← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 71

Sashe 39

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mecece ma'anar k'ungiyar?" Seda Sabir ya d'an waige waige sannan yace "Ture wannan Mulkin sukeso suyi su d'aura nasu sarkin, abinda kenan shine shi sarki meci yanzu yayansane uwa d'aya uba d'aya ya sauka akan mulkin, koda yake ciwo yayi to bayan yayi ciwo seya zamana baya komai kuma babban yaransa be wuce shekaru goma sha biyar na seya d'aura k'aninsa rik'on k'warya seya zamana ya rasu kafin ya warkewa ciwon tofa shine k'anin aka rad'ashi sarki, shikuwa ya kafe sarautar ta ubansa ce abar masa bayan daya girma kenan shiko sarki d'ansa yakeso ya gaji sarautar, to duk wata fitinar data taso a k'ark'ashin wannan mulkin ne" Gyaran zama yayi kafin yace "please tell me more" Murmishi sabir yayi kafin yaci gaba

"A yanzu haka so suke su samu dalilin daze hanawa D'an sarki meci yanzu wato Hammood yin sarauta, kaga sarki idan matar farko daya aura bashi ya fara tarawa da itaba to kuwa baze tab'a mulki ba, an camfa akan idan akayi haka lallai masarauta zat rushe tun kaka da kakakanni, sannan basa son nakasasshe kuma shi kurma ne da farko ammaya samu lafiya yanzu yanaji amma harshensa baya motsi ma'ana baya magana sam" Hannu Billal ya d'aga masa yana murmushi sannan yace

"I've heard enough dakata anan" k'ara nutseshi yayi da ido kafin yace

"Kanaso ka zama gwarzo sosai? Well respected acikin wannan k'ungiyar ka zama kaine kan gaba bayan shugaban k'ungiyar? Murmushi Sabir yayi

"Ranka ya dad'e ai akwai manyana" Shafar gemunsa yayi kafin yace

"Yaro kazo a sa'a ina k'aunarka sosai, ina tsananin sonka Sabir, kasan me? Kallonsa kawai sabir keyi yace

"Inada video na matar Hammood tsirara muna aikata masha'a kafin tayi aure, kuma har wanda nayi sa uwarta inada, kaga idan kashiga k'ungiya bame sanin ka tonima a shigar dani mu kai musu wannan mu tona musu asiri kaga dole a hanashi sarautar, daganan nidakai zamu shana dole a girmama mu a masarautar" Wata mahaukaciyar dariya Sabir yayi kafin yace

"How true? Wayarsa ya janyo ya kunna masa video ya tura agabansa, to waye besan khairiyya ba amaryar Hammood tabbas itace bilal yanata cakalkalarta" Dariya yayi hadda tsalle

"Me gida Allah ya k'ara girma, wlh ka biyani zan b'oye sirrrinka har abada yanzu meye abinyi" ...... Da wannan suka shigar da Bilal acikin k'ungiyar aci duhu wacce akafi sani da Idan fada, sedai kuma gaba d'aya Me neman kujerar sarki be shirya sakin video ba ya shirya amfani da matar Hammood ne ta wannan videos seyaga bayansa cikin ruwan sanyi, acewarsa idan ya sake video za'a zargesa kuma har abada baze bari a gano k'ungiyar saba kodan wasiyyar mahaifin sa........

