Sashe 55
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tin da sassafe angwaye suka jera mota guda huɗu saboda ɗaukan amaren su da wasu kayan nasu,Jabeer ma ya dakko hanya shima amma bai iso ba Innarmu ta zo gidan da sassafe dan a yi komai gaban ta, amare na ta dan koke koken rabuwa da gida na al'ada, Saudat kuwa tsoro ne fal cikin ta na komawa Abuja, ji take yi kamar ta fasa auren amma ta dake, tana son ta yi wa mijin ta kyakkyawan zato, Adda Suwaiba anyi anyi ta yi rakiya tace ita da Abuja ko a film ba ta so taga Ali Nuhu a can balle ita ta sa qafarta a Abuja, haka aka hakura aka barta wataran zata je ne da kan ta, Jabeer ne ya iso nan ya tsaya Shima aka yi sallama da Amare daga nan ya ɗauki matar shi suka wuce gidan iyayen shi dan ya huta gajiyar aiki da ta tuqi.
Bayan tafiyar su ne Hajiya Goggo Sarai mai niyyar zuwa Makka ta na tsaye tana zabga masu addu'a da fatan alkairi,haka ma Baba Baballiya da Mama Bilki ba a bar su a baya ba wajen amsawa da Ameen tare da ɗora tasu addu'ar akan ta ta,kwalla Goggo Sarai ta share na tsoro da tausaya wa yaran nata dan bata san wannan karon me zai faru da su ba, gaba ɗaya son Abuja ya bar ran ta a cewar ta koda Makka za a biya mata ta na rokon kar a ce jirgin su zai tashi ko ya sauka ta Abuja dan akan ya bi ta Abuja sai ta fasa zuwa Makka,Mama Balki ce ta ga yanda take cikin damuwa a hankali ta dafa kafad'ar Goggo Sarai ta ce mata,
" Addu'ar fatan alkairi zaki ci gaba da binsu da ita kamar yanda ki ka fara ,ki daina zurfafa tunani, ki yi masu kyakkyawan zato Yaya,"
" To Bilki Allah ya kai su lafiya, Allah ya zaunar da su lafiya da alkairai maras yankewa"
Amsawa dukkan su suka yi da
" Ameen" suka koma cikin gida.
*****************************
A gidan su Jabeer kuwa ya na can bai samu hutun da ya so ya samu ba ba dan komai ba sai dan tafiya da su Ammar da Abrar da suka yi, dan ma yaran sun shaqu sosai da Suwaibah musamman Abrar, amma ganin Jabeer sai ya sa Abrar maqale masa ta na yi masa rikici, daga qarshe da ya gaji ya tattara su ya kai wa Suwaibah su dan ya huta.
Ko da aka kai wa Suwaibah su nan da nan ta karɓe su Ammar ɗin ta hau yi masu wasa, Ammar ya damu sosai da rashin Adda Calman shi, fitowa Suwaibah ta yi zata deb'o masa dambun naman da ya ragu a kitchen wanda akaiwa amare, tana tashi Abrar ta dinga tsaga kuka kamar ana zare mata rai ita ala dole Suwaibah ba zata tafi ta bar ta ba sai dai su tafi tare,
Jabeer da Juwairiyyah na kwance a parlour sun d'aga labulayen d'akin su dan su sha iska su na hango duk abinda ke faruwa, mamaki ne ya kama Jabeer dan ganin yanda Abrar ke matuqar son Suwaibah, Juwairiyyah ce ta yi murmushi ta ce
"Haka suke fa, in dai Addah Suwaiba na kusa to fa ni na huta,sai mu yini ko nono bata nema ba, sai dai ta yi ta bata kunun ta, idan kuwa na gama bata nono ban mayar da ita wajen Addah Suwaibah ba kuka zata dinga yi min kamar na sato ta"
" Ikon Allah lallai akwai soyayya mai qarfi a tsakanin su,"
Lokacin bacci na yi Suwaibah ta d'akko Abrar dan ta dawo da ita wajen iyayen ta,Ammar kuma zai kwana wajen ta kafin gobe a maida shi gida Shima,tunani ta hau yi,
'Yanzu shikenan idan su Abrar suka koma gida na maida Ammar zan dawo na ci gaba da zama babu d'a babu jika, dama bahaushe ya ce son zuciya ,b'acin ta'
Bayan ta yi sallama Juwairiyyah da ke kwance a jikin Jabeer suna kallo ta miqe ta buɗe qofar ta yi wa Yayar tata izinin shiga ciki, miqa mata Abrar ta yi ta na murmushi sannan ta ce,
"Ga Iya rigima nan ta yi bacci sai da safen ku,"
Murmushi Juwairiyyah ta yi ta ce,
"Iya rigimar gaske, ai wannan kyanta kawai a yaye ta ma dan ba wani shan nono take yi ba da dare"
Da sauri yarinyar ta sake qanqame Suwaibah ta na so ta yi kuka, Jabeer ne ya tashi ya yi dabarar karb'ar ta a hankali sannan suka yi sallama da Suwaibah ta juya dan komawa sashen ta, ta na juyawa hawayen da suka taru a idanun ta suka zuba da qarfi a kuncin ta, zafin su ne ya sanya ta saurin sanya hannu ta share su sannan ta sa hannun ta na dama ta shafa marar ta, hawaye na ci gaba da fita a Idon ta.
