Sashe 37
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kar ki yi fushi da ni 'Yar qanwata,na jima ina so in sanar da ke ina matuqar jin daɗin yanda ki ke bani girma a gidannan ba dan na girme ki da shekara ba sai dan sanin darajar ɗan uwan ki da kuma mutunta shi da ki ke yi har ta dalilin haka nima ki ke daraja ni,na jima ina mamakin yanda ki ka ajiye duk wata quruciya da yarinta da muka ci ki ke kasa Kiran suna na kai tsaye sai idan kin so tsokana ta, sannan tunda muke baki taɓa yi min abu cikin gadara da isa ba dan ganin ke qanwar miji na ce ki na da 'yanci da iKon yin duk abin da ki ka ga dama a gidan yayan ki,a gaskiya Nafee samuna irin ki sai an tona Allah ya barki da masoyin ki kema ya nuna mana ranar auren ku,Allah ya sa ki samu kwanciyar hankalin da tafi tawa a dangin mijin ki,Allah kuma ya qara mana zumunci ina son ki 'yar uwa ta,maza taho to ki taya ni aikin ki dena Fushi da ni,abinda ya sa ma ban kira ki ba na dauka kina taya Innarmu aiki ne shiyasa ban kira ki ba, tayata aiki ai yafi nawa ko? And dan Allah ki dena fad'ar min da gaba dika dika fa yanzu cikin ya shiga wata takwas"
Murmushi suka yi wa junan su Nafeesa ta ji daɗin maganganun Juwairiyya sai kawai ta nufi inda Juwairiyyah ke yin wanki ta ajiye kayan ta koma ta tattaro sauran 'yan kayan da ba su da wani yawa ta fara wankewa,ranar dai kusan a tare suka ci gaba da aikin su, sallah ce kawai da cin abinci ke tsaida su,Saida ya rage sauran wanke band'aki kawai Juwairiyyah ta deb'i ruwa a bokiti ta ɗauki omo da tokar murhun da ta zuba wa gishiri kaɗan ta matsa lemon tsami ta zuba ruwa akai ta nufi hanyar band'akin.
Nafee na ganin haka ta bi bayan ta ta amshe wankin toilet ɗin, bayan ta kammala ta fito da komai ta ajiye inda ya dace ta kalli Juwairiyyah ta ce,
"Wai nikam me zaki dafa wa Yah Jabeer ne naga baki fara batun girki ba ga shi yamma ta yi"
"Abinda ya fi so zan dafa masa, da kud'in da ya bani kafin ya tafi, jiya na yi aike kasuwa aka siyo min k'wai, nama dankalin turawa, da cabage sai carrot da green beans kin san bani da su a lambu na dama zan iya noma su har su zan saka tinda Yah Jabeer na so a yi girki da su, sai flour ina da mai dama, an siyon yan kayan qamshi da maggi, ɗan wake zan yi mishi mai ajiiiii Hajiyata kin san shi a duniya na kula yana son abunnan"
"Waiiii sosai ma kuwa, baki gan shi bane yana satar danwake a tukunyar Innarmu da sai kin sha dariya, Innarmu in ta kama shi sad'af sad'af take tafiya ta damqe hannun shi ta matse da ludayin tsamar danwaken, shi kuma ya yi ta ihu dan azaba ita kuwa ta qi saki sai ya wahala ta sake shi ta na bin shi da zagin ya na mata satar ɗan wake a tukunya ni da baba mu yi ta musu dariya"
Dariya suka yi tayi sosai dan kuwa Juwairiyya bata taɓa jin labarin ba sai yau, miqewa suka yi suka fara gyara dankalin, suka yanka veges harda na lambun nata da zai tafi da kalar girkin da zata yi,musamman alayyahu da albasa mai ganye, sai da suka yanka komai ta wanke tsaf ruwan jikin su ya tsane sannan ta shiga soya dankalin turawan da ta yi wa yanka a tsaye,sannan ta dakko dafaffen naman ta da ta yanka qanana-qanana ta soya sama-sama ta aje gefe, sannan ta rage man suyar ta dakko jajjagaggen kayan miyar ta, da ta sanya tumatur guda biyu jal ta zuba, ya na tsaka da soyuwa ta zuba kayan qamshi da na dandano,bayan miyar ta soyu ne ta dakko wannan veges din ta zuba, ta bari ya dahu har sai da ruwan jiki ya qame tass sannan ta zuba dankalin ta soyayye da dafaffen k'wai a ciki ta juya ya haɗe jikin shi da kyau.
A gaban Nafeesah ta d'akko flour da wani gari ta zuba kuka ta juya sosai sannan ta fara kwab'a wa da ruwan kanwa, cike da mamaki Nafeen ke bin ta da kallo, cikin tuhuma ta tambayi Juwairiyyah ta ce,
"Wai nikam Matar yayah wannan garin meye ne naga kin zuba a cikin flour ɗin kuma?"
"To Hajiya tambaya an fara tambayar ko, to garin wake ne na niqa da yar dawa kadan sai alabo shine na haɗa da flour din, ɗan wake yafi dad'i sosai idan aka saka su"
" Auuuuhooooo, to ai sai ana yi ana tambaya ko kinga laifina ba gashi yanzu na qaru ba?"