*Tirk'ashi gadai Bilal, ga kuma khairiyya, ga hammood ga kuma Hafsatuwalle, kowa ya fito tsintar aya, ohh how time flie's, the table shake and turn very first love u bohot bohot readers.....*

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA GOMA SHA TARA*

     Zaman fada ake cikin tsananin jin zafin juna, kowanne da abinda yake sak'awa aransa game da d'an uwansa, tsananin takaicin juna akeji a wannan zaman, gyaran murya Me martaba yayi sannan yace

,"Hammood ya bada sak'o a gaya mana ta hanyar kawun sa yana neman alfarmar a k'ara d'aura auren sa da waccen  yarinyar da abu ya had'asu a baud'e" Zabura magatakarda yayi sannan cikin girmamawa yace

"Ranka ya dad'e ayi haka? Kallon sa me martaba yayi sannan ya d'auke dubansa daga gareshi yace yana kallon Jay

"Menene kake tunanin ya dace akan wannan maganar, naso sosai hankalin sa ya soma kwanciya akan matarsa ta farko, banason rigima"  Zubewa yayi yana me bada girmamawa kafin yace

"Idan mukayi duba da yanayinsa na farko akan maganar auren zamu iya yiwa Allah godiya hakan yana nuni ne kai tsaye da cewar hankalin sa ya kwanta da iyalansa har yake sha'awar k'ari, dan haka ina ganin gwanda acika masa burinsa kawai" Magajin garine ya zube kafin yace

"Allah yaja daran sarki, banaji hakan tunani ne me kyau, idan har akayi hakan ita gimbiya khairiyya nasarautarta bazuji dad'iba sam, duba da cewar dududu auren nanfa ko wata shida be rufa ba"  Sarkin baka cikin girmamawa yace

"Mahaifin gimbiya khairiyya yasan da maganar ita wannan yarinyar ai, ai gata ya masa dacen farko kuma yanzu akan gimbiyar ai bazamu fasa cikawa yarima me jiran gado burinsa ba Allah yabaka nasara"  haka kowa da abinda yake fad'a akan maganar daga k'arshe Sarki yace zeyi tunani akai............

******************
Yau Hafsat sun tashi a aschool kai tsaye Bus stop sukaje itada k'awayenta, tunda taketa wannan ciwon tadena yawo ma sam, tana nan zaune suna jiran isowar Bus se ganin Hammood tayi a gabansu, mik'ewa tayi ganin ya jingina da mota ta matsa kusa dashi, seda suka kalli juna na some seconds sannan tace

