Sashe 21
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gidan Talle kuwa cikin dare Salma ta ji kamar buga qofa ake yi,dan haka a hankali ta miqe ba tare da ta yi wanai kwakkwaran motsi ba, dan tare suke kwana da Haule yanzu, leqawa tayi ta qaramar bular jikin qofar d'akin nata,ta bular ta hango Yayan mijin nasu na waige2 yana kwankwasa qofar Marka, mamaki ne fall cikin ta na me ya kawo shi d'akin Marka da tsohon daren nan, dan kuwa duk yan kwanakin nan marka ke zuwa wajen shi, yau fushi take yi da shi shi yasa ya biyo sahu, saboda daren jiya ya hana ta dari da hamsin da ta roqa yace bai da su, shine tace yau ba za ta ba, shi kuma gashi a mugun matse yake,jikin shi har wata rawa yake sanda yake kwankwasa qofar, budewa ta yi tana magana qasa2 ta ce,
" Dalla can sai ka tada yaran ma sun gan ka, ni shigo kayi ka gama ka tafi jarababbe kawai"
Jan shi ciki ta yi su ka rufe qofar, aiko akan idon salma, kame baki salma ta yi tana fadin,
"Tab ashe wannan matar munafuka ce? Ba ta da maqiyi da rana da ya wuce Baban Bangis,amma kuma ashe da dare bata da masoyin da ya wuce Baban bangis, lallai ran da Su Badamasin suka sani akwai case a gidan nan ko kuma idan Talle ya ji labari"
Tana cikin wannan tinanin ta fara jiyo qarar dan qaramin gadon na Marka irin na qarfen nan, sannan ga sambatun ta nan da bata iya shiru ita sai ta tona masu asiri, yaran akwai nauyin baccin tsiya shi yasa ma basu san wainar da ake toya wa ba, to an wuni shiririta kuma anyi bacci late dole in sun kwanta su zama kamar gawwaki Marka a wayon ta hade yaran take dika daki daya saboda irin haka, kafin Salma ta zo ne d'akin tan yake na Yammatan, amma kawo ta yasa aka haɗe su waje ɗaya maza da matan,motsin qofa Salma ta ji Baban Bangis zai fito sai da ya fito Marka ta biyo shi tana miqa masa hannu ta na wani gantsaro girji, shi kuma yana qara shafawa, ya ce,
" kamar na koma mu yi ta yi sai asuba na tafi"
"Lallai ma Yaya kaima a gaida ka, duk wannan aikin da garar da ka diba bai ishe ka ba, in kana son ka koma ciki qaron nera dari kacal"
Murmushi ya yi haqoran shi jajaye suka bayyana ya ce,
" Aaaa dari tab na gama baki dari ukun yau, ni dai gaskiya ban da su"
"To kuwa kama gaban ka ka wuce ya ishe ka haka a barwa gobe"
Yana qarasa fitowa gaba daya Salma ta fito da buta a hannu ita ma , hankalin su ne ya tashi gaba ɗaya da ganin ta tsaye ta na murmushi ta na bin su da wani shu'umin kallo,jiki na rawa baki na karkarwa su Marka suka zube a Saman guiwowin su suna roqon Salma,
" Salame dan Allah ki rufa mana asiri, kar kowa yaji labarin nan"
Cikin Isa da gadara Salma ta ce,
" Anawa zan yi shirun ko ko haka nan zan rufe bakin nawa kuke nufin baku ban ko sisi ba tunda ke na ji ɗari uku ma aka baki"
Jiki na rawa Baban Bangis ya sa hannu a aljihun shi ya dakko dari biyar guda biyu ya miqa wa Salma ,
"Ke ma ina naki kud'in?"
Da sauri Marka ta shiga d'akin ta ta d'akko dari biyar ta haɗa dana hanun ta ta bawa Salma, "
Kallon su ta yi ta na juya kud'in ta ce wa Marka,
"Marka ina son ki sani Talle ya kusan dawo wa dan jiya baki nan kina yawon ta zubar Badamasi ya faɗa sun yi waya ya ce zai dawo nan ba da jimawa ba, in ya dawo kika kuskura na ganku tare har kika haɗa wannan qazamin jikin baki da shi warin ki ya mannu a jikin shi saina faɗa masa, dan ba zaki sa yanda ni na tsare aure na ba ina juran ya dawo mu raya sunna ki ja min amai kuma ba biyan buqata, kinji ni ko baki ji ba?"
Wani yawu Marka ta had'iya na yau ta shiga uku an raba ta da gwarzon maza Talle, sannan a hankali tace,
"Na gane kiyi wa Allah ki rufa mana asiri"
" Baku da matsala in ma komawa zaku yi sai asuba din zan iya yi maku gadi"
Da sauri suka furta,
"Aaaaa tafiya zai yi/zan yi"
Fakam fakam Yayan Talle ya bar sashen nasu, ita kuma salma ta koma d'akin ta ta bar Marka da cizon yatsan an amshe yan kudaden ta kuma gashi ba wai ta wani samu biyan buqatar ta bane, yau ta yi biyu babu, tura qofar ta ta yi ta koma dakin ta.
Salma na shiga d'aki ta datse qofar ta zauna ta dinga babbaka dariya, a ranta ta na ayyana,
'Shikenan yanzu sun dawo hannun na sai yanda na yi da su'
Shikenan yanzu da ta ji tana son kuɗi zata neme su kuma dole su bayar ko ta tona masu asiri, cikin murna ta dale gadon ta ta miqe.
****************************
Yau garin na Kano an tashi da ni'ima sakamakon sanyi da ya ɗan fara shiga, garin ya yi daɗi ya yi kyau gwanin sha'awa,rana ta yi sanyi babu kuma zafi.
Shamsiyya qawar su Juwairah da Nafee ce ta kawo ma Juwairah ziyara ta musamman dan tana son ta qara bata wasu shawarwarin game da yanda zata gyara nonon ta da suka lamushe kamar an yi gobara ta ciki an yashe komai sai fata, sannan ga kanta dake yawan karyewa gashin ta na zuba, bangare ɗaya kuma abu mafi mahimmanci da zai kaita ta taya su murna dan Nafeesa ta bata labarin samun cinkin da ta yi, murna take yi sosai itama da jin hakan.
Shiryawa ta yi bayan ta gyara gidan ta tsaf kamar ba ita ba ta fito ta hau abin hawa ya kai ta har gidan su Juwairah da Nafeesa bayan ta sauka ta sallami mai adaidaita sahun ne ta shiga ciki, bangaren innar mu ta fara shiga ta gaishe ta, bayan sun gaisa ne ta mata murnar abun alkhairin da ya same su sannan ta shiga ciki wajen Juwairah, a can ta hango Nafeesa tana alwalar la'asar, Juwairah na d'aka tana gabatar da tata sallahr.........
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
page 15:
Ranar litinin da safe ne su Suwaiba da Saudat suka shirya tsaf dan zuwa asibiti su ga meke faruwa har yanzu ba su samu ciki ba balle a kai ga sa ran haihuwa, shiga suka yi ta alfarma sai walwali suke da ka gan su ka ga matan manya.
Qarya suka yi wa mazajen nasu suka sanar da su zasu tafi shoping ne, Dunes Supermarket suka nufa cikin isa da qasaita irin ta isassu kuma hamshaqan mata, Alhj Salihu ne ya biyo su a b'oye dan ya tabbatar da ina zasu je, ganin sun isa super market ne da gasken ya sa hankalin shi kwanciya sai ya kira ya Alhj Kalla ya sanar da shi cewar da gaske shoping suka tafi, Suwaiba ta kula da binna ta da yake yi duk kuwa da qoqarin boyewar da ya yi ta yi kar ta gan shi,wannan shine dalilin da ya sa ta ce ma driver ya kai ta can super market ɗin a hanya ta yi wa Saudat message akan su tafi can din daga baya sun san shawarar da za su yanke.
Bayan sun isa ne suka fito a motocin su suka shiga super market su a dole siyayya za su yi,suna shiga suka hau waige Saida suka tabbatar ba direbobin su ba su gani su cikin sauri suka fita ta wata qofar suka samu taxi suka ce ta kai su asibiti mafi kusa,nan take kuwa aka kai su wani private hospital dake kusa,bayan gwaje gwaje da aka yi masu a tashin farko likitar ta gane ai ba ma mahaifa a tattare da su an cire ta.
Sanda ta sanar da su suwaiba hauka ne kawai ba su yi ba saboda tsananin damuwa da shiga tashin hankali, kuka suka saka sosai kamar an masu duka, jikin Saudat sai rawa yake dan ta fi Suwaiba son yara,ita Suwaiba dama ita ba wai ta wani damu da su ba ne, amma kasancewar yanzu ta ji bata da mahaifa kwata2 hankalin ta ya dagu sosai, tashi sukai bayan sun gama biyan komai suka dawo supermarket din suka debi wasu daga abubuwan da suke buqata musamman na gyaran jiki, Suwaiba kuwa acici kayan kwalam da maqulashe ta jida sannan suka je suka biya kud'in aka zuba masu kayan su a leda,jerawa suka yi su na tafe suna magana,suwaiba ce ta ja hancin ta sannan ta ce wa Saudat,
" Da mu zauna ba mahaifa ba kayan more rayuwa ai gwanda mu kwashi rabon mu muci tin da bamu da magada"
Fadin hakan ke da wuya sai Saudat ta saka kuka har ta na shassheqar kuka, cikin faɗa Suwaiba ta ce,
" Malama kar ki taran jama'a, meye na kukan kuma a cikin mutane, daga cewa mu more rayuwar mu,an fa tabbatar mana da ba za mu haihu ba,to in dai haka ne me zan haihu ba zamu more rayuwar mu ba? Ki fa duba ki gani ba mahaifa ba haihuwa ba kuɗi,to haka ki ke so mu zauna cikin wahala? Sanin kan ki ne ma mazajen mu suka san bama haihuwa mun shiga uku, in gaba suka so qara auren su za su yi, ba gwanda mu ware ba mu saki ran mu mu tatsi abinda muka tatsa, tin da mun taba zaman Abujan mun ji abinda ke cikin ta, kinga sai mu canja sheqa da uwar kud'in mu wa ya isa ya taka mu?"