← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 61

Sashe 49

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuba wannan kayayyakin kamshin ta yi ta zuba kazar da ta gyara ta wanke ta yayyanka a ciki, amma banda madarar ta ajiye ta sai naman ya dahu sannan zata zuba, sai da farfesun ya dahu sosai sannan ta zuba madarar shanun, tana tafasa ɗaya biyu ta sauke ta juye  a mazubi Mai kyau ta kaima Juwairah mai jego.

Godiya ta yi mata Jabeer na shigowa ya zauna zai saka hannu, Nafee ta riqe ta ce,

" A'a Yah ga tamu can wajen Innar mu wannan nata ne, ita fa ta haihu ba kai ba, sannan na zuba mata maganin basir a wannan ka jira tamu"

Dariya ya yi sosai har yana kama ciki ya ce,

" Yarinya ni za ki yi wa qaryar? zaki yi bayani ne kice kawai Nafeesa na hada maki kayan da zaki warke da wuri to da kyau Allah ya baki lafiya,ke kuma me maganin basir ki dena qaryar,banqi ba in an hanani ci saboda ita ta haihu ta yi wahala ya kamata taci ta yi qat, amma batun ace wani maganin basir ne ma bai taso ba, in haka ne ai na fita basir ɗin nifa namiji ne zaman kasuwa waje ɗaya wasa ne?"

Dariya suka dinga yi dikan su, Wajen jaririyar ya je ya ɗauke ta yana kallon ta yana mata wasa kamar gane wa take, wani farin ciki yake ji a ran shi, nan take ya hau yi mata hotuna, yana gamawa ya danna kiran Baban su Suwaiba dan  tun da aka yi haihuwar ya kira sau biyu bata shiga ba, sai ya sa a ran shi ko ba wuta an kai caji ne, shi yasa ya sake gwadawa.

Su kuwa a can gidan Baba Baballiya duk suna zaune a tsakar gida gaba ɗayan su har da Goggo Sarai, duk da ba wani sake mata kowa ya yi ba sosai amma sun rage gudun ta, sallama ya yi ya sanar da shi haihuwar, cike da murna kowa ke amsar wayar suna gaisawa, Juwairah kuwa sam taqi karb'ar wayar wai kunya take ji, dariya suke ta mata Suwaiba tace sai gobe zasu zo, dik da mamakin da ke a zuqatan Jabeer da Juwairah har ma da Nafee Hakan bai hana su suma sakewa da ita ba suka yi ta hira.

Bayan sun gana ne Juwairah ta ɗauki pillow da aka kawo mata dan ta zauna ta jefawa Jabeer, tana buga qafa cike da shagwab'a ta ce,

"Ni baka fad'an zaka kira su ba kawai sai dai naji kana waya da Baba, kuma wai Babana ka ke iya fad'awa na haihu, wayyo ni Allah da wanne idon yanzu zan kalle su?"

"Da idon da ki ke kallo na yanzu mana"

A haka Juwairiyyah ta miqe da Baby Abrar suka wuce d'aki dan ta kwanta ta shayar da ita Itama ta ɗan rintsa dan kuwa yanzu ne take jin bacci na ratsa idanun ta.........
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA. 💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 29:

Alhaji Kalla gaba ɗaya ya tattare hankalin shi ya mayar kan Alhaji Salihu da ke yi masa wata maganar da yake jin ba mai yiwuwa bace a gare shi,cikin nuna kafiya akan ra'ayin shi ya ce wa Alhaji salihun,

" kai nifa ba qungiyar da zan bari gaskiya, habaawaa yo me ma aka yi da maza? har yanzu fa da quriciyar mu Salihu ko hamsin bamu rufa ba, akwai sauran rayuwa a gaban mu na tuba, me zai sa kuma mu katse rayuwar mu tun kafin mu more ta?"

"Hmmmm Kalla kenan, kai abokina ne wanda na ke matuqar so saboda tare mu ka taso da kai tun mu na yara,kar ka manta dika iyayen mu da wasu daga cikin 'yan uwan mu mun bada su ta wannan harka, kana ganin zunubin bai isa haka ba? Tin da ba yanda za ai mu dawo da su? Ka duba fa in bamu tuba ba yanzu kowanne lokaci mutuwa na iya zuwa, ita bata sallama bare qwanqwasa qofa in......"

Cikin haɗe fuska da taurin kai irin na mutane marasa rabon shiriya Alhaji kallah ya d'aga wa Alhaji Salihu hannu tare da fad'in,

"Malam dakata, yau kuma da abin da kazo kenan? i am very sorry to disappoint you my friend, cos i am not ganna buy this shit, akan me ina tsaka da jin daɗin rayuwa ta kace na koma rayuwar talauci, bayan kasan sharad'in fita daga qunyiya mai da duk abinda ka mallaka ne dai-dai da allura ba a yarda ka ajiye ba ballantana ba ma za su ajiyu ba wuta ce zata cinye su ko ka manta me ya samu sauran mutanen da suka bijire wa qungiya? Idan na bar qungiyar me na tanada wanda ba daga qungiya bane kuma ka ke ganin ba zai kare ba ballantana na yi rayuwa mai daɗi ko bayan babu ƙungiyar? Haka siddan mad'alaqan kasa na koma almajirin qarfi da yaji? kan kuma ka fita kar ka manta sai an yi asiran rufe maka tinanin ka na gidan Oga da qungiya gaba ɗaya wanda a kallah zai kai nan da sati ɗaya, kai ka san dan mun riga da an bamu ɗaukaka a qungiya ne yasa akai mana wannann alfarmar da qananan yan qungiya ne kashe ka za ai ko da tinanin nan ka yi, ni dai ina nan kai kuma Allah ya taimaka ka fita lafiya, amma ka sani sisina ba zan taimaka maka da shi ba in ka talauce,amma kuma abotar mu na nan har yauma ta nade"

