← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 71

Sashe 41

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har sati biyu ta cika wasan b'uya akeyi tsakanin Hafsat da Hammood tunda ta kira bahar aka tabbatar mata da zancen auren gaba d'aya se hankalinta ya tashi, wata irin damuwa mara misaltuwa ta shige ta, lallai tabbas yau ta tabbata mara gata wannan wane irin aure ne? Ace koda Ummi bazata iya kiranta ta sanar mata ba, rayuwarta gaba d'aya a baud'e take, koda wanda ya tsinci kansa agidan marayu yafita gata ayau, tanada family, na uwa dana uba yaya zata k'are a haka, babu me saurarar ra'ayin ta, bame saurarar uzirinta bameso yaji me take so ita kenan ba kowa bace, da wannan damuwar ta rage walwala sedai tas kudirinta yana nan nason shiga al'amuransa dasuka shige masa duhu.......A b'angaren Hammood kuwa banda damuwa ba abinda yake ciki, yayi imanin cewar yayi katob'arar yin magana ya bud'ewa hafsat sautin muryarsa, besan da wane ido ze kalli Uncle Jay ba, bare kuma Barra datasha gargad'insa aka ko khairiyya kartasan bakinaa yana bud'ewa dan kuwa mata wawaye ne, acewar su kosu haka suke fama da magana dashi irinta wahala ta kurame,dan haka ya zame masa dole ya iya takunsa, mesa bakinsa yake k'aryata zuciyar sa akusa da Hafsat kullum se idan be ganta ba, amma duk suka kasance a tare babu abinda ke hanawa zuciyar sa bugawa dason furta kalamai irin na baki agareta, yaudai yayi kudirin nemanta su fita dan kuwa nanda kwana d'aya zasuje Nigeria yana da kyau ya sanar mata karta kuskura ta gayawa wani wannan sirrin dan haka sak'o ya tura mata akan k'arfe 5 na yamma ta sameshi a mota parking lot zasu fita, dan magabar tafiyar ma baharce ta sanar mata.

Yau d'inma wandone d'amamme ajikinta sedai wannan karon kaftan top ta saka tare da d'aura k'aramin d'ankwali ke zubin hanky akanta, sumarta se yawo take abayanta dan kuwa batayi parking na sumar ba ta zubar dashi abayanta se shek'i take, tana yawan sonyin mu'amala da makeup wannaj ya sanya fuskar nan rad'am take da light makeup wanda gaba d'aya yake shirin turata a jinsin larabawan usul! Kallo d'aya ya mata ya d'auke kanta yauma kamar kullum atare suka zauna a bayan motar driver cikin girmamawa ya gayar da ita sannan suka kama hanya, wani restaurant suka je acen suka jeru domin shiga daga ciki, hannun ta ya kama ya rik'e batare daya kalle taba ita d'inba bata k'wace hannun nataba bata kuma ko kalle saba har suka zauna inda takeda yak'inin an tanadesa ne domin su, lemo aka aka ajiye haka sukai shiru ita ma yau fuskar nan a d'aure tamau, seda yasha lemom ta hanyar zuk'a da straw ya zare gilashin idansa ya ajiye sannan ya shanye idansa anata ya tangale hab'arsa da hannayensa daya dunk'ule sannan yace yana kallon ta

"Kinsan dalilin dayasa muka zo nan" Kallon sa tayi ta yamutsa fuska ya dinga yin abubuwa da izza sekace ajiye mutane yayi cikin takaici tace

"Saukar wahayi ne inaga" D'an had'e fuskar sa yayi "Me kikace ? Kallon sa take har lokacin sannan cikin tsiwa tace "ka manta" Wani gajeran murmushi yayi da gefen bakinsa kafin yace

