← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 61

Sashe 35

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kammala meat pie ta ɗora ruwan kunu bayan ya tafaso ta dama masu koko da d'umamen tuwo ta kai masa dan ya karya, a shirye ta gan shi tsaff ya na sake duba jakar shi da k ta hada masa tun cikin dare.

Cikin wata roba fara ta zuba masa meat pie sannan ta zuba masa zob'on da ta haɗa tun jiya da yamma mai daɗi a gora ta d'aure bakin ta da kyau ta saka a leda har biyu dan kar ya b'ata masa takardu ta zuba duk a jakar ta zuge,kallon ragowar meat pie din ta yi ta ga ba laifi da yawa za a samu wanda za a baiwa surukan su idan sun zo da rana dan neman auren Nafee, ɗan girki kawai zata qara yi shikenan sannan an fita kunya tunda sun san gidan da za su zo neman auren ba na masu da shi bane, d'aki ta shiga ta ga ya kammala komai ita yake jira su yi sallama,ta na qarasa shiga d'akin ya ja ta jikin shi ya na bin fuskar ta da kallo ya ce,

" My princess ba abinda zan ce maki sai dai na yi maki fatan shiga aljanna, tin da ance sai miji ya yarda da matar shi sannan za ta shiga aljanna, My Juwairiyyah na yarda da ke ina rokon Allah da ya sanya min ke a aljannah madaukakiya, ke macen kwarai ce Juwaireren mama, matar da kowanne namiji zai yi fatan samu,macen da zan iya nunawa duk duniya ta gani ba tare dana kunyata ba, Allah ya sauke ki lafiya, ya shiryar min dake , Allah ya qara miki imani, kinga ga riqe wannan ba yawa kwana biyu zan yi kamar yanda na sanar dake, ki yi ta tayani da addu'a inna samu aikin nan zamu samu hutu sosai, zan jiyar da ke daɗin da baki taɓa zato mace zata iya samu wajen mijin ta ba, Juwaireren Mama ina son ki, Allah ya yi maki albarka"

Tun da ya fara magana Juwairiyyah ke murmushi sai dai ya na  cewa Juwaireren mama ta turo baki tana buga qafa,sannan ta ce masa,

" Ni dai Yah Jabeer bana so, taso ka tafi kar ka makara, Allah ya karen kai mijina kaje lafiya ka dawo lafiya, Allah ya bada sa'a a abinda aka tafi nema, inshaa Allahu kai me nasara ne akan komai na alkairi da ka sa a gaba, dan haka kar ka ji wata damuwa ko ka sa shakka a lamarin,zaka iya miji na saboda kai din na daban ne a cikin mazaje,karka manta da karanta lahaula wala quwwata illa billahi, da hasbunallahu wa ni'imal wakeel,sai kuma hasbunallahu sa'yu'utinallahu min fadhlihi inna ilallahi raghiboon,Allah zai zama jagoran ka, zai taimaka maka ya kare ka, ina son ka Yah Jabeerun Baba"

Ta karasa maganar ta tare da miqewa da sauri tana dariya bin ta ya yi ya cafko ta ya haɗe ta da gini ya na dariya Shima ya ce,

"Maimaita me kika ce in ba tsoro ba"

Turo baki ta yi cike da shagwab'a tace,

"Yo ni me nace, dan dai kawai an ga yau mijina zai yi tafiya shine za a yi min yar qure a ci zalina, Yah Jabeer irin wannan kallon da kake yi min ji nake kamar na dawwama da kai a haka a tsaye ba tare da duniyar ta juya ba"

Ta karasa maganar ta cikin yin qasa da muryar ta, wani irin farin ciki ke ziyartar zuqatan su a wannan lokacin suna jin kamar kar su rabu da junan su, a cikin ran su kowa na yaba kyau irin na dan uwan shi, sumbatar ta ya yi da salon bankwana wanda Juwairiyyah ta biye masa dan faranta ran mijin nata, Nafeesa ce ta yi sallama ta shiga dayake Juwairah tace ta zo su yi komai da wuri zata je gida a yau d'in, janye jikin shi ya yi a kasalance ya riqe hannun ta ita kuma ta kwantar da kanta a jikin shi, fita suka yi tare idon ta taf hawaye, yau ce ranar farko da zai yi tafiya mai nisa tin bayan auren su, saurin maida kwallar ta tayi kar ya gani hankalin shi ya tashi, sai dai inaa ta makaro dan kuwa ya gani,cikin muryar lallashi ya ce,

" Haba my Queen, ki kwantar da hankalin ki mana, inshaa Allah jibi da yamma kina maqale a jikin mijin ki kamar haka,daga wannan tafiyar ba zan sake yin wata tafiya ba ke ba ko ina zan je to fa qafa ta qafar ki kin ji"

Kamar wadda ya ce wa ta yi kuka haka Juwairiyyah ta b'are baki irin na yaran nan masu rikici ta fara kuka, rungume ta ya yi a jikin shi ta yi kukan ta son ran ta da kan ta ta yi shiru ta sake yi masa addu'a, suka fita tare har Nafee suka raka shi wajen Innarmu Itama ta masa addu'a daga qarshe ta hau tsokanar Juwairiyyah,

"Tooo kukan rabuwa da masoyi aka shaaaaa ?? Hoh yan zamani ba ko kunya to d'akko mayafi ki bishi kawai 'yannema sai kace cinye ki za mu yi kafin ya dawo"

