Sashe 27
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A Abuja garin shugaban qasa kuwa Talle ne ya sanya manya kaya har da hula shiga dai ta kamala ya yi ranar ya sanya Salma yin shigar kamala Itama suka shiga sashen uban gidan shi dan ya gabatar da Salma a matsayin iyalin shi, cikin wata murya mai cike da ladabi Talle ya ce,
" Alhj wannan itace mata ta da kuka Karb'a min auren ta a garin kano, dama na dawo da ita nan ne dan na dinga samun kulawa, zama ni ɗayan ba daɗi"
Talle ya fada yana sosa qeya, murmushi uban gidan na shi ya yi sannan yace,
" Allah sarki ai ba damuwa, hakan da ka yi kayi tinani mai kyau,sannan kuma ka kyauta, ina maku fatan alkairi, Allah ya bada zuri'a dayyiba"
" Ameen"
Gaishe shi salma ta yi kanta a qasa tana wasa da gyalen ta,shi kuma ya amsa ba tare da ya kalli in da take ba, kuɗi ya qirgo dubu goma ya bata, yace gashi ta sai wasu abubuwan da take buqata, amsa ta yi hannu na rawa,dan kuwa rabon ta data riqe kuɗi haka ai ta manta, tashi suka yi suka fito, suna isa daki ya miqa mata hannu fuskar nan ba walwala, ita ma ta d'aure tata fuskar ta ce,
"Me zan maka kuma"
Ta karasa maganar ta cikin tsiwa,
" Kee! ni za ki tambaya me zaki min, to in baki san me zaki min ba bari na fada maki, kawo su nan"
Alamun da ta gani na ba wasa yasa ta miqa masa kud'in tana hawayen baqin cikin ganin samu ga rashi a lokaci d'aya, murmushi ya fara yi saboda jin dumus ɗin kuɗi da ya yi,
" Ko ke fa salameme na, yanzu ai kin ga ko dari biyar na baki ai yafi na qattin qauye masu baki dari da hamsin ko"
Juyo wa ta yi cike da bala'i tana kallon shi kuma sai ta fasa yin maganar da ke bakin ta ,wani irin tsoron shi ne kamata saboda yanda yake kallon ta,gani ta yi yana cire kayan shi ya na nufar ta, hankalin ta ne ya tashi dan ko bata shirya ba masa ba har a wannan lokacin ciwon jikin da take fama da shi bai tafi dika ba, gashi shi in ya fara abu bai san ya bari a huta ba, sai ya gajiyar da mutum, kuka ta fara tana fad'in,
"Ni na bar maka ɗari biyar ɗin dan Allah ka bari sai nan da kwana uku, na gaji banda lafiya fa ka sani"
Dariya Talle ya yi sosai ya maida kayan shi, ya kalle ta ya ce,
" Da kyau matar manya matar Ɗan Abuja, ku baku da buqatar kuɗi ai, ni na fita to ga wannan ki leqa waje akwai shago ki siyo kwaki da sugar ki sha, ina jin har canjin gyada zaki samu ma a ciki"
Nera ɗari biyu ya wurga mata ya fice yana wata tafiyar yan duniya a shagide, kuka Salma ta durqusa a wajen tana yi tare da fadin,
"Wai ni ina yan uwana ne, suna can suna jin daɗin su sun manta da rayuwa ta, basu san a halin da nake ciki ba,Oh Allah ka kawo min ɗauki, Allah na tuba, Juwairah kin huta, da baki bi zabin aure irin nawa ba, gani ina cin ubana a garin da na taso da kwadayin yin auren a cikin shi, na manta da neman zaɓin alkhairin Allah a lamura na,wataqila da na nemi zaɓin Allah da ko mummunar jarabawa Allah ba zai haɗa ni da ita ba a Abuja,sai na biye wa son zuciya gashi ina ganin b'acin zuciyar har da gangar jiki na, wayyooo Allah na na shiga uku ni Salma ina zan saka kai na?"
kuka take ta yi mai ban tausayi, yunwar dake cin ta ce ta dawo da ita cikin hayyacin, tashi ta yi ta wanke fuskar ta, ta saka mayafi ta je ta siyo garin ta da sugar da gyada, haɗawa ta yi tana sha tana kuka,ganin duk talaucin su a can gidan iyayen ta ba su shan gari, amma yau gata da gari ba isasshe sugar , share hawayen ta ta yi, ta jingina da katifar su, a haka baccin wuya ya dauke ta.
****************************
Parlour ne na alfarma da ya sha kayan more rayuwa kala da kala, matan biyu masu ji da kyau da nera na zaune su na shan kayan marmari da lemo irin na manyan kwalaben nan mai tsada, saudat ta kalli yayar ta ta da tsabar kwanciyar hankalin da take ciki ya sa ta dan yi qiba kaɗan irin mai ban sha'awar nan ta murje fata sai sheqi take, alamun bata da wata matsala a rayuwar ta, dan gyara zama Saudat ta sake yi a karo na ba adadi sannan ta ce,
"Ni kam Adda Suwaiba ki na tunanin kai ziyara gida kuwa? Ina gani fa ya kamata mu je ganin gida yanzu haka, haba tinda muka zo yau watan mu na takwas kenan fa muna cikin na tara amma bamu taba zuwa gida ba sannan ba a taɓa zuwa mana ba, ga labarin Salma shiru, har yanzu ko waya bamu yi mun ji daga gare ta ba"
Iska Suwaiba ta furzar sannan ta kora jusi ta ajiye glass cup ɗin ta ce,
"Hakane kam ya kamata muje muga ya su Goggo suke, batun Salma ki daina damun kanki tana can suna cin amarcin su a qasar waje da dikkan alama, kin san mijin ta ma ba laifi akwai kudi, wataqila ma basa qasar nan fa"
"Haka ne kuma Allah dai ya jiyar da mu alkairi, amma nikam na tambaye ki mana,"
"Uhumm Ina jin ki"
"Dan Allah baki taɓa zargin komai game da mazan nan namu ba kuwa?"
Ɗan yatsina fuska Suwaiba ta yi sannan ta ce,
"Kamar ya fa?"
Tina wa da ta yi in ta sake Suwaiba ta san me ake ciki kashin su ya bushe, dan haka sai ta yi saurin kauda zancen ta basar tace,
"Ba komai yanzu dai mu tambaye su, yaishe zamu je gida"
" Ba rana balle wata"
Amsar da suka ji kenan ana basu bayan an bude qofa an shigo,cikin haɗe fuska Alhj Ƙalla ya kalli Saudat ya ce,
" Ke tashi mu tafi gida, ai an sada zumuncin haka, ku da kuke son Abuja kamar ran ku in ban manta ba, Saudat kan mu yi aure cewa fa ki kai, in Allah ya baki miji kuka tare a Abuja sai kin shekara biyar baki je ganin gida ba, ko ba ai haka yi ba?"
Cikin qunar rai da kwallar da ta maqale mata tace,
" Anyi haka, amma a da ai ban da isasshen sanin ya Abujan take kuma gani nake zan iya amma ni yanzu gaskiya gidan mu nake son zuwa naga uwata"
Wani hatsabibin kallo ya watsa mata wanda ya sa ba ta san sanda ta durgusa ta dauki jakar ta ba ta yi hanyar fita, sallama ya yi wa abokin shi wanda daga jin warin da suke yi zai sa mutum ya san sai da suka biya suka yi mankasss sannan suka dawo gida.
Nikam nace Saude Allah shi kyauta karki daku yauma.......😂
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 18:
Tabbas gaskiyar mutane ne da suke cewa wani talakan bai iya samun waje ba, da ya samu waje sai ya dinga wulaqanta mutanen da bai kamata ya wulaqanta ba.
Goggo Sarai na daga cikin irin wadannan mutane masu wulaqanta duk wanda suka ga sun fi qumbar susa,rashin iya cin arziqi da baqin ciki ne ya sanya ta bada umarni a gyara iya sashen ta har da ƙara d'aki ɗaya wanda na yi zaton Baba Baballiya ta sa a yi wa shi, amma ga mamaki na sai na ga ta cika shi da kayan alatu ta ce na 'ya'yan ta ne a duk sanda suka sauka a gidan, dan kuwa a yanzu sun girmi zama a d'aki ɗaya da ita suna gogar kafad'un junan su.
Haka ta yi ta gama wulaqancin ta babu wanda ya kula ta a gidan, amma ita gani take gaba ɗaya an saka mata ido a matsayin ta na uwar masu kuɗi.
A yanzu mijin Salma kawai take jira su dawo daga qasar waje a yo mata kabakin arziqi irin na qasar waje.
Ammar ne ke ta wasan shi a tsakar gida ya na tafiya abun shi dugui2, dan ba wai tafiyar ta gama wani kwari bane,tafe yake har ya samu nasarar zuwa wajen randar ruwan Mama Bilki, da dikkan alamu qishirwa yake ji, Mama Bilki kuwa na d'aka tana baccin tsakanin azahar da la'asar.
(Bacci ne da in bawa yayi shi yake samun lada daga wajen Allah)
Ita ko hakima Goggo Sarai ana zaune a ɗaya daga cikin sabbin kujerun da aka sanya mata a d'akin ta ta na kora jus da meatpie, ga mafici a hannun ta irin wanda ake zuge shi dinnan ta kwama uban baqin glass a ido irin na ba mutunci dinnan, Baba Baballiya yau a d'akin ta yake, amma gudun wulaqanci sai dare yake shigowa shi duk ranar girkin ta,kafin tace ita ke ci da gidan ko makamancin haka gwanda ya je ya nemi na kan shi idan ya dawo ya bata duk abinda ya samo sai ya koma qofar gida ya zauna sai dare.
Ammar ne ya dakko cup ya yi ta buqawa a jikin randar a qoqarin sa na son d'iban ruwan ciki ya sha, cikin Fushi Goggo ta sauke qafar ta da ta ɗora ɗaya kan ɗaya ta cire baqin gilashin idanun ta ta qanqance Idon cike da masifa sai ta ga ashe ba randar ta ake bugawa ba ta Mama Balki ce, dariyar qeta ta saki sannan ta ce,
" Yauwa yaro fasa wa uwar taka dan arziqin da ya rage mata ka huta gadon mugun abu kawai"