"Hafsa Abu biyu zan gaya miki, da farko dai wannan shigar dakike kina fita bazan lamunta ba har abada, karki kuskura ki k'ara koda tunanin fita a haka, abu na biyu kuma magana ce akan wannan maganar ta fatar baki damuke nidake, ki sani ko.Ummi na bana magana da ita sabida wani babban dalili damuka barwa kanmu sani, matata zab'ina khairiyya ma dakika gani batasan wannan harshen nawa yana kad'awa ba, inada tarin mak'iya irinki masuso kawai susan sirrin harshena, dan haka ya zame miki dole ki adana wannan sirrin, idan kikayi gangancin zuwa Nigeria koda shadow d'inki kika gayawa mun tab'a magana haka dake wlh sena b'atar dake a doron k'asa, abu na k'arshe dazan gaya miki kuwa shine daga yanxu, karki kuskura kokuma kiyi tunanin zan k'ara miki magana a haka, munyi na farko bisa rashin sani, mukayi na farko bisa kuskure wannan ya zama ma k'arshe kuma munyishine bisa tilas sabida haka anyi farko anyi k'arshe kinaji na ko" sake baki tayi kamar me mamaki seda yakai aya sannan ta tab'e baki tana murmushin kama rainani sannan tace

"Kasan Allah wlh sena tona maka asiri, sena gayawa duniya bama masarauta ba duniya setasan kai butulu ne ka butulcewa Allah da Ni'imar bakin daya baka kana living fake life, ur all fake bakada godiyar Allah, sabida haka sena fad'a coward! Kalmar ta ta k'arshe da matuk'ar dakesa a k'irji dukan ya kaiwa table d'in sannan ya tarwatse duk abinda ke table d'in cikin k'araji sannan isa gabanta ya cafki sumar kanta, atake jijiyoyin kansa suka bayyana tsananin b'acin rai ya haddasa masa ganin jiri da kuma harbawar zuciya, take ya sake kanta yayi azamar zaunawa, ya dafe kansa kusan minti biyar be motsa ba, dan haka hankalinta ya tashi da sauri taje ta dafa shoulder's d'insa

"Dan Allah kayi hak'uri" hannun sa ya sanya ya doke hannunta dake kan kafad'arsa da sauri tayi waje kai tsaye taxi ta hau tawuce gida tanata kuka a motar, tayi danasanin abinda ta gaya masa, tarasa dalilin sayasa take yawan fusata akan sha'anin Mood, koda gaje zalinta yakeci shisa.

Basu kuma had'uwaba sesa zasuje airport, nanma dai irin wannan shigar ta kumayi amma wannan khairiyya ce ta mata magana akan bazeyiyu ta doshi masarauta a hakaba ko kallon khairiyya batayiba har suka hau jirgi zuwa Nigeria. K'asar dasuka tsaya transit ma bakinta da nashi be had'uba, anan ta sauya kaya dan sesa suka kwana ta sanya jallabiya cream me adon dutse bak'i tayi matuk'ar yi mata kyau, sannan suka d'auki hanya dukda a k'ule take da Hammood dankuwa wannan karon iya shisa Khairii ne kawai a VIP ita tare da kuyangi sukabi yarima sukasha kid'ansu.

*Nigeria*

Tunda sukazo khairiyya b'angaren hammood sabo acen suka sauka sabida dama yayi gini acikin masarautar me d'auke da part biyu gefe gefe manya da madaidaici a tsakiya, na gefen dama khairiyya anan danginta suka gyare mata wanda dama tanada labarin hakan se hagu da aketa hidima acikinsa na kai kaya k'awata wuri.
Durk'ushe yaukam Ameena take agaban Hafsat tana gaya mata yanda akayi

"Ranki ya dade anmun waya da kuma sak'on inda zamuyi meeting da 'yan k'ungiya a daren yau, tun zuwanmu dama aketa shirin hakan" Murmushi Hafsat tayi kafin tace tana kallon Ameena

"Kai abin yazo a daidai lokacin danake sha'awar faruwar hakan, nice zanje taron ba keba" Da sauri Ameena ta kalleta ita kuwa taba dariya tace

"Karki damu ai kince basa bari wani yaga wani ko, bazan bari asirin mu ya tonu ba, bazan mayi magana ba akwai abinda nakeso najine da kunnena Meena" Jinjina kanta tayi sannan tace

"To babu damuwa ranki ya dad'e, sunce da magrib zasu ajiyemun kayan sakawa a wani wurin zanje na d'auka" Jinjina kai Hafsat tayi kafin tace

"Wannan yayi daidai, zanyi basaja da magrib sena sauka a d'akinki kekuma karki fito harse zuwa safiya" Meena kanta a k'asa tace

"Amma ranki ya dad'e keda kika fini sanin suma inaga ai kyau kema ace sun gayyaceki sunce babban tarone" Murmushi Hafsat tayi aranta tace ba laifi itama wannan yarinyar akwai brain "Idan suka gayyaceni Hammood ze gane kekuwa, kinsan fa ni komai nawa anfiso ya zama sirri" Jinjina kai Ameena tayi "Ea gaskia Ranki ya dad'e hakane" Hafsat gyaran zaman ta tayi sannan tace

"Ina mutumin damukayi zaki had'ani dashi idan mun dawo? Shiru Ameena tayi kafin tace "Na bincikesa ance wlh ya koma ghana" Tsaki kad'an Hafsat tayi sannan tace

"Yadai zamar mun dole in ziyarci tsohuwar secondry school d'ina, uncle computer nake nema, akwai abinda nakeso na tambayeshi ni banda waya ba abinda na iya operating sosai gwanda ma laptop yanzu nad'an iya"

"Ranki ya dad'e me zakiyi dashi to" tab'e baki tayi

"Ba ruwanki kinji, tashi kije" Haka Ameena ta mik'e tana mamakin wayo irinna Hafsat, yarinyar nan seta warwasa ilimin tantiri kai tsaye.....

********************
Se k'arfe uku da rabi na asuba sannan aka tashi daga wannan taron wanda tsabar tsorata dajin abubuwa Hafsat kasa d'auka kanta tayi, a wannan safiyar kuwa Hammood yana zaune da waya a hannun sa yana duba labarai na wannan safiyar yaci karo da wani heading .

BREAKING NEW'S..*Ashe dama prince Hammood na masarautar Daulatul dinar ba kurma bane?* Da sauri ya mik'e tsaye ya nanata wannan rubutin yakai so goma kafin saitin kansa ya tsaya akan abinda ya gani, k'irjin sane ya doka, tabbas wannan aikin Hafsa ne, dama abinda ya kawota kenan, abinda tazoyi kenan kuma gashi tacika burinta a wurin mak'iya, idan hakane se yarinyar nan ta yabawa aya zak'inta, seya nuna mata iyakarta ayau, setayi danasanin zuwan sa a dumiyar ta me cikeda hazo!!! Wayoyin sane suka hau ruri kusan a tare, nan Uncle Jay ne d'ayar kuma Ummin sane gaba d'aya babu d'aya daga d'aga dankuwa yasan ko zancen me zasu masa!!!

Hafsat dake rik'e da wayarta a wannan lokacin tana karanta New's d'in itama murmushi tasake wanda ita kad'ai tasan ma'anar sa.

MOM NU'AIYM.

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

    *NA: BILLY GALADANCHI*

*Ohhhh gaskia Reader's kuna bani nishad'i, harga Allah inajin dad'in comment naku dakuma k'aunar dakuke nunawa wannan littafin na tsintar aya, Allah yabar tare..... Wannan shafin gaba d'ayan sa sadaukarwa ne ga duk wata me bibiyar littafin Tsintar Aya, kuyi yanda kukaga dama dashi.*

*SHAFI NA ASHIRIN*

  20.

Gabaki d'aya kanta ba k'aramin d'aurewa yayi ba, tayama za'ayi wannan maganar ta fita? Waye yaje ya buga wannan labarin meke damun wannan gidan jaridar dazasu buga labari kansu tsaye batare da wata hujjar ba? Mik'ewa tayi kawai tabar Fadar sarauniya cikin sassarfa har tana had'a hanya kai daga bisani ma da gudu ta had'a dashi, sedai lungu da sak'o na masarautar mutane sunyi gungu d'aya idan ba wayace a hannunsu  ba to jarida ce, wannan abin ne ya sanya ta k'arawa gudun gudu zuwa na fanfalak'i har zuwa lokacin data iso gidan Hammood, tana haki ta kalli hadiman dasuma jaridar suke kallo tace fuskarta a had'e

"Ina prince mood yake? Kallon ta sukayi sannan d'aya daga cikin su yace
Chapter 41 · 0% Book details