" Ban ga laifin ki ba Hausawa sun ce matambayi baya bata ai"
Hira suka ci gaba da yi ita kuma ta na kwab'in danwaken ta,bata bar kwab'a wa ba har sai da ta ji ya yi laushi sosai sannan ta buɗe tukunya ta ga ruwan ya fara alamun tafasa sai ta fara jefawa qanana, dan yafi son a jefa d'an wake qanana, rufewa ta yi sai da ya tafaso ya yi kamar zai zube ta buɗe marfin ta bari ya ɗan qara dahuwa sai ta kwashe a ruwa Mai kyau daga nan kuma ta tsame shi a mazubin ta mai riqe zafi, ta zuba wa su Innarmu ta bawa Nafeesa.
Nafeesa ta barwa wajen dan ta gyara ita kuma ta dakko nunannen tumatur ta wanke ta raba shi biyu tare da baɗe shi da sugar a tsakiyar shi ta hau goge fuskar ta da shi, nan da nan fuskar ta ta dau kyalli kyan ta ya qara fitowa.
Lalle Juwairiyyah ta deb'o ta zuba masa man kwakwa ta kwab'a shi da ɗan ruwa kaɗan ta dinga bin ko ina na jikin ta ta na murjewa,gaba ɗaya lamarin ta ya gama bawa Nafee mamaki,kasa shiru ta yi sai da ta yi magana,
"Tab a gaskiyar magana Yayah na shan daɗi aradun Allah, yau fa ba ranar gyaran jikin ki bane kamar yanda ki ke tsara abubuwan ki, bama fa ki wani dad'e da yi ba amma ji yanda ki ke faman dirzar fata kin koma kamar wata tauraruwa mai haske da kyau"
" Nafee kenan, ai ita mace ana son in mijin ta ya yi tafiya ko na kwana ɗaya ne ya dawo yaga ta canja kawai ko da sauyin ba yawa, balle kuma Nafee muna magana ne fa akan Yah Jabeer d'ina, My love, my everything"
Dariya suka fashe da ita tare da tafawa,Nafee nata tsokanar ta ta gama ta shiga wanka abun ta ba tare da ta biye wa tsokanar Nafeesan ba.
Ta na fitowa ta tsane jikin ta tare da shafa mayukan ta masu kyau da ta haɗa da kan ta dan gyaran fatar ta sannan ta yi shigar da yake matuqar so, doguwar rigar material ne aka mata irin na masu ciki ma'ana mai faɗi ta yanda ba za ta takura ba,an d'aure hannayen rigar dika ta wuya daga qirjin ta ɗan kama ta kaɗan, cikin nan ta bi ta shafe shi da mai sai kyalli yake gwanin sha'awa,kwalli da powder kawai ta shafa sai man leb'e, wani irin sassanyan qamshi mai ratsa zuciya take fitarwa saboda bata amfani da turare mai karfi.
( kwalli na da matuqar tasiri a idon mace, macen da ta saka kwalli ta kuma iya sarrafa idanun ta ta daban ce)
Dogon hijab ta saka akan kayan ta tada sallar magrib bayan ta idar ne ta zauna ta na azkar a hankali ta fara karanta qur'ani, ana kiran sallar isha'i ta kabbara zata yi sallah kenan Sallamar Jabeer ta daki kunnuwan ta dake buɗe suna jiran su ji muryar shi da ta yi kewa.
Jin shiru bata je tarbon shi bane ya sanya Jabeer leqawa parlour ganin tana sallah ne ya sanya shi ajiye kayan shi a cikin palourn ya tafi ya d'aura alwala shima ya tafi masallaci.
Ta jima ta na gode wa Allah da ya dawo mata da mijin ta lafiya qalou kafin ta yi tahiya ta Sallame sallar ta, ninke hijabin ta take yi bakin ta na tasbihi ga Allah ta shiga d'aki ta dan sake shafa humra da powder sannan ta hau kallon kanta a madubi, murmushi ta yi wa kan ta kafin ta koma parlour, ɗauke kayan da ya dawo da su ta yi ta hau dubawa nan take ta hau ware komai ta na ajiye wa a mahallin da ya dace da shi,hatta da kayan wankin da ya dawo da su sai da ta yi masu mazauni sannan ta dawo ta ɗauke wata leda da bata buɗe ta ga meye a ciki ba ta kai ta ajiye.
Ruwan wanka ta haɗa masa mai d'umi, fitowar ta kenan ta shiga parlour kafin ta kai ga zama Jabeer ya sallama ya kulle sashen nasu, kafin ya gama karanta ayatul kursiyyun a qofar gidan ta tashi da sauri ta na dariya qasa qasa ta b'oye a bayan qofa.
Shigowa jabeer ya yi bakin shi ɗauke da sallama fuskar shi cike da annuri saboda ganin gidan qal fiye da yanda ya saba ganin shi,cikin murmushi ya hau dube -dube alamun neman ta yake, gajiya ya yi da tsayuwar ya kama qugun shi ya ce,
" Juwaireren Mama ko ki fito ko na zauna a qasa na yi ta maki kukan wahal da idanu da ruhi na da ki ke yi, dan na kula da alama baki son gani na ni kaɗai ne na yi kewar ki"