Juwairiyyah na jin haka ta saki hannun Jabeer ta taka da gudu ta bar wajen tana dariya, suma dariyar suka yi mata, sai da taje baqin qofar shiga wajen su ta juya, dan tsuke bakin shi taga yayi alamar kiss, ta waro ido ta kalli su Baba Balarabe dake gefe zasu raka shi qofar gida, rufe baki ta yi da hannun ta ta fada wajen nasu tana dariya,

" Allah sarki mijina,kaje lafiya ka dawo lafiya cikin sa'a da nasara, tare da kariyar Allah"

Nafee ce da ta biyo bayan ta tace

" Ameen masoyan asali"

Murmushi suka yi wa junan su sannan suka shiga kitchen dan fara aikin da ke gaban su, leqa parlour Juwairiyyah ta yi ta duba lokaci ta ga har takwas da rabi ta wuce,cikin sauri ta ɗauki kwaryar da ke ɗauke da masarar da aka barza ta duba ta ga tabbas za ta isa su yi dambun masara, nan da nan suka je suka tsinko zogalen da Juwairah ce ta shuka da hannun ta da alayyahu, sai albasar su mai lawashi, gyarawa suka yi suka dake gyad'a, da kayan qamshi attaruhu da maggi da gishiri suka saka yanda zai isa ya yi daɗi suka zuba wa wankakken tsakin su suka dora a wuta.

Cikin qanqanin lokaci dambun masara mai daɗi ya haɗu, man gyad'a Juwairah ta soya da ya ji albasa, suna kammalawa Juwairiyyah ta d'akko mazubi masu kyau ta zuba komai a inda ya dace har zob'on da meat pie sai da aka zuba su a waje mai kyau da tsafta.

  Nafeesa ta ji daɗi sosai dan haka duk inda Juwairiyyah ta sa kafa Nafeen na biye ta na godiya da addu'a har saida ta ba Juwairah haushi,dan kuwa godiyar ta yi yawa a cewar ta, ajewa suka yi a gefe Juwairah ta sa Nafee deb'o wani alayyahun da albasar mai ganye, ta sa ta gyara su ta daka kayan miya wannan karon harda tumatiri, jelop rice mai daɗi ta dafa wadda ta yayyanka ɗan naman a ciki qanana ,kasancewar nama bashi da yawa yasa Juwairah tace bari su yanka qanana sai a soya sama2 su saka a abincin, har da dan carrot ɗin su, nan da nan sai ga girkin da su suke ganin anyi a talauce ya koma a yalwace, dan kuwa wata macen ma ko an kawo mata kayayyakin girkin da ya fi wannan ba lallai ta tada abinci mai kyau da daɗi kamar wannan ba.

Wanka ta tafi ta yi ta sa Nafee taya ta gyara gidan, dan bata son fita ta bar gida da datti in ta dawo ranta baya yi mata daɗi, sannan kuma ta san idan bata gyara ba zata dawo da gajiya sai dai a bar gidan ya kwana da datti kenan

Wasu matan taqamar fita za su yi unguwa sai su bar gidan kamar bola su tsallake su tafi abun su,idan baki gyara ba ki ka tafi ki ka dawo ki na iya yin baqin kunya su tadda gidan ki g kaca-kaca, ko kuma ki dawo a gajiye ga shi maybe miji ya kusa dawowa, shima ya dawo yaga yanda ya fita haka ya tarar wataqila harda qarin datti ma, amma in kika gyara gidan ki fes in da hali ma har girki ki yi ki ajiye, da kun dawo wanka zaki yi kawai ki faɗa gado ki huta,maybe sai bacci ma tinda baki da aikin da za ki yi.

Sai da ta gama shirya wa tsaf sannan ta zauna ta ci abinci a gaggauce ta rufe sashen ta ta sanya mayafin ta ta riqe jakar ta a hannu mai ɗauke da waya da ɗan kud'in abun hawan ta ta wuce bangaren Innarmu ta yi mata sallama ta dau hanyar gida cike da zumud'i da d'okin ganin iyaye da 'yan uwa ta.

Mai adaidaita sahu na ajiye ta ta sallame shi ta shiga cikin gidan su bakin ta ɗauke da sallama,ba wanda ya ji ta ma ballantana a amsa mata saboda ta isko ana ta daru akan komawa Abuja ,ita Saudat tace bazata koma ba, Suwaiba kuma ta shirya tsaf da shirin tafiya ta na tursasa Saudat akan sai sun koma tare Goggo ma ta sa ta a gaba da magiyar ta daure ta koma, ba zai qara dukan ta ba, Shima kuma Baba ya kafe Saudat ba zata koma ba tinda bata so mijin nata ya biyo ta da takardar sakin ta idan a son shi ne ma ita kanta Suwaiban ba za ta koma ba,ganin abun ya qi ci ya qi cinye wa ne ya sanya Mama Bilki cewa,

" Ayya Goggon su tinda ta ce bazata koma ba a barta mana in aka kwan biyu kin taushe ta sai a maida ta dakin ta"

" Ba laifi yau ɗaya kin yi magana mai ma'ana,Allah ya kaimu ta huce an maida ta ɗin, dan kuwa 'ya ta ba zubin zaman Kano bace zubin rayuwar Abuja ce ah toh"

Cike da rashin kunya Saudat ta kalli Mama Balki ta ce,
Chapter 35 · 0% Book details