilkisu sunyi matuqar qoqari wajen baki tarbiyya managarciya, baki nufin kowa da sharri a rayuwar ki kullum alkhairi ne a tsakanin ki da kowa,wannan shine dalilin ne ya sa kika zamo mai samun nasara da ɗaukaka a rayuwar ki, Allah ya yi muku albarka, kai ma Jabeer na ji daɗin wannan kyauta da ka yi, duk da nasan ita zata saka ka yi, amma da baka aminta ba da hakan bai samu ba,"
Sai a wannan lokacin ne su Suwaibah suka fita daga yanayi na mamaki suka hau godiya ba qaqqautawa, Innarmu ce tace,
" Suwaiba Allah ya taya ku riqo, ya sa ki qoqarta bata tarbiyya mai kyau yanda zata tashi abar so ga kowa"
Cikin kukan farin ciki Suwaibah da mijin ta ke gyad'a kai alamar za su yi duk abinda ya dace dan baiwa Abrar rayuwa mai inganci,daga qarshe Suwaibah zuwa ta yi ta rungume qanwar tata tare da durqusawa a gaban Jabeer ta na kuka, d'ago ta ya yi ya na buga bayan ta da sigar lallashi, yana kada mata kai alamar ta dena kuka,Salihu ne ya je ya miqa mai hannu daga baya ya rungume shi ya saki kukan murna Shima dan kuwa sun yi masu kyautar ba zata,
" Na gode ! na gode ! Ban taɓa ganin mutanen kirki irin ku ba,baku yi la'akari da rayuwata ta baya ba kuka mana wannan kyauta Allah ya faranta maku, ya baku yara masu albarka,Allah ya bamu iKon kula da ita fiye da yanda za ku yi mata,"
"Ameen"
kowa ya amsa sannan su Juwairiyyah suka ja akwatin su suka tafi zuwa mota,suna barin qofar gidan nasu Juwairah ta saka kukan rabuwa da 'yar ta, hannun ta Jabeer ya kama shima yana jin wannan kewar na damun zuciyar shi, amma ba yanda zasu yi dole su yi haƙuri na ɗan lokaci ne, Allah ya basu ladan abinda suka yi a hankali Juwairiyyah ta warware suka hau hira har daga baya bacci mai daɗi ya ɗauke ta........
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 32:
Ba a tafi kai amarya Nafee d'akin ta ba sai da misalin 10am saboda kukan da suka tsaya yi ita da Innarmu da Juwairiyyah sai kace idan an rabu ba za a sake haɗuwa ba, kuka suka dinga zuba wa har sai da suka ba wa mutane tausayi shaquwar da ke tsakanin Innarmu da Nafee ba karama bace domin kuwa ko hutu Nafee ba ta zuwa gidan kowa kullum ta na tare da Innarmu su yi faɗa su yi daɗi,sai gashi yanzu aure zai raba su zai kai ta can nesa garin da ba ta da kowa, nasiha aka dinga yi masu tare da nuna masu ai rabuwa ba mutuwa bace wata rana za su gana,har a cikin mota Nafee bata daina kuka ba a haka suka kama hanyar garin Kebbi dan kuwa anan ne za ta tare.
Mama Balki da Saudat na daga cikin 'yan kai amarya gidan ta dan kuwa kowa ya san halin Goggo Sarai idan aka ce ta je zuwa za ta yi ta zubar wa da Nafee mutunci a gidan surukan ta musamman da yake su na da rufin asiri,har yanzu halin ta na son abin duniya na nan sai dai kwad'ayin ace yaranta ne ke da dukiyar ya ragu gudun kar a koma 'yar gidan jiya, ga wani irin jiji da kai da take yi, ta ji zafin rashin tafiya da ba a yi da ita ba amma haka ta jure ta danne saboda kar ta yi magana a yi mata caaa dan ta kula dangin mijin nasu haushin ta suke ji tun da suka samu labarin abinda ya samu su Saudat.
Juwairah ta so matuqa ta je amma Abrar ta sha gajiyar biki bata da lafiya dan haka Jabeer yace ba inda zata kar su je gajiyar hanya ta sake sanya 'yar shi rashin lafiya,ai kuwa haka ta zauna ta dinga kuka har dai daga qarshe ta ba wa kan ta da kanta hakuri.
