Sashe 18
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri take yin komai ba tare da son jiki ba,dan ba ta son sai ya dawo ne zata yi wadannan abubuwan, ya na dawo wa daga masjid ya tsaya wajen Innar mu su gaisa, kamar kullum riqe shi ta yi da surutai na ba gaira ba dalili, daga baya ne ta fara tura masa saqon dake ranta cikin dabara irin ta masu son qulla sharri,
" Allah sarki Juwairah yarinyar nan akwai hakuri, kaga fa yanzu wata na wajen shida kenan da auren ku amma ba wani labari,gashi duk qawayen ta sun haihu ma su,ita ko da b'atan wata bata taɓa yi ba ka ga sam bata damu ba, ko dake dama yaran zamani ai ku ba ruwan ku, mu ne dake son yan jikoki mu za mu damu, waya sani ma ko maganin hana haihuwa take sha"
Wani irin faduwar gaba ne ya samu Jabeer ido ya zaro waje yace,
" Haba Innar mu Juwairan nawa take d zata yi wannan tinanin? Kuma har ta aikata hakan ma? Inaaaa sam ba zata yi haka ba kima daina wannan tinanin dan Allah, kuma da kk zancen sa'o'in ta Innar mu Nafeesa ma fa sa'ar ta ce ita kinga ai har yanzu ma bata yi aure ba, in da zaki gane komai nufi ne na Allah kenan"
Da jin wadannan kalaman daga bakin Jabeer sai Innarmu ta ji kamar ya watsa mata wuta, bala'i ta fara yi kamar ta ari baki,cikin masifa ta ce,
" Inyeeeee lallai ne Jabeeru ka nuna min mata tafi 'yar uwar ka ko? Har qanwar ka zaka duba ka yi wa gorin aure? To bari na faɗa maka abin da nake boye maka, nifa na fara gajiya da wannan yarinyar, tin da ka aureta ka daina bamu lokacin ka, ka daina zama ai hira kamar ta da da kai, sannan gaba ɗaya soyayyar ka da kulawar ka ta koma wajen ta, akan me?"
" Akan shi ne mijin ta, kuma hakan da yake shine yake nuna ya haifu ɗan sunna daga iyayen shi,yanzu dan Allah ba ki ji kunya ba? Kike haɗa kan ki da surukar ki?sannan 'Yar ki ta wani bangaren? Habaaaa Hansai, wace irin rayuwa kk daukar wa kan ki yanzu, abinda ba halayyar ki ba kina neman shaid'an ya maki huɗuba ki fara yi, to bari na faɗa maki abinda mata kan ku yake toshewa akai, kowacce mace dangin miji ce, kuma uwar miji ce wataran in ranta ya kai, dan haka in ki kai wa matar dan ki adalci, kema sai wata ta yi wa taki 'yar adalci, in kk kyautata wa matar wanki ko matar qanin ki, kema naki qannen mijin da matan yayun sa zasu tausaya maki su miki adalci, in kuma duk kin kiyaye amma ana maki abinda bai dace ba, to ki sani kowanne dan Adam akwai jarabawar shi, wataqila taki anan take, sai ku hakuri ki yi qoqari kuma ki cinye jarabawar taki, dan haka in kk kula, tin da Jabeeru ya yi aure kulawar da na ke ba ki ta qaru, ba dan komai ba sai dan kula da na yi kin kai idon ki gidan matar dan ki, ki gyara hali ko kin samu rabauta a lahira, baki tafi da haqqin kowa ba, haihuwa ta Allah ce, ko bata haihuwa haka yaga zai zauna da ita ke baki isa ki ce dan me ba"
Baba Balarabe kenan ya ke yi wa Innarmu faɗa akan abinda take yi mara kyau, wanda ya dad'e a tsaye yana jin maganganun Innar mu, wata irin nadama da kunya ce ta kama ta nan take cikin jin nauyi ta furta,
" Malam ka yi hakuri, Jabeeru ka yafe min sharrin zuciya da shaid'an ne, baqin ciki na da tin da ta zo komai namu ya ja baya, ga shi kana nuna mata tsantsar so, idona ya rufe akan hakan na manta nima nawa mijin yana iya qoqarin shi akaina, ku yafen ba zan qara ba"
Nan ta zayyano yan sace2n da tai ta yi wa Juwairah dan ta haɗa su faɗa da Jabeer amma sai ta ji shiru, sakamakon iya zaman duniya da Juwairah ke da shi da ta kula hakan ta faru zata san dabarar da ta yi ta bashi hakuri, da jikin ta da kalaman ta,
" Babu komai Innarmu ya wuce ke uwa ce a wajen ta, da bata ɗauke ki a uwa ba uwar miji ta ɗauke ki da ita kanta zaman sai ya mata wuya amma tasan ko da uwa da uba ana sab'awa fiye da haka ma a kuma ci gaba da zama, dan haka na san ba ta qullace ki ba, jiya kwana ta yi ma ba lafiya, asibiti zamu je yanzu ma ni take jira na san"
" Subhanallahi"
Suka hada baki dika ukun har da Nafeesa suka fada,Innar mu ce ta furta,
"Meke damun ta?"