Ta na shiga sashen su ta tadda Alhaji Salihu zaune ya miqe qafa ya na jiran dawowar ta,ya na hango ta cikin wannan halin ya tashi cikin hanzari ya isa gareta, rungume ta ya yi dan ya fahimci halin da take ciki, kuka ta saki mai ban tausayi ta ce,
" Yanzu Mine shikenan ba zan haihu ba, d'a ko 'ya ba zasu taba samun mazauni a wannan marar ba? Ya zanyi da son yara dake addabar zuciya ta Mine?"
Kuka shima yake sosai, sai da suka yi ma'ishi sukai shiru dan kan su, sannan Alhaji Salihu ya ce,
" kiyi hakuri ni na jawo maki wannan nakasar, ki gafarta min, nima ina cikin quncin rashin haihuwa,musamman inna kalli yanda Abrar ke son ki take matuqar qaunar ki,ba dan zaluncin da mu ka yi maku ba da na san zaki haifamin yara kyawawa kamar ta, amma na yi mana mugunta ba zamu ga k'wan mu ba a duniya Allah wadaran rayuwata bata da amfani"
Da sauri Suwaibah ta sa hannu ta rufe masa baki ta ce,
"Dan Allah kar ka sake cewa haka Mine, Allah ya albarkaci rayuwar ka Mine, ka ci gaba da gyara kurakuren ka na baya, ka duba ka ga ni fa yanda Allah ya maka albarka a kasuwancin nan, har fili ka siya, nan gaba kadan gida zamu yi na kammu mu koma, mu ci gaba da jin daɗin rayuwar mu, to meye na d'aga hankali har ka na wa kan ka mummunan kalami? Allah ke bada haihuwa fa, kuma ya na bawa duk wanda yaso ne,mu ba zamu yi kuka da Allah akan bai bamu ita ba,saboda mu da kan mu muka yi wa kammu mugunta dan haka hakuri zamu ci gaba da yi,"
Juwairah ce ta koma sashen ta da gudu tana kuka, sai da Suwaibah ta koma sashen ta ta tuna da turaren da ta siya masu da garin kayan qamshin da bata bata nata ba saboda ba su samu zama ba, shi ne dalilin da ya sa ta biyo sahun ta dan ta kawo mata nata sai kuma ta ji duk abinda ke faruwa a tsakanin ma'auratan, kuka take sosai har tana shessheka, wani irin tausayin su ne cike a zuciyar ta, Jabeer gaba daya ya rud'e ya rikice sai ya kama tambayar Juwairiyyah ya na fad'in,
" Babe me ya faru ? Me aka yi maki ki ke kuka haka?.... Ya Allah Sanar dani abinda ke damun ki ko zan iya sama maki kwanciyar hankali, ki sanar dani kome ki ke so na yi miki , kukan ki na d'aga hankalina"
Da sauri ya maida k'wallar Idon shi dake barazanar fitowa saboda rashin son ganin Juwairiyyah a cikin damuwa, cikin shessheqar kuka Juwairiyyah ta ce,
"Sweet one ka taimake ni ka bawa su Adda Suwaibah Abrar"
Maganar ta ta yi matuqar dukan shi,anya ba gamo matar tashi ta yi ba kuwa? Kyautar fa gudan Jinin shi k'walli ɗaya jalli jal take so ya yi? to ta yaya ma zai iya yin kyautar ɗan mutum balle Abrar ɗin shi farin cikin shi? Duba da yanayin damuwa da tashin hankalin da take ciki ne ya sanya shi rungumar ta ya na lallashin ta dan ta dawo hayyacin ta da wuri ta bashi labarin abinda ke faruwa.
Sai da ta nutsu ta daina kukan ne Jabeer ya umarce ta da ta sanar da shi akan wane dalilin zai ba da yarinyar shi guda ɗaya tilo,babu bata lokaci kuwa Juwairiyyah ta yi masa bayanin duk abinda ta ji Suwaibah da mijin ta suna tattaunawa akai cikin kuka batare da ta rage komai ba, shi kanshi Jabeer labarin ya taɓa zuciyar shi sosai,
" Tabbas sun cancanci wannan kyautar daga gare mu,nima Allah ne ya ban ita ai ba ni naba wa kaina ba,dan haka na basu ita halak malak, ko bayan raina Abrar wato Hafsat 'yar su Suwaiba da Salihu ce"
Sai Jabeer ya wani kashe murya dan ya sake sanya ta farin ciki ya ce,
"kinga da mun koma gida sai mu samu qanwa ko qanin Abrar ko? Idan mace ce a sanya mata Sunan Mama Balki idan kuma namiji ne mai rabo ya ɗauka tsakanin Abbah da Baba ko?,"
Yana maganar yana shafa cikin ta yana murmushi,cike da narkewa a jiki shi Juwairiyyah ta ce,
"Ni dai Yah Jabeer anan nake so, sai mu haɗa da addu'a Allah ya sa a dace, ka ga daga gobe ma zaka iya fara kira na da Maman Abbah"
Dariya ta sanya ta kai masa dukan wasa saboda ta bawa kanta da kanta kunya, shi kuwa sai ya goce ta daki iska ya shiga d'aki da gudu ta bishi suka kashe fitila, abinku da makauniya ido sai da gilashi sai na fito na basu waje.