Cikin masu kai amarya har da qannen Abbah Balaraben su Goggo Karima da Goggo Mero,sai ta bangaren Innarmu ma mutum biyu aka zab'a Inna Fateema da Inna Aishe, sai kuma wata aminiyar Innarmu wato Baba Maryam,lokacin da suka isa Birnin Kebbi dare ya yi sosai gaba dayan su jikin ta qaura ya yi la'asar, a unguwar Alieru Quaters motoci guda ukun da suka d'akko amarya suka tsaya,tun daga yanda gate ɗin gidan yake zaka gane fasalin gidan nasu gidan ya bambanta da na sauran mutanen unguwar,kana kallon gate ɗin zaka san gidan masu akwai ne, yan uwan ta sai san barka suke su na yi mata addu'ar Allah ya zaunar da ita lafiya ya sa gidan zaman ta ne na mutu ka raba, kwanan su biyu suka fara shirin komawa Kano,Saudat kuka tasa data tuno nisan hanyar da suka kwaso, sai lallashin ta ake abokin angon daya tuqo su yana ta mata dariya ya ce,
" A gaskiya zan faɗa ma Umar farouq ya shirya matar shi raguwa ce"
Ta na jin haka ta miqe ta goge hawayen ta tare da zabga masa harara ta ce,
"Inji waye ya ce maka ni raguwa ce? Ni kar ka wani fada masa komai mu tafi"
Dariya aka saka a wajen banda Nafee da take rab'e a gefen mijin ta ta yi kalar tausayi, ai ko suna barin qofar gidan nasu ta fashe da nata kukan,'yan kai amarya na hanya suna tausayin Nafeen, ganin yanda take zubar da hawaye ne ya sanya angon ta ɗaukar ta cak a hannun shi ya yi ciki da ita yana lallashi, mijin Nafee ya na son ta sosaiii ya na da kirki gashi da kulawa da tattali gefe d'aya kuma ya na tausayin matar shi duba da garin da ya kawo ta bata da kowa sai shi.
Bayan dawowar su Saudat Kano lafiya ne aka kai kowa gidan ta aka aje ta, abokin angon daya kawo su Mama Bilki ne ya tsaida Saudat, cikin kashe murya ya ce,
"Ba daban Farouq ya rigani ba yana da kirki da nagarta tabbas dana kawo kaina nima,zuciya ta ta kasa haƙuri ta ce kar na tafi ban sanar dake sirrin dake raina ba,Saudat na kamu da son ki a kwanakin nan da muka yi tare, ina maki fatan alkairi, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mumina saliha"
Saudat ta ji daɗin yanda ya ke da fahimta da addu'o'in da ya musu,ta kula shi ɗin mutum ne mai natsuwa da hankali, murmushi ta yi sannan ta ce,
"Na gode sosai da soyayyar ka a gare ni, ina ma ka fatan alkairi, Allah ya baka wadda ta fini, tabbas abotar ku akwai amana kuna da halin manya,"
Murmushi suka yi sannan daga baya ya mata sallama ya ja ya tafi.
Kwana biyar tsakanin bikin Nafee masoyan huɗu suka hau musayar saqwanni da jaddada manufar su ta son auren su Saudat ɗin, dan haka su kuma suka ce su zo su sami Baban su a San da zaman su.
Babu b'ata lokaci kuwa wata ranar lahadi da yamma wasu dattijai suka zo gidan Baba Baballe dan nemawa Farouq da Ibraheem auren su Saudat ɗin,a wasu manya-manyan motoci suka zo wanda yasa baba jin tsoron kar a maimaita 'yar gidan jiya fa,daga ƙarshe dai Baba ya kirawo yayan shi wanda ya jima da fara bincike akan zuri'ar gidan su Farouq ɗin tun da Jabeer ya sanar da shi labarin da Juwairiyyah ta faɗa masa game da yaran, ya na zuwa ya tabbatar wa da Baba Baballiya ai mutanen kirki ne a nan take suka roqi arziqin a d'aura auren in babu wata damuwa, saboda ba a kusa suke ba kowa da garin da yake aiki, shi Abban su Farouq mazaunin Abuja ne sai qanin shi dake lagos, dayan kuma a kebbi yake, Baba Baballe sawa ya yi a kira wani kawun su daya rage masu da abokin shi babba ga kuma Yayan shi aka haɗu aka daura auren su Saudat da Farouq, Salma da Ibraheem akan sadaki naira dubu hamsin hamsin, tare da alqawarin Ibraheem zai riqe yaran Salma kamar nashi in sun masu izinin hakan, su Abbah sun yarda amma sun qara da cewa in babu takurawa sun masa izini,su kuwa iyayen su Farouq suka jaddada masu cewa shi Ibraheem da kan shi ya sanar masu ba Salma kawai yake so ba, har da Yaran ta ya gani ya kamu da qaunar su dika,Baban su Suwaiba ya ji daɗin hakan sosai, a haka taron ya tashi cikin farin ciki da yarjejeniyar sanda duk Amaren da angwayen suka shirya a tsakanin su sun tare.