"Yaa Mood Barka da rana" kallon sa take yanda yake wani yamutsa fuska kuma ga mamakin ta seya motsa bakinsa amma ba magana yayi ba, hannu ya nuna mata ta shiga mota seda ta gama karantar yanayin sa sannan ta juya dayiwa cylia da chidi sallama ta bud'e gidan baya ta shiga, shi d'inma baya ya zauna ya janyo New's paper ya soma dubawa abinda yake shirinyi rayuwarsa banda harbawa babu abinda take amma duk yanda yaso yaji maganar Uncle Jay yau ji yake baze iya ba, shi d'inma namiji ne, ya mallaki hankalin kansa, yanada matuk'ar muhimmanci ya yak'i mak'iyansa, yanzune lokacin daya dace ya zauna acikin mak'iyansa ya dena tsoron su ya nuna musu iyakar su....A b'angaren Hafsat kuwa Allah ya halicceta da saurin karantar halayen mutane, indai har ta nutsu mutum ya nutsu tokuwa sedai idan bashi take kallo ba, amma muddin idanta yana kan mutum to kai tsaye zata iya karantar zuciyar sa akowane yanayi suke atare musamman idan akace idansu yana sark'e dana juna, a irin hakan ta karance Bilal tunkafin ya bayyana manufar sa akanta, a irin haka ta karance halin da Bilal da momy suke ciki tun kafin ta fara jiyo sautuka muryoyin su suna shek'e ayarsu, a irin haka take janye jikinta daga duk wani me sak'a gadar zare iri biyu a rayuwar ta, Hafsa yarinyace da magana be wani dameta ba, amma tanada wayau fiye da tunanin duk wani me tunani, wayonta yakaita gacin nasara ta k'waci kanta a hannun Bilal! Wani mayaudarin murmushi ta sakarwa kanta tunawa da yanayin idan, labarin da zuciyar sa ke bata daban akanta amma idansa yana yawan k'aryata nazarin sa, zuciyar sa tak'i tsayawa akan cutar dashi zatayi idan nashi ma basu gama yadda da hakan ba, abinda ta lura dashi a yanayin sa na yanzu akwai abinda yake shirin aikatawa sedai ya gagara nutsuwa ya aikata koma menene, kawar da kanta tayi daga dubansa zuwa ga hanya taga gaba d'aya ba hanyar gida suka d'auka ba, wani siririyar dariya tayi me had'e da Hmm tana son wannan baiwar da Allah yayi mata, tana tsananin jin dad'i idan tayi karatun faifan fuska da zaren zuci ta canka daidai kanta har wani fad'i yake, d'agowa yayi ya kalleta idansu ya sark'e dana juna ko wannensu ya gagara d'auke idansa ana d'an uwansa har lokacin murmushi ne k'unshe a fuskar ta yayinda yake k'ara had'e tasa fuskar sa a zuciyar sa yanaji tamkar yarinyar nan ta gama raina masa wayau dariyar me take, k'ara fahimtar abinda yake tunani aransa ya tilasta mata k'arayin wata dariyar babu shiri wacce a wannan lokacin kasa hak'ura yayi ya damk'o k'aramun d'an k'walin data rufe kanta dashi me zubin hankici ya had'o tare da sumar kanta, idansa anata amma ga mamakin sa go gezau batayi ba, bata motsa ba, bata kuma nuna alamar taji zafin rik'on ba, d'auke nashi idan yayi anata sannan ya cillar da ita gefe yana jan gajeran tsakin daya fallasa tabbas harshensa yana motsawa ya kwantar da kansa akan jikin sit motar yarasa mesa hankalin sa yake yawan d'aukewa zuciyar sa bata masa sassauci akan kai hannun sa jikin Hafsa, besan wane irin k'i yake mata ba haka, koda yake shi halittarsa ce k'in duk wani mak'iyin sa indai har ya fahimci kai mak'iyin sane tokuwa tabbas shima daga ranar ya dena sonka har abada, driver daya gaji da shawagi dasu seyace

"Yallab'ai ina zamuje? Beyi magana ba bashida niyyan yi, har yanzu yana b'oye ainahin gaskiyar magana hafsat ce ta kallesa ya lumshe ido amma bashida niyyan magana tace

"Take us home" Bud'e idanshi yayi ya zube su tas akanta tace tana gyaran sumar kanta

"Take me home i mean, bansan inda yakeso yaje ba shi, amma ni gida zanje" Parking driver yayi ya waigo yace "yallab'ai muje gida ne?" A hankali ya gyad'a masa kai ita kuwa ta d'auke kanta ganin driver ya d'auki hanyar gida tace a sarari

"Ko'a tarihin hikayoyin da suka gabaci zamanin mu ban tab'ajin labarin ko wanda ya tab'a ganin kurma wanda takejin komai amma baya magana ba, se kai yaa Hammood kai d'an baiwa ne, sam harshen ka baya motsi" Yi yayi tammar beji taba, dankuwa ko motsawa beyiba harta k'araci maganganun ta na rainin wayau aganin shi..........Motar yana parkawa da sauri ta fito ta zari jakarta, kanta yana mata ciwo sosai akan rik'on sumarta da yayi, tarasa metayiwa wannan man d'in yakeji da kansa sosai, mugu kawai. A k'ofar shiga parlor tayi karo da khairiyya zata fito ita da muk'araban ta, kallon juna sosai sukayi sannan da k'yar Hafsat tace

"Sannu da gida khairiyya" Dama khairiyya ta shak'a ganin Hammood ya d'akko Hafsat daga school sekace ba Bus take dawowa dashi ba, rigarta ta janyo tayi dragging nata gabanta dan ita hartayi gaba abunta

"Ban hanaki kiran sunana ba gatsai, ni sa'ankice gimbiya khairiyya zakