← Book details Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 61

Sashe 60

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baba dan Allah da son Annabin rahama ka yi hakuri ka saurare ni,Baba na san na tafka babban kuskure a rayuwa ta wanda zan mutu ina nadamar aikata shi dan Allah Baba ka yafe min, tabbas na kasance daga cikin jahilai, marasa sanin Allah a baya, sakamakon jahilcin da ya mamayi zuciyata, kuma naqi na nemi sanin Allah da dokokin shi, ina jin girman kai da ganin na wuce na nemi ilmin addini na yi girma da hakan, shiyasa na aikata munanan abubuwa a rayuwata kala-kala waɗanda naga isharar su tun kan aje ko ina, babbar isharar da na fara gani shine mutuwar 'ya ta,sannan na kama dan uwana Yayana da mata ta suna zina, ɗaya 'yar tawa ga ta can da ɗan gaba da fatiha, babbar isharar da ke d'aga min hankali itace rabuwa da Salame da na yi, ta tafi da cikina na rabu da ita rabuwa da ban nuna tausayi da imani a ciki ba,a yanzu nayi nadama, na koma islamiyya ni da iyalina dika, ka yafe min ba dan halaye na ba sai domin Allah"

kalaman shi sun saka jikin baba ya yi sanyi amma sai ya wuce cikin gida kamar bai ji shi ba, yana shiga Mama Bilki ta sauke shi da ruwa da abinci, ga kuma ruwan wanka ta kai mashi bayi,zufa ta hau goge masa tare da jera mishi sannu da zuwa cikin tattausan lafazi, umartar ta ya yi da ta kira yayar tata,miqewa ta yi ta tafi Kiran Goggo, ta na shiga ta tarar da Goggo Sarai ta yi zurfi a cikin tinani har bata san shigar ta d'akin ba ma, yanzu da hankali ke qara shigar ta ba qaramin kunyar Mama Bilki take ji ba akan abubuwan da ta yi mata a baya, saqon Baba Mama Balki ta isar mata ta fita ta fara yin gaba,itama tasowa ta yi kamar wadda kwai ya fashe ma a ciki, ta bi bayan ta ta na shiga ta gansu zaune ita kaɗai ake jira ta samu waje ta zauna ta ce,

" Ga ni baban su"

D'agawa ya yi ya kalle su cikin sha'awar yanda suka koma a nitse ba hayaniya ko mummunan kishi, Ammar ne yaje wajen Goggo Sarai ya zauna a cinyar ta, shafa kanshi ta yi tana mai murmushi, cike da natsuwa Baba ya labar ta masu zuwan Talle da abinda ya sanar da shi, sannan ya tabbatar masu da cewar yanzu haka Tallen na qofar gida, haquri ya bawa Goggo Sarai da ya ga ranta ya baci, ya na juyawa yaga fuskar Mama Bilki ma a b'ace, mijin Salma ko da ba matsafi bane ya cutar da ita a zamantakewar su shima ba qaramin azzalumi bane, kwantar masu da hankali ya yi da dad'ad'an kalamai a hankali suka sauke fushin su, aika Ammar waje ya yi yace yaje ya shigo da baqon nan, cikin tsalle-tsallen yara ya tafi ya sanar da Talle Baba na Kiran shi.

Talle ne ya shiga kai a duqe qafa duk ta sage masa saboda tsaiwa, waje baba ya nuna masa a kan tabarma, tsakiya ga abinci nan da ruwan sha, Goggo Sarai ce ta qaro ruwan sha da ɗan abin motsa baki dangin su cincin ta ajiye musu, ci suka yi suka qoshi, sannan Baba ya kira su baki ɗaya suka zo suka samu kujeru na tsugunne suka zauna kowaccen su sanye cikin hijabi,bayan sun gaisa da Talle ne Baba ya ce,

" To da farko dai zan fara cewa alhamdulillah,dikkan godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai,sannan in sanar da kai dukkanin mu nan iyayen Salma mun yafe maka abinda ka aikata a baya, kuma muna saka ran itama ta yafe maka, tabbas ka cutar mana da yarinya, ka zalunce ta, amma duba da cewar muma masu zunubi ne a wajen Allah kuma mu roqe shi ya yafe mana banga dalilin qin yafe maka da muka yi ba, daga qarshe ina mai sanar maka yanzu haka Salma na Abuja gidan kuɗi gidan hutun dai da take fata da buri a rayuwa ita da yaran ka, dan kuwa biyu ta haifa dika mata,kuma ta samu miji saurayi ya dauki yaran kamar shi ya haife su, ni ba zan sanar da kai ina Salma take ba a yanzu dan ta fara samun farin......."

" Ban katsi nunfashin ka ba baba, amma tabbas nima ba zan so abinda zai hana ta farin ciki ba a dai-dai wannan lokacin, tabbas na amince su ci gaba da rainon yara na a tare ba dan ina gudun d'awainiya ba, lokaci zuwa lokaci zan dinga zuwa nan ɗin dan mu gaisa,ga address d'ina saboda wataran ko za a buqaci hakan,"

Takardar da ya rubuto adireshin sa tun a gida ya zaro ya miqa ma baba, idon shi ya kad'a ya yi jawurr, tabbas har yanzu akwai son Salma a ran shi, wanda a da ya ɗauka sha'awa ce kawai sai yanzu da hankalin shi ya dawo jikin shi ya gane ba hakan bane,miqawa baba ledar hannun shi ya yi ya masu sallama dan komai dare gida yake son ya kwana zaman Kano ba nashi bane, Mama Balki ce ta d'akko hotunan yaran guda uku ta bashi ya riqe ya na kallo hawaye na zuba a idanun shi.

Kaff haife haifen da sauran matan shi suka yi ba wadda ta haifi 'yan biyu, sannan babu mai kyaun wadannan da ya kora tun kafin su zo duniyar, tashi ya yi bayan ya sake yi masu sallama da godiya ya isar da saqon su Huwaila da Marka,godiya suma suka yi masu tare da bada saqon gaisuwa a Kai masu, ya kama hanya ya tafi sai qauyen su.

*BAYAN SHEKARA UKU*

Yau ta kama ranar Asabar ce kowanne ma'aikacin gwamnati ya na gida ya na hutawa da iyalin shi, bangaren 'Ya'yan Alhaji Baballiya kuwa su na can sun tare a Abuja gaba ɗayan su, Suwaibah da Abrar ne suka kai masu zira wanda da kyarrr aka samu Suwaibah ta yarda ta sanya qafafun ta a garin Abuja dan kuwa har a wannan lokacin ba ta jin so da qaunar Abuja a ran ta, Alhaji Salihu kuwa shi ya biya kud'in jirgi suka tafi ya ce idan an gan shi a Abuja to gawar shi ce amma ba dai ya koma mata ba da rayuwar shi da kuma qafafun shi.

A gidan Juwairiyyah duk suka taru, duba da cewa Jabeer shi ne babba sai ta ci wannan girman ake yawan taruwa a gidan ta, hira suke ta sha tare da tuna yarintar su suna dariya ma junan su,wayar saudat ce ta yi qara alamar shigar saqo ta na dubawa ta ga mijin ta ne, murmushi ta yi ta samu wata kujera ta zauna ta na ci gaba da hira jefi-jefi sannan ta na chatting da mijin ta da ke can k'aramin parlour shi da Jabeer da Ibraheem.

Abrar ce ta shiga da mashacin gashi da kibiya ta zauna a jikin Suwaibah ta ce,

"Mom dan Allah ki yi min kalba guda huɗu irin na 'yan biyu ya bani sha'awa"

"Ah toh dai,a ce wai mutum baya son kitso sam a rayuwar shi gashi Allah ya hore masa gashi?"

"Ni dai dan Allah Mom kar ki yi faɗa zan yi kuka"

Gum Suwaibah ta yi da bakin ta ta karɓi kayan kitson ta raba mata kanta huɗu ta fara kitse mata, suna ci gaba da hira.

'Yan biyu ne suka shiga da gudu su na wasa yara sun girma sosai, dika-dika ba za su wuce shekara uku ba, amma iyayin su da maganar su sai mutum ya rantse sun kai shekara huɗu ko biyar,wasa suka hau yi suma Salma na yi masu faɗa akan yanda suke ta rikici,sam ba su zama waje ɗaya ba su yi faɗa ba, sannan kuma ba su iya zama ba tare da junan su ba,Ibraheem ne ya yi sallama ya shiga,bayan sun amsa ne yaran suka nufe shi da gudu suna fad'in,

"Daddy !"

"Na'am yaran Daddy,wa zai je play ground?"

"Niiii, ni daddyna zan je"

In ji Hassana da ta maqale masa wuya tun qarfin ta, Hussaina ce ta janye hannun Hassana a wuyan shi ta ce,

"Dalla sake masa wuya malama kuma Daddy na ne ba naki ba, ke ba ga Mommy can ba ita ce Mommyn ki?"

"Ah ahhh daddy na ne, ko Daddy? Ai dai kai nawa ne ko?"

Yaron da Juwairiyyah ta haifa takwara ga Abbah Balarabe ne ya isa gaban su ya ce,

"Dattyna ne"

Dariya suka sanya a wajen gaba dayan su,har saudat mai latsa waya,Salma ce ta miqe ɗauke da yarinyar ta a hannu ta dungure kan Hassana da ke kukan banza ta ce,

"Na ji kar a so nin, nima ga Faihah nan Allah ya bani in ta girma za ta ce ni Maman ta ce sai me"

Saudat ce ta sauke wayar ta qasa ta ce wa Salma,

"Why are you like zis Maamaa? Are you jealous?"

Dariya suka sake sanyawa, Abrar ta miqe da sauri ta sumbaci kuncin Suwaibah tare da furta mata,

"I love you Mommy sai mun dawo"

"I love you too baby a dawo lafiya"

"Mommy zan siyo maki kayan daɗi "

"Ina nan ina jira my love, kar ku manta a yi addu'a kafin a fita daga gida,ki kuma d'akko hijab ɗin ki ko d'ankwali a rufe kai"

"Toh Mommy bye"

A haka Ibraheem ya kwashe yaran dika suka bar gidan, dan shi ba mai yawan surutu bane, da ya zauna ya na hira da mutane ya gwammace ya yi ta hira da yara,shi yasa Farouq da Jabeer suka fi shaquwa dan kuwa idan suka haɗu suka fara hira kamar ba za su daina ba.

Bayan fitar su ne Juwairiyyah ta miqe ta ce,

"Sisters a shirya tunda yaran sun fita kuma bayin Allah'n can na hira a parlour ku zo mu tafi shopping akwai wasu sabbin abubuwa da nake so mu siyo"

Cike da murna da ihu Saudat ta ajiye wayar ta ta na fad'in,

"Yeeeehhh shopping"

Salma ce ta kalle ta ta ce,

"Kaiii Addah Saudat ke dai ba kya girma you are very childish"

"Yess I am, saboda har yanzu ni kaɗai ce babyn miji na dole na yi abinda na ga dama,wata kuwa an fi son yara akan ta woooo"
Chapter 60 · 0% Book details