Sashe 22
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gyada kai Saudat take ta yi kamar wata qadangaruwa, ta fahimci suwaiba Sarai,kawai ta na wani tunani ne na wannan zancen rashin mahaifar tasu abu kamar na had'in baki ace basu da mahaifa iya da yar uwar ta ? Anya babu wata a qasa kuwa? Lallai ba zata huta ba kuwa sai ta binciko ta san mene dalilin da ya sa suka rasa mahaifa a lokaci d'aya da yayar ta bayan ta san ko a da da suka yi yawon su ba su taɓa yunqurin zubar da ciki bama balle cire mahaifa, suna gama tattauna wa a tsaye nesa da drivers ɗin su suka yi sallama da juna suka koma gidajen su.
*************************
Yau fa gidan Talle shar da shi domin ta shi kawai suka i suka ga Salma na bada umar ni ko ta ina kuma Marka bata ce komai ba,ta ɗauki ido ta zuba mata ba ta uhuummm ba kuma ta ah ah.
Tun da ta ga yara sun tashi daga bacci ta sa masu hankalin a gaba sai da suka gyara d'akunan baccin su ta na yi ta na masifa kamar yanda ta ga Markar na yi,daga nan ta ware manyan ta sanya su shara nan suka haɗu suka share gidan tsaf,daga nan ta sa aka deb'o toka a murhu aka cika a shaddar gidan aka kwab'a wata da omo aka wanke bayin nasu tasss.
Kiran kowa ta dinga yi da Sunan shi ta na bada umarni kowa ya d'akko wankin shi,nan fa suka fara fito da wanki tsibi tsibi kamar a gidan wankau,ta na zaune a qofar d'akin ta tana kallon yanda 'yan matan ke kallon Marka suna jiran su ji ta tsawatar amma shiru, ga wani uban kwarjini da Salma ta yi masu ko rashin kunyar ma sun kasa yi mata,da kudin da ta Karb'a a wajen su Marka a daren jiyan da shi aka siyo sabulun wankin, bayan sun gama wanki ne Salma ta sa su a gaba Saida kowaccen su ta yi wanka.
Abun nasu sai ya zama gwanin sha'awa gidan ya yi fes da shi yaran ma sun yi acan acan,sai da Salma ta tabbatar kowa ya yi fesss sannan Itama ta shiga ta fesa wannan ta ta fito ta shirya tsaff cikin kwalliya,ganin haka ne ya sanya Marka leqa Salma da ta ke dakin ta ta na huce gajiya, dan kuwa ta bada kuɗi a siyo kayan miya a yi girki,Saida Marka ta tabbata ba za ta fito da wuri ba ta deb'i ruwa a bokiti Itama ta je ta yi wanka,ita da kan ta sai ta ji iska na ratsa ta.
ko da ta gama shirya wa Itama sai ta bi lafiyar gado dan ta dan matse ido kafin a yi girki,kwanciyar ta ke da wuya Huwaila da Jummala suka shiga dakin mamar su ta da ya sha gyara suka hau tambayar ta wai me ke faruwa ne yau a gidan ko dai asiri salame ta yi mata ne? Marka ce ta kalli hanyar kofar d'akin ta ta gyad'a kai tare da fad'in,
" Um Um Um Um Um"
Wannan kalmar kawai take ta maimaitawa tana kama bakin ta, alamar su yi shiru maganar babbace , kame bakin nasu ko suka yi ba su qara tambaya ba dan sun san wacece Marka duk abinda zai ta tashiga hankalin ta haka ba qarami bane,Marka ko cikin zuciyar ta cewa take,
'Yarinya ni ce fa uwar shed'anu, ki gama wannan mulkin naki na yan kwanaki, kiga abinda zai faru dake nan gaba kaɗan, dani kk zancen'
Da yamma sakaliya suka ji qarar motar Talle,yaran fita suka yi da gudu dan tarbon Baban nasu, Huwaila na can Ita da Baban gida a wani lungu na gidan suna sana'ar tasu, su ka ji qarar motar Tallen, a firgice suka saki juna suka yi hanyar fita daga lungun kowa na zare Idonu.
Talle kenan mai gayya mai aiki shine ya dawo gidan nashi bayan tsahon lokaci, Salma na jin haka ta miqe tana rangwada ta je ta taro shi, dawowa suka yi cikin yaran yaran nata gaida shi yana amsawa.
D'akin Marka ya leqa ya ganta ta yi wanka dakinnan fes kamar ba shi ba, wata uwar dariya Talle ya saki sannan ya ce,
" Hajiya Marka, Markar Talle ,Marka Ikon Allah, wato ganin Kyakkyawar amarya ta ne ya nutsar dake har ki ke wanke da gyara gida, yo ni dana san haka ne ai dana dawo da jimawa, da ban tsaya wajen qadangarun bariki suna amshen 'yan kud'ad'e na ba,"
Qafar sa ɗaya ya d'aga zai shiga d'akin na Marka Salma ta koma ta tsaya a bayan shi tana kallon Marka da wani irin mugun kallon ya na shiga zan tona maki asiri, da sauri Marka ta miqe ta ja baya ta na fad'in,
" Aa Talle in ka zauna d'akin nan ba ai wa yarinyar can adalci ba kuma, wancan karon ai a wajena ka fara zama ina ganin wannan karon wajen ta zaka fara zuwa"
Tsantsar mamakin Marka ne ya kama Talle har ya sa shi sake baki ya na kallon ta, qarasa ya yi wajen ta ya taɓa wuyan ta dan ya ji anya lafiyar ta qalaou kuwa? Jin ta ya yi daidai ba alamun zafin jiki ko wata lalura,girgiza kai ya yi ya na tsananin mamakin sauyawar da Marka ta yi
kad'a kai Talle ya yi sannan ya juya ya nufi d'akin Salma dan tana ma Marka kallon nan ta juya ta bar wajen,hira ya dinga yi mata da ba wani ganewa ta ke yi ba, dan gaba ɗayan shi tsami yake yi kamar wanda ya yi aikin qarfi kafin ya dawo.
