Sashe 3
Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari Juwaiirah ce zaune saman sallaya da goshin asuba ta na ta ibada, kamar wata babbar mata, Maman ta ta saba mata da tashin dare, dan ta sanar da ita cewar duk abinda bawa ke so ya roqi Allah da ikhlasi da yaqinin Allah zai biya masa buqatar shi to fa ba makawa Allah zai biya masa buqatar shi musamman in bawan nan ya yi addu'ar a lokutan karbar addu'a, wanda qarfe uku zuwa asuba ko huɗu zuwa asuba Allah na amsa addu'ar bayin shi dan lokaci ne mai mahimmanci ga bayin Allah, sannan ba a son mutum mumini ya zage ya dinga kwasar bacci daga farkon dare har zuwa qarshen dare ba tare da ya farka ya yi nafila ko da raka'a biyu bane,mu ke da buqata a wajen Allah Allah ba shi da buqatar mu, ya na daga cikin cikar imanin mutum ya dinga rokar Allah ya bashi ikon ganawa da shi a cikin dare ko da ya na jin kiwar yin hakan da kan kan shi ,to sai Allah ya bashi ikon tashi ɗin.
Hannu ta daga sama cikin qasqantar da kan ta a gaban mahaliccin ta ta ce,
" Ya Allah kai ne masanin abin da ke zuciya ta Allah ka biya min dikkan buqatu na na alkairi Ka sa Yaya Jabeer ya zama shine mafi alkairi a rayuwa ta duniya da lahira....."
Wannan addu'ar ce tafi daukan hankali na, nace tooooo waye kuma Yaya Jabeer? Addu'ar ta ta ci gaba bayan ta gama ta yi wa iyayen ta da yan uwan ta da dikkan muslmi, bayan ta idar ne ta hau karanta Qur'ani da zazzaqar muryar ta, har aka kira sallah ta gabatar da sallar asuba ta dora da azkar da karatu har gari ya waye, a sannan ne ta samu ta dan koma bacci zuwa qarfe takwas ta tashi, ta fara taya Maman ta aiki, bayan ta gama gyara gidan dan ba su ke girki ba balle ta taya ta aikin girki, wanka ta shiga ta fito,haka nan taji tana son yin kwalliya yau dan ita ba ma'abociyar yin kwalliya bane a koda yaushe,sai lokaci lokaci ta kan dan taɓa ,ta na gama sheqa kwalliyar ta me kyau ta buɗe akwatin ta ta dakko wata rigar ta doguwa ta atampa ,rigar na da fadi ta qasa ta sama kuma an dan tsuke ta da dogon hannu ,jujjuya rigar ta yi ta kara ta a jikin ta kafin daga baya cikin murmushi ta saka rigar,yanda rigar ta zauna mata abin kallo ne domin Juwairah akwai shape mai kyau, gyara gashin kanta ta yi da kyar dan yawan shi da tsahon shi ke wahal da ita wajen kula da shi, bayan ta gama ne ta kafa dauri me kyau, ta samu tiraren ta da Mama ta bata ta fesa, tana gamawa ta je wajen Maman ta ta na wani yanga ta na nuna mata yau fa Allah ya yarda 'yar ta ta yi kwalliya, ta duqa zata dau Ammar, cikin tsokana irin na tsakanin 'ya da uwar da suka shaqu da juna Mama ta ce,
" A'a kaga Juwairere saraunuyar mata,Juwairere diyar Mamanta gaye ne aka sha haka yau, to ko dai suruki na ne zai zo?"
Cike da shagwaba da nuna jin kunyar Maman nata Juwairiyyah ta ce,
"Haba Mama wanne irin suruki kuma,kawai dai na yi sha'awar na yi kwalliya ne yau, kuma ni mama na ce maki bana son Juwairere Allah dariya qawayena suke min in suka zo sukaji kina fada musamman Nafeesa"
Cikin 'yar dariya Mama ta ce,
"To in banda abinki Nafi ai qanwar ki ce kin fa bata kwana bakwai masu kyau dan haka data tsokane ki sai ki yi murmushi irin na manyan yayu saboda yarinta ce ba wani abu ba"
Dariya suka saka a tare, sosai suke dariya abun su gwanin sha'awa,Goggo Sarai ce ta ja dogon tsaki ta ci gaba da aikin ta,a tunanin ta Mama Balkin na tsokanar ta ne kawai su na yi ne dan su bata haushi , ba tare da sun ji sallama ba Juwairiyyah ta ji an kama hancin ta, muryar da ta ke tsakanin buri da muradin ji ce ta ce mata,
"Wannan dariyar taku Mama ba zata bari kuji komai ba , musamman wannan Juwaireren da ta buɗe wannan qaramin bakin nata take cika wa mutane gida da qara da wata Muryar ta se kace ta kanari"
Tsalle ta soma yi na murnar ganin Yayan nata sannan ta kama hannayen shi dika biyun a nata ta na kallon kyakkyawar fuskar shi da ta yi kewa ta ce,
" Yayana, wayyo Yayana kaine da gaske? I missed u so much Yayana, yaushe ka dawo? "
" Oh Juwaiiraah ko zama bai yi ba fa wannan zumud'i da tambayoyi a bari ya ɗan zauna ya huta mana"
"Mama rabu da ita nima ba qaramin Missing din Juwairere na na yi ba, ban ga laifin ta ba dan ta nuna murnar ta na gani na"
Murmushi Mama ta yi sannan ta fita d'ebo masa ɗan ruwa ya sha dan gidan haka suka tashi ko na karyawa ba a miqo masu ba, jawo ta ya yi kusa da shi sannan ya ce,
" Amma da Juwairere kin san na hana kwalliya ko?what if wani ya zo ya gan min kwalliyar mata ta? Ko a aike ki a haka kowa ya kallen min ke? A gaskiya ni dai bana so, ba wannan ba ma dai yanzu ai ta qare tinda ga angon ki nan ya gani kuma ya yaba kwalliya ta yi dari bisa dari"
Duqar da kan ta ta yi qasa wata iriyar murna da farin ciki na ratsa ta tunda ta ji ya kira kanshi angon ta, ga hannun ta da yake murzawa a hankali, karɓe hannun ta ta yi ta canja mazauni tana turo baki, ita a dole fushi ta fara,Mama ce ta shigo ɗauke da kofi a hannun ta ta aje masa a gaban shi ta samu wajen zama,
" Mama kin ga wannan yar rigimar ta turo baki, lallai akwai magana a cikin shi"
" A'a ni kam ba ruwana ina gefe ba a shiga tsakanin ku ai ku se mutum ya ji kunya"
komawa ya yi kusa da ita ya d'ago kanta ya na kallon kyakkyawar fuskar ta da ya ke jin zai iya shekara ya na kallon ta ba tare da ya gaji ba,
"Juwairere na me ya faru?"
