← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 71

Sashe 68

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  *SAFIYA*

Ƙarfe takwas na safiyar rananr agidan tayiwa Bahar, tazo ta tarar Hafsa tana bacci, Mood dake falo ta harara kafin tave tana taɓe baki "Kai ina Jikata kums ƴata" Girgiza kanshi yayi kafin yace "Ohh matata wai? Bacci take meye?  Dundu ta ɗaka masa a baya

"Ja'irin yaro ni zaka gayawa sanabe? Matarka ma kake gayamun, zakamun bayani ko kuwa, yau inaga ka ɓalla mata ƙafa ɗaya ko? Murmushi yaƴi sannan ya gyara zaman sa

"Dama wurinki zanje yanzu, maganar Hafsa. Jiya Momyn ta tamun waya akan maganar mahaifiyar ta, nasha mamaki sosai wannan ya sanya nake cewa zanje nayi ƙwaƙwaran bincike akan hakan, ban gama aminta ba" Kallon sa tayi cikin mamaki sannan tace tana kaiwa zaune

"Meta sanar mata ne? Gaba ɗaya ni bata sanar dani akan komai ba" Murmushi yaƴi sannan yace

"Idan aka motsa kice Jikar ki ƴarki, gashinan dai kinga nafiki matsayi a gunta" kallon takaici tayi masa kafin tace,

"kaga zaka gayan ne ko kuwa?

"Bahar kinsan meta sanar dani? Tsaki taja cikin masifa tace "Dole in sani mana tunda abun saukar wahayi ne" Dafa kanshi yayi yana dariya kafin yace

"Cewa tayi ƴar sarkin fulanin wuro ce taya haka zata kasan ? Magana take akan Masarautar Sarki Me Fura, Malam Arzika Djoro" Shiru Bahar tayi kafin tace "Tunani na bawai akan gaskiya ko ƙaryar abin bane ba, tsananin kamannin Hafsa da kuma Surbajo nake hasashe kamar karka ambaci Sarkim Fulanin Wuro" kallon ta yayi da mamaki "Surbajo kuma da Hafsah? Tayaya? Gyaran zaman ta tayi kafin tace

"Surbajo da kake gani mahaifin ta shine tsohon Sarkin fulanin wuro me rasuwa, a yanzu haka ɗan sa ne akan  mulkin wato Arzika Modibbo Djoron daka faɗa, ita sunan mahaifin ta Modibo Djoro,abin ma daya ƙara kawoni shine akan matsalar ita Surbajon, sam bata maganar gida idan na mata maganar seta saka kuka tamkar dai am mata kurciya" Ɗan kallon Bahar yayi cikin mamaki sannan yace

"Kaina ya ƙulle sosai, tayaya haka zata faru? Babu shakka Ubangiji me girma da ɗaukaka ne, idan har ya zamana Hafsa jinina ce to ko tabbas zuwanta a rayuwa ta akwai wani dalilin, ambatar kalmar kamanin da kikayi tanayi da Surbajo seyaja tunani na zuwa ga kawo siffar Surbajo a kusa, tabbas murmushin su kaɗai yana kamancece niya dana juna" Nisawa Bahsr tayi ƙafin tace

"Maza tashi muje wurin.Momyn tata, inason sanin gaskiyar labarin" Miƙewa yayi  ya shiga ciki ya ɗakko key sannan yazo suka bar gidan.

**************
   Lokacin dana koma ƙauyen dana dakko hafsa da sunan zan bata haƙuri akan abinda ya faru senayi rsshin sa'a dajin akasin labarin abinda nake tsammani, gaba ɗaya Bilal ya lalata sunan Hafsa ta dawo mara tarbiƴa a idan dangin ta, haka fito gwiwa a sace sedai me kakarta wacce ta haifi ubanta wato Baba suwai seta janyoni gefe tace dani

"Barira akwai abinda nake so in gaya miki akan Hafsa" Nan take cewa dani,
"Yarona Kabir ya taso yana son kiwo sosai mu kuwa gaba ɗayan mu nan gidan maƙera ne bama noma baku ma kiwo. Yasha wahalar duka da kyare akan yaƙi gadon gidan su awurin mahaifin sa da kuma sauran ƴan uwan sa, amma sam.be saka yaja baya ba, ni kaina nayi dukan nayi faɗa amma a banza, dukda ni bawai na hanashi kiwo bane nace ne ya haɗa da ƙirar amma sam seyace bazeyi ba, nayi rashin sa'a ne Kabir yanada kafiya! Haka girma yazowa Kabeer yace tas matan garin nan bayaso kowa se wata Nufaina ƴsr ƙauyen tsallaken nan wacce gaba ɗaya mahaifinta da Jere me ƙira basa shiri haka yarinya ma ta kafe amma me se kawai suna zuwa da maganar iyaye suka ce basusan zancen ba, shekarar su biyu suna faman neman ysnda za'ayi amma ina kowa mahaufin sa ya dage. Wata rana muka tashi wuni cur ba kabeer! Babu wanda ya damu saini, dik rintsi baya magarib a ko ina sai a nan gidan amma ranar shiru, muna nan sega samari maza daga ƙauyen mijiye sunzo neman wai ƴarsu da makmai akan Kabeer ya sace ta. Nan aka shiga nema da ban baki amma ssti guda ko labarin wanda ya gansu bamu jiba, hankalin kowa ya tashi akayi ta neman har aka haƙura babu labarin wanda ya gansu ma. Watanni suka wuce har wata goma sha ɗaya kullum ba dare ba kuma rana addu'a nake akan dawowar su, katsam rana guda sega su a gidan mu a tare amma tare da jinjira a hannu! Nan take ƙauyen nan ya ɗauka akan sunce sun dawo da shegiya! Sukayita rantse rantse babu wan ya saurare su seni bayan sati biyu na saurari kabeer sabida tausayin yarinyar datake a yashe kullum bame kulawa da ita, dana ɗauketa jere har sakina yayi naƙi in tafi ko ina, haka dai na saurari kabeer ga labarin daya bani.

_"Lokacin damuka bar gida ƙauyen samarin shaho mukaje domin Malam Bargu ya ɗaura mana aure amma semuka yi rashin sa'a malam ya rasu a ranar da muka isa,dan haka bamu ɓata lokaci ba muks ƙara gaba, bamusan ko inaba sedai akwai kuɗi a hannuns dan haka bamusha wahala ba sabida shanu na na sayar! Muka isa wata rugar Fulani se kawai mukace miji da mata ne dan haka aka bamu masauki ɗaki daya, haka muke kwana tare amma wani mummunan al'amari be taɓa shiga tsakanin mu ba dan haka bayan wata tara da kwanaki a garin semuka nemi zuwa wani garin a ɗaura mana aure, anan semu ka isa wata babbar ruga me shirin bunƙasa saboda arzikin su zanma iya cewa rugar ta zama babban garin fulani naga sunada wayewa har karatun boko suke ba irin mu bane ba, anan muka sauka mukayi kusan wata biyu sedaga baya na gayawa Sarkin gaskiya inaso a ɗaura mana aure, nan take ya hau yimun wa'azi akan lallai mu koma gida a mu baiwa iyayen mu haƙuri akan su barmu muyi auren mu idan har muka kuskura muka bari mukayi aure ba slbarkar iyaye har abada zamu tabbata acikin dana sani! Da wannan muka juyo gida munyi nisa a jeji muka haɗu da wata mata ga jina jina ga alama da wuƙa aka yanki gefen cikin ta tana cikin suturu irin na bororin gidan sarautar yamma damu na shaida hakanne danna taɓa ganin su wata rana munje siyan shanu. Tana ɗauke da jinjira ƙarama ɗanyen haihuwa da kuma wata takarda tare da wani abu me kamada ruwan ɗanyen gwal, munso mu ceceta seta ce mu karɓi yarinyar mu gudu mata da ita tanaso ta cikawa mahaifiyar yarinyar alƙawarin tseratar da ran yarinyar datayi, ta bani takardar hannun ta da ruwan wannan ɗanyen gwal tace in adana idan akaƴi shekaru biyar in kaita inda akayi bayani acikin takardar nan, tare da ssyar da wannan ɗanyen gwal in ciyar da ita, tace ƴar mulki ce a bata kulawa! Hadda zoben zinare a hannun jinjirar, muna tsakiya da cewa bazamu karɓi ƴar ba matar nan ta mutu, muna tunanin ya zamuyi da ita kawai muka jiyo muryar ƙarti suna ga layin jini inda ya zuba, ku bita ku kashe ta har jinjirar, da wannan muka yanki jejin a guje bamusan ya sukayi da matar ba. Ya ƙarashe maganar da wlh Baba haka akayi.