Dabara ce ta fad'o mata tashi ta yi ta na yanga ta fita, shi kuwa Talle wata shashashar dariya ya sake ya na bin mazaunan ta da kallo, ta na fita ta ɗauki bokiti ta zuba ruwa a bokiti babba, ta koma d'akin ta dakko brush guda biyu ta saka toothpast a jiki ta je kusa da shi zuciyar ta na tashi amma ta jure ta zauna a cinyar shi tana shafa shi ta ce,
" Babe taso mu je mu yi wanka magariba na yi, kaga in munyi sai mu yi sallah ka zo na yi maka tausa dan da alama ka gaji sosai"
Gyada kai ya dinga yi kamar qadangare ya daga ta yana son ya dauke ta, da sauri ta sauka dan in ya sata a kafadar nan tashi sai ta yi aman hanji ta tasss saboda tsamin zufar da yake yi,cikin kirsa ta ke masa nuni da yara, kawai ya je ya fara shiga zata biyo shi ta masa wankan daga baya, tafiya ya yi yana washe baki, rabon da a masa irin haka tin tana amarya a cikin garin Abuja.
Ai kuwa da Salma ta samu dama ta kora yara Mazan su tafi masallaci,matan kuma a shiga a yi sallah sai tayi wuff ta faɗa band'akin,wanka ta masa sosai, ta bashi brush ya wanke bakinnan fes,sai ga Talle an yi shar, shima kar ba ya yi ya mata wankan ta wanke bakin ta, ta fara leqawa taga ba yaran maza 'yan matan na d'aki suna hira da Marka sai ta fito, daga baya shima ya biyo ta dakin, shirya shi ta yi tace ya yi alwala ya je masjid, amma sai Talle ya buɗe baki cikin b'ata fuska ya ce,
"Ka ji min yarinya da ke kike sani na yi sallar? To banga dama ba haɗawa zan da isha'i in na gama abinda zan yi"
Cikin kwantar da kai Salma ta ce wa Talle,
" Ah ah ba ni nake saka ka ba Allah ya baka hakuri, ni so nake dama kayi da wuri saboda in na zo maka tausar nan bana son abinda zai sa na tsaya ne ka ga idan baka yi sallahr ba dole ana tsaka da tausa ka ce na tsaya ka je ka yi sallahr shi yasa na ke baka shawarar ka yi yinsa wuri amma tinda baka so kwanta na yi maka tausa"
Cikin yauqi da kwarkwasa ta qarasa maganar ta,tini Talle ya washe baki kamar dolo, miqewa ya yi zai tafi masjid, yajiyo maganar ta tana fad'in,
" Babe in ka je ka jira ayi isha'i kawai ka ga in ka shigo sai asuba zamu sarara ko ya kace"
Ta qarasa ta na kashe masa ido ɗaya, wata dariya Talle ya saki kamar wawa ya ce,
" Maganar ki dutse sweety na se na dawo"
Koda ya isa masallacin har an yi magariba makararru ya samu aka ja su jam'i suka yi sallar,lokacin isha'i na yi aka kira sallah aka tada sallah,ana idarwa kuwa Talle ya miqe ya koma gida,tafe yake cikin sauri fakam fakam ya qarasa tsakiyar gidan nashi,Marka ya yi wa sallama ya faɗa dakin Salma wadda ya tadda ta sha gayu sosai da yan kayan da take da su, ta dan fesa turaren ta da ya kusa qarewa dan kale ma take yi, yana shiga d'aga sama Talle ya yi yana juyi da ita,ita ko sai dariya take yi, sumbatar ta ya fara aika mata da shi tana mayat mashi da martani, suna tsaka da wasannin su ya katse ta ya ce,
"Ni fa yunwa nake ji, mu fara cin abinci kannan yarannan sun yi bacci sai mu dora daga inda muka tsaya, dan yau kam sai yanda hali ya yi,"
Cikin jin daɗi Salma ta saki dariyar murna,a haka ta tafi ta dakko masu abinci suna ci suna hira Salma cikin shagwab'a ta ce,
" Babe me yasa ka amshen waya ta ne, tinda nazo yanzu kusan wata bakwai da wasu kwanaki ban ji muryar kowa nawa ba"
Wani mugun kallo Talle ya buga mata daya sa cikin ta kad'awa, dan dai Tallen Tallen ne fa kar ta ga ya na biye mata ta kawo masa raini, sunkuyar da kan ta ta yi qasa cikin kwantar da kai tace,
" Ka yi hakuri ba zan sake zancen ba dama na yi kewar Goggo da Baba ne"