Cikin 'yar kwallar da ta daddage ta taro a idon ta da ya sha kwalli ta ce,
"To ba ga shi nan ba wai Juwairere, ni Allah bana son sunan nan,gaba ɗaya kun sa Nafee na tsokana ta, Kullum ta ganni sai ta hau ce man Juwairere "
Ta qarasa maganar 'yar kwallar ta na qarasa sauka a kuncin ta bakin nan a gaba, dariya ta bashi ba kadan ba wauta da shagwabar ta na burge shi sosai
"Ki kwantar da hankalin ki princess ba zan qara faɗa ba inshaa Allah sai munyi aure"
Hararar wasa ta masa tare da jin kunyar kalmar aure da ya ce, sai kawai ta miqe ta fita a dakin da gudu tai tsakar gid tana dariya, kad'a kai Mama ta yi sannan tace
"Ni Allah dariya kuke bani yaran nan, kun iya wauta da yawa"
Cikin wata iriyar murya jabeer ya ce,
" Mama kenan ba wauta bane da gaske auren ta nake son yi, amma idan Baba zai ban ita, ko ita ɗin ma Abuja za a kai ta? Dan na ji an maida sunan gidan nan wai gidan 'YAN ABUJA saboda yaran gidan a Abuja suke son yin aure su kalar Abuja ne, ina jin haka hankali na ya tashi ina fatan Allah ya sa ba Juwairere na a cikin wannan haukan, dalilin zuwana kenan Mama wato na yad'a manufa ta na son auren Juwairiyyah, na ji a wajen Innar mu wai har an kawo kuɗin Auren wadan can marasa kunyar"
"Hhmmm haka ne Jabeer amma kasan ni ba ruwana da wannan kalmar ta 'YAN ABUJA ko? Duk inda mijin Juwairiyyah yake ina fatan ya kasance miji na gari mai addini wanda zai riqe min ita da amana ,kuma wannan magana ta Abuja su da kan su yaran gidan nan duka qirqirar wa kan su ita wai su YAN ABUJA NE ba zasu auri kowa ba sai ɗan can, in su suna faɗa kuma sun yarda zasu aure su ni ban faɗa ba, kuma ban ba 'yata izinin kiran kanta da 'YAR ABUJA ba , in da rabon can ne gidan auren ta yake Allah ya zab'a mafi alkairi in ba can bane ni ko ina albarka na ke nema mata kullum"
" Haka ne Mama, Allah ya shige mana gaba"
"Ameeén ya Allah Jabeer"
Jabeer dan gidan Yaya Balarabe ne ya dawo daga bautar qasa inda aka tura shi illorin, ya kammala karatin shi bangaren kasuwanci, to a yanzu haka yana taɓa saida jakunkuna da takalma, ba wani arziqi ne da shi ba, yayun ta sun so matuqa ace me kuɗi ne da sun aure shi ko dan kyawun shi, amma inaaaa talauci a cewar su ya dakushe tauraruwar shi.
A yan kwanakin nan kusan kullum sai ya zo gidan su Juwairiyyah ,ga saurayin Salma mai baqin naci shima kullum ya na tafe, shi ma d'an Abuja ne ya na sana'ar saida motoci, kullum in zai zo zance se ku ga ya baza uwar riga ya shigo mota mai tsada ya zo amma fa baya bata ko sisi, wataran ne ma zai dan samu ya siyo mata yar shawarma kamar mayya tana rawar kai saurayi ya siyo mata abu ta amshe ta shigo gida,itama tini ta bi sahun manyan ta amsar kudin maza da basu jiki ai tabe2 , Alhajin da ke son ta shima in yazo zancen haka yake gama lalube ta ya yi gaba abun shi.........
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 YAN ABUJA. 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 3: