Sashe 32
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ok" Juyowan da Khairiyya tayi anan ta gansu a tsaye tanacen tana kwasar kayan kwalliya, gaba d'aya ranta seda ya jagule amma batayi magana haka ta tako tazo taja hannun mijinta tana masa lank'wasa, Hafsat murmushi kawai tayi dan ita harga bazatace ga wani namiji a duniya dazata so har take gwada kishi sosai akansa haka ba...... Khairiii tsabar bak'in ciki bata shiga shagon sayar da wayoyin ba, iya Hafsat da Hammood ne suka shiga, lokacin datake zaban wayar acikin wayoyin da aka jere mata k'irar iphone wata fara ta d'auka tana kallon wayar, murnushi tayiwa me shagon sannan tace
"I like this, but pink color" Daga gefen ta taji wata murya dabata tab'a jiba tace
"Your too childish me zakiyi da waya pink kuma?" waigowa tayi suka kalli juna ita da wanda ke maganar a tare suka zare ido, shiya rufe bakinsa ita kuma ra nunashi da yatsa tana k'ok'arin yin magana amma gaba d'aya ta kasa furta komai tsabar mamaki..
*Mu had'u gobe inshaa Allah danjin shin waye wannan kuma maganar sa ta rikitar da hafsat..*
Mom Nu'aiym.
*TSINTAR AYA* FREE BOOK
*NA:BILLY GALADANCHI*
-Babu wata k'awa datake tona miki asiri face kin tonawa kanki asiri, ku dena ganin laifin k'awaye dan abu ya had'aku dasu kuma sun muku tonon silili, kece kika gaya musu kikace kuje ku fad'a.Ba zancen dena yin k'awa kuyi k'awayen ku na alkhairi amma ku adanawa cikinku abinda be shafeku dasuba, koyin tsegumin wani, idan kika sirrinta sirrinki babu wata wacce ta isa ta yayata sirrinki.-
*SHAFI NA GOMA SHA BIYAR*
Cikin wazgewa ya sauke hannun sa, jotter sa ya zaro a hanzarce ya rubuta
"Your wasting my time" Haska mata jotter yayi amma be kalleta ba, waige ta shiga amma tana mamakin mesashi gwale ido hadda rufe baki, babu kowa awurin se ita dashi kawai se kuwa mutumin dake gaban table nashi yana displying mata phones dasuke dasu, kallon rubutun tayi sannan setayi wata siririyar dariya tace a sarari
"Zargina ya tabbata kenan" Amma bashi take kallo ba koda tayi maganar, d'auke kai tayi ta ksrb'i farin wayar kawai suka bar shop d'in bayan ya biya kud'in, seda ya saya mata sim cards har biyu da layinsa akayi gwaji sannan suka d'auki hanyar gida, lokaci zuwa lokaci a mota suna satar kallon juna wanda khairiyya ma ta kula dukkansu basa cikin nutsuwar zuciya kaman yanda suka fito agida, amon sautin muryar Mood yana ratsa dodon kunnen Hafsat, tabbas magana yayi wannan shine karo na biyu dataji maganar sa sedai kuma wancen karon waya kawai ta hango yanayi amma ta tabbatar magana yake, yanzu kuma murya rad'am lafiya lau mezaisa yayi hakan to? akan wane dalili ze takure rayuwar sa alhali yana magana? to kuma ance mahaifiyar sama kurma ce kodai ita d'inma tana magana akwai abinda yasa sukewa mutane kwantan b'auna? zuciyarta tana azalzalarta akan sanin waye Hammood menene ainahin gaskiyar labarin sa shida mahaifiyar sa, daga wacce masarautar suka fito ance kakansa ma na wurin uwa sarkin wata masarautar ne shin menene dalilin dayasa Uncle Jay yana k'anin Ummin hammood amma yake zama a masarautar da yayarsa ke aure a maimakon tasa masarautar, batada wata alak'a da kowacce masarauta seta k'auye, a k'auyensu mahaifinta mahaifinsa shine me garin k'auyen nasu amma banda hakan batasan komai akan sarauta ba, abu d'aya ta sani akwai mak'iyan Hammood a masarautar daga lokacin da akace ze aureta mutane sama da goma sunce ta kashe sa zasu bata dukiya, kodai itama kurmar zata zama ne sabida ta samu amsar tambayoyinta? Har suka isa gidan batasan sun k'arasa ba, seda Driver ya mata magana so kusan uku sannan tafita tabi bayansu tana godiya wa Hammood.
Kai tsaye Toilet ya fad'a ya sakarwa kansa shaya, ya akayi yayi sub'utar baki haka? ze iya cewa a shekaru biyun dayayi a Nigeria koda kuskure be tab'a yiwa wani magana ba seso d'aya shi d'inma a wayane, wayar kuma ta zama dole ne sabida daga U.S d'in aka kirasa, lumshe idansa yayi ruwan me zafi yana sauka ajikinsa, dukda dad'in ruwan dayakeji hakan be hanawa xuciyar sa cunkushewa ba, idan har zargin sa akan Hafsat hakane na turota akayi ta dagula lissafin sa tabbas yau ta samu makamin dashi kad'ai ya ishi mak'iyansa kawar dashi dan kuwa sun saki jikine akan bazasu tab'a bari kurma ya mulke suba, daga lokacin dako yau akace sunsan yanxu ya samu lafiya yana ji yana kuma magana tokuwa sesun yi duk yanda zansuyi sun kashe ruwan daya cika masa baki ya furzar sannan ya fito yabzura bathrobe d'insa ya zauna a bakin gado, wayarsa ya janyo ya k'urawa number ta daya gwada kira d'azu, shin magana ze mata ko me, kokuma ya bata kwana biyu ya gani koda zatayi wata alamar dake nuni da cewar taji kai tamaji, reaction d'inta kawai ya isa ya nunar masa cewar tabbas taji yayi magana, ajiye wayar yayi agefe ya shafi sunar kansa datasha gyara tamkar ta larabawa anyi style da sumar ata gaban kansa, Khairii ce ta shigo ta zauna a kusa dashi
"Menene yake damunka you look really tensed, tunda kuka fito shagon wayar nan naga mood naka ya sauya, kaddai wani izgilin waccen wawiyar tayi maka" Murmushi yayi ya janyita gaba d'aya ya ringum'e a k'irjin sa, sumba ya manna mata a goshi yanajin sonta yana ratsa shi, be tab'a zata qrayuwa zeso wata mace kamar yanda yakeson khairiyya ba amma me wannan yarinyar ta gama da ilahirin gabb'an jikin sa da zuciyar sa, bece komai ba a haka suka fad'a sabuwar duniya, ga alama khairiyya tanada yawan sha'awa sedai kuma tabbas raguwa ce, batason sakin jikinta ayi sha'ani daga zaran tabiya buk'atarta a wurin wasanni seta soma yangace masa ala dole ita ta gaji.
Kai kawo hafsat keyi da wayar dake hannun ta ta rasa tunanin da take, bazata iya ci gaba da rik'e wannan abun a ranta ba, dole acikin biyi setayi d'aya, kodai ya sanar mata gaskiyar maganar sa kokuma ta nema da kanta amma bara ta jarraba magana da Bahar. A zaune ta taddata tanacin Apple zama tayi ta d'auki d'aya itama ta gutsura tana murmushi tace
"Ammu hutawa ake tayi" Murmushi Bahar tayi
"Yo wane hutu da jiki irinna na tsufa kuma? aiba zancen hutu kedai se abinda Allah yayi, likita yace inta faman shan 'ya'yan itatuwa yana k'ara lafiya shisa kikaga gaba d'aya na duk'ufa da shansu" Kwantar da kanta tayi a saman cinyar Bahar kafin tace
"Ammu nikuwa wani abu yana damuna?" Kallon ta Bahar tayi
"Kaddai yawan ciwon kanne ko? Yamutsa fuska tayi tace
"Bashi bane Ammu, kawai akan rashin lafiyar Hammood ne, wainikam anya ba iska bane dashi, amma ayi mutum yana ji amma baya magana? Nisawa Bahar tayi kafin tace
"Hammude haryakai shekaru tara a duniya bayaji bakuma ya magana, makaranta ma seda yakai aka sakashi ta kurame, yanada shekaru goma a duniya akayi masa aikin k'walwa anan garin aka samu nasarar jin sa ya dawo sedai maganar ce tak'i yiyuwa, ita kanta maganar likitoci cewa sukayi damu daga lokacin da akayi aikin zuwa kowane lolaci ze iya dawowa yana magana kamar kowa tunda yake lalurar tasa bada ita aka haife saba, dankuwa harya soma yin magana yanada shekara da wata uku, Abbi Ummi duk fad'a yake, ni kaina yakan fad'e sunana Bare uncle Jay, tuni ake cewa UJay , yaro wasa wasa ya dena magana mun zata shiru shiru ne bayason surutu sekuma abu ya dawo kiyita masa magana baze waigoba sekin tab'asa, koda akaje asibiti sukace cutar kurumta ce akayita magani abun beyiba, jida farko ina kallon komai a matsayin wasa har ina ce masa kurma amma daga bisani sema abun ya shallake tunanin mu, akace a k'walwarsa ne jini ya shiga wani wurin akayi aiki so 2 amma ba nasara, seda yakai 9 aka sake aiki anan akayi nasarar ji ya dawo amma babu magana, Kurma ya wahala arayuwa Hafsat ina masa fatan macen dazata yi tattalin sa, dukda na kula jininku be had'u ba amma inaso kiyita hak'uri da kurma, yakai matsayin da be yadda da kowa ba a duniya sabida wahalar daya sha abaya, idanda yanada bakin magana daya gaya miki irin wahalar dayasha a hannun mak'iyan sa, har gobe sharri ake k'ulla masa agun mahaifin sa, sannan sun kasa aiwatar da komai akansa, kurma yayi kud'in da ko mahaifin sa banaji yanada rabin su, ya samu sa'ar k'warewa a harkar zane da taimakon Shammaz (Likitan yaso a littafin Sa'a tafi manyan kaya), yanzu haka yana kulanda babban kamfanin sa dake UK, ya k'ware a zanen motoci da jirage ke harma da kekuna, ya kware sosai a zanen komai ma daidai da kamfanin k'era tile Hammood ne yake zana desighn duk sanda zasu fito da new, ya shahara a harkar dukda haka nake tilastawa mahaifinsa bashi kud'i sabida kawai yaji kwanciyar hankali akan cewa yanada mahaifa, a Nigeria seda masu tsaro yake yawo, sannan bazaki gansu tare dashi suna yawo ba amma duk inda ya saka k'afarsa suna cen a b'oye. Mangalo dan Allah karki guji Hammude akan halinsa, karkice zaki gujesa sabisa lalurar sa ni nayaba da hankalin ki, wannan ya sanya nake masa sha'awarki dukda dai dayake ina duniya babu wanda ya isa ya miki dole" Nisawa Hafsat tayi kafin tace
"Amma kun k'ara bincikawa koda maganar tasa ta dawo? Dariya Bahar tayi"Ai sunce indai ta dawo muna zaman mu zamuji yana magana, so munata dai addu'a amma har yau shiru" Nisawa tayi
"Allah ya bashi lafiya me dorewa Ammu, inshaa Allah wata rana se labari" Shafa sumar kanta Bahar tayi "Hafsatu, Allah kuma ya bani ikon aske kan nan tatas a huta da rashin zama da hula ko kallabi" Turo baki tayi
"Allah Ammu ina kokari ma, amma kiyi hakuri zanke sakawa"
"Yauwa koke fa? Allah ya miki albarka yar k'warai" Ameen tace tana kara shigewa ajikinta, ta dad'e sosai bata samu wannan kalmar abakin kowa ba, kada Allah ya kashe mata ammunta da wuri....
Zubewa Baba yayi akan gwiwowinsa, tuba nake akan abinda Bilal yayi na rashin hankali, banida ikon lank'wasa Bilal Hajiya, nayi nayi ya maida miki kud'inki amma yak'i, dan Allah dan Annabi ki yafe mana rashin amanar dabamu rike miki ba" Sauke ajiyar zuciya Momy tayi