Baza babbar rigar shi ya yi ya fice ya bar Alhj Salihu da tinani, wata zuciyar na kwad'aita mai ci gaba da rayuwar hutu, ɗaya ban garen na nuna mai illar hakan, in ya ci gaba da zama ɗan qungiya ya kai soyayyar Suwaiba kuma inaa? da ace ya rasa abar son shi gwara ya hakura da qungiyar nan Allah zai kawo mai wata hanyar, miqewa ya yi dan shima ya bar wajen, yana tashi kuwa wayar shi ta hau ringing, dubawa ya yi yaga kiran Alhj Kallah, tsaki ya yi kamar ba zai ɗauka ba, dan abin da ya masa d'azu ya sosa ran shi sosai, amma sai ya lallashi zuciyar shi ya d'aga dan yaji ko ya canja ra'yi ne zasu fita tare, yana d'agawa ya ji wata muryar daban da bai san ta waye ba, cikin mamaki ya ce,

"Waye kai ina mai wayar?"

"Ranka ya dad'e mai wayar Allah ya masa cikawa,yanzunnan ya samu hatsari da wata babbar mota hakan ya yi sanadiyyar fashewar kan shi nan take sannann qafar shi ta dama ta karye"

Komawa ya yi Saman kujerar da yake kai ya dafe kan shi tare da Kiran Sunan Allah cike da jin tsoron Allah na sake huda naman jiki da b'argon shi ya furta.

"Innalillahi wa inna ilaihirra ji'un"

Itace kalmar da yake maimaitawa a bakin shi,qarar message ne ya maida shi cikin natsuwar shi,cikin tashin hanakali ya duba sai ya ga address ɗin inda Kalla ya yi hatsari aka turo masa, kamar wanda aka ma allurar bacci haka ya miqe ya na jin wani jiri ya na d'iban shi,tafe yake yana fad'in,

" Allah na tuba ka yafeni, Allah ka gafarta min ni Salihu daga yau na yi alqawarin tuba daga zunubaina na daina harkar nan ko zan rasa raina ne"

kuka yake yi sosai kamar zai shid'e a haka ya kai zuwa inda motar shi take ya tada ita ya yi inda aka kwatanta masa, wayar shi ce ta qara ringing ya miqa hannu ya ɗauka,Sunan da ya ga ya na yawo a Saman screen ɗin wayar shi ne ya bashi mamaki ko dai har maganar rasuwar Alhaji kallah ta riske shi ne?

" Oga Zaks"

Shine Sunan da ya karanta a Saman wayar tashi,tsaki ya yi ya d'aga cikin dakiya ya kara a kunnen sa, kafin ya yi magana Oga Zaks ya riga shi,

" Salihu kaji abinda wani ya kira ni yake faɗa min? Kana ina yanzu haka,shin da gaske ne Kalla ya mutu?"

" Ni ma ban sani ba sai na isa wajen na gani, ka kashe wayar na kusa isa ga mutane can dai an taru a wajen sosai"

kashe wayar ya yi ya qarasa,halin da ya ga abokin nashi a ciki ya gigita ƙwaƙwalwa da tunanin shi dan haka nan take ya yanke jiki ya fadi, wasu ne a gefe suka taimaka suka watsa masa ruwa ya farfad'o,da rarrafe ya yi wajen abokin nashi yana kuka, riqe shi mutanen wajen suka yi suna bashi hakuri, umarni ya basu akan su taimaka mai su d'aga gawar akai masallaci mafi kusa a yi masa wanka da sallah a binne shi kawai,dan kuwa basu da kowa balle a ce sai an kai shi gida wajen dangin shi,haka ko aka yi, nan take mutane suka taimaka aka d'aga gawar Alhaji Kalla aka kai wani masallaci da ke kusa,waya ya zaro ya sanar da Oga zaks, jikin Oga zaks ya yi sanyi amma dake zuciyar ta dake ko kuka bai yi ba, sai dai ma kawai ya masa ta'aziyya kawai yace in an kai shi yaje yana son ganin shi, kashe wayar shi ya yi yace,

"Ba dole ma na fita daga wannan muguwar ƙungiyar ba, ai ko ba komai Kalla ya yi wa qungiya hidima ya cancanci azo kan gawar shi a mai addu'a amma wai in an kai shi na je, ko baka ce ba zaka ganni kuwa"

Share hawayen shi ya yi shima yabi bayan yan tsiratun mutanen da suka gama rife Kalla a makwancin shi na gaskiya,mota ya fada ya yi gidan shi, tattaro duk wata dukiya tashi ya yi, yaje ya dakko ATM cards din shi, da makullan motocin shi, da takaddun filaye da gidajen shi da kamfani da komai ya zuba a akwati ya wurga cikin motar shi, ya sa kai dan zuwa gidan Oga zaks,

Haka ya shiga motar shi ya tuqa bai zame a ko ina ba sai qofar gidan Oga Zaks, yana isa a tsaye a ka ya tsaya ma Oga Zaks , cikin bacin rai Oga Zaks ya ce,

"Ya haka Salihu zaka zo ka tsaya min akai kamar wani sanda"

Duk wata dukiya da Alhaji Salihu ya tattaro ya zube ta gaban Oga Zaks cikin haɗe fuska ya ce,
Chapter 49 · 0% Book details