" Da ciwon jiki ta kwana ga zazzabi da ciwon kai, ciwon mara da yawan kasala, dan jiya wani irin bacci ma ta dinga yi"
Murmushi Innar mu ta yi sosai sannan ta ce,
" Ikon Allah ai ya kamata a kaita ta ga likita bokan turai a fada mana wata nawa ne, na fara tanadin kayan kwalliya dan da alama bana zan yi ango nima, in kishiya ce na samu na gyaran daki,kar ta zo ta fini a Wajen Malam"
"Innar mu me kk nufi da hakan?"
Nafeesah ta yi tambayar cikin mamaki, Jabeer kuma a ranshi cewa yake yi,
'Allahumma ameen Allah ka amsa ka sa hasashen Innarmu ya zama gaskiya'
A zahiri Kuma ya ce
" Innar mu bari na wuce naga ko ta shirya mu tafi kar mu makara"
" To Allah ya qara afuwa"
Tashi ya yi baki a washe kamar gonar audiga ya isa sashen nasu, qamshin da ya ji ne ya qara kwantar masa da hankali da nutsuwa tare da qaunar matar tashi da yake matuqar so, sallama ya yi ta amsa cikin muryar da ke tafiya da hankalin shi,durqusawa ta yi ta gaida shi, ya amsa tare da jawo ta jikin shi, d'aga kanta ya yi yana kallo, wata riga ta saka shara2 ko ina ana hangowa a jikin ta, sai wando guntu rigar bata gama rufe mata cibiya ba , ta yi parking gashin ta a tsakiyar kan ta, fuskar ta ta yi fayau kyaunta ya qara fitowa, the more yana kallon ta the more yana qara ganin kyaunta, bata cikawa fuskar ta makeup ba, iyakar ta powder da lipstick, sai tirare da ta fesa ta shafa mai, zame rigar ya yi daga kafad'ar ta yana shinshina wuyan ta, maida ita ya yi baya ya tsaida ita ya na kallon ta,cikin shagwab'a Juwairiyyah ta ce,
" Babe ni dai bana son wannan kallon da kk man ya yi yawa, tin da ka shigo kk ta kallona"
Ta wani sake narkewa a jikin shi tana wani dan zame wa shi kuma da sauri ya janyo ta, gaba daya ta gama rikita shi, daukar ta ya yi cak suka yi daki, ban qara sanin me ake ba sai da naje na wajen Innarmu na sha kokon safe na dawo a gadon na hango su suna manne da juna, Jabeer ne ya ce,
" My princess , jiya kin manta yau munyi zan kai ki asibiti ne? Gaba daya naga yanda jikin ki yake jiya da yamma yau kin tashi garau da ke" Eh My dear, kaga in banda da asuba dana tashi na ji kaina na ɗan ciwo kadan, sai da na zo brush warin toothpast din ya sani amai, tin da na yi aman nan na ji daɗi daga nan ban sake jin komai ba, ni fa Ina jin ma na warke ba sai mun je ba ma"
" A'a ba haka za ai ba, ya kamata mu je asibiti muji me ke saka motsin da kk ji ko ya daina"
"Ah ah ya na yi har yanzu"
Jabeer ne ya shafa cikin nata da tausayawa, nan da nan idon ta ya ciko da kwalla ta ce,
" Ɗazu ma fa sai da ya min, ga tsoro da yake ban in ya motsa din, sai naji kamar wani abu ne a ciki"
Ta qarasa tana mai sakin kuka
" Yi shiru my princess bari kuka,ba komai inshaa Allahu sai alkairi, u don't have to worry ur self babe, koma meye zamu samu maganin shi tashi muje mu yi wanka mu shirya muje"
Tashi ya fara yi sannan ya miqa mata hannu ta kama, a hankali ta miqe tsaye sai yanzu ya qara ganin qirman da qirjin ta yayi, ga cikin ta ya dan tasa ta qasa, ta yi wani fari sosai, kamata ya yi ya zura mata doguwar riga da dan hijab din da take zuwa wanka, tinda gidan akwai suruka duk da ba sashen su ɗaya ba dai amma Juwairiyyah na gudun kar watarana a yi kicibus,sai shima ya zura tashi riyar sannan ya fara fita waje ya rufe qofar su,daga nan suka shiga wankan a tare bayan sun gama ne suka dawo suka shirya za su tafi asibitin ,kafin su fita saida ta biya wajen Innar mu ta gaida su sannan ta tashi zasu wuce,ta ji Innarmu na fad'in,
" Juwaireren Mama ki yafe wa Innar ki laifukan da ta yi miki domin Allah, sharrin shaid'an ne ya shige ni da son zuciya, amma in Allah ya yarda ya wuce ba zan sake yi maki duk abinda na yi a baya ba"
kwallar farin ciki ce ta fito wa Juwairiyyah ta godewa Allah da ya kawo mata komai da sauqi kuma cikin gaggawa,cikin murmushi ta cewa Innarmu,
" Haba Innar mu ai ba komai, ni fa 'yar ki ce, ke uwa ta ce, ban dauki hakan a komai ba face ma gani nake nice bana kyautata maki yanda ya kamata, nima ki yafe min,
Baba balarabe na d'aki yana jin dadin kasancewar Juwairah a matsayin surukar shi, yarinyar dan uwan shi na da hankali da tarbiyya mai kyau,ta samu tarbiyyar a wajen iyaye na gari.