Uwar tace "mahaifin sane ya masa tambarin ƙira na fanɗararrun ƴaƴa yaƴi ajalin sa, ta bani takardar da zoben hannun jinjirar da kuma ɗanyen gwal ɗin tace in nemi gaskiyar magansr. Sanda na buɗe takardar sena tarar da bayani kamar haka

"Sarki me adalci, ko bayan raina kasani ƴarka ce wannan dako suna baka raɗa mata ba, na haihu bayan baka nan kayi tafiya, amma Fulani se neman ran ƴar jinjirar takeyi! Na baiwa Adama ita ta gudu mun da ita se bayan shekaru biyar zata dawo da ita, babu tabbacin zan rayu dan haka idan na mutu ta dawo da ita yarinyar tana tsananin kamannu da kai tamkar an tsaga kara, sannan a gefen hancin ta na dama akwai baƙin ƙololo, ayanzu haka inta yamutsa fuskarta kumatunta duka biyu sukan loɓa, zoben daka bayar a sakawa kome aka haifa yana hannun ta. Masarautar sarkin Fulanin wuro, Malam arzika Djoro. Saƙo daga matarka Fulanin Yarima Djoro Hinda".

Sanda na gama karantawa seda nayi ƙwalla, ko wacece Fulani kuma? Kanaji kasan makircin sarauta ne tsagwaran sa, menene daliƙin ta na neman ran jinjira kamar wannan. Driver na ya kaini har garin inda na nemi iso a masarautar da ƙyar, matsalar dana samu ta farko itace awurin Fulani Babba aka kaini, kallon farko naga tanayi mun kallon wulaƙan ci anan na nemi ganin Fulani ƙarama setace ni wacece? Ana haka kawai sega Sarki ban ɓata lokaci wurin sanar masa wa nake nema ba, anan yace a jagoran ceni zuwa gunta har yana faɗa akan lallai idan baƙo yazo ya tabbatar da inda yazo ziyara amasa iso cen, har zan bar wurin sekuma na duƙa na nemi alfarmar ganin su a tare, shida Fulani ƙarama bayan mun zauna sena gabatar da abinda yazo dani tiryan tiryan na miƙa zobe da kuma ɗanyan gwal sannan kuma na haɗa da karanto takardar nan da nan Fulani ƙarama ta rikice akan lallai tanason ganin Hafsa danna gaya mata sunanta, hatta zanin saƙin fulani datazo dashi nannaɗe tana jinjira kai dama kayan jikinta da Babar Kabeer ts bank na nunar mata, haka tayita kukan farin ciki, da ƙyar mukayi akan yau zasu zo kuma tabbas suna kan hanya dan ita da kanta tamun waya akan hakan" Nisawa Bahar Tayi atake ta zube tana godiya wa Allah da irin wannan girman dayafi ƙarfin duniya da abinda ke cikinta, tabbas Allah mabuwayi ne, wato Hafsa Jinin Surbajo ce sannan kuma jinin Hammood ce! Bahar ta ce,
Chapter 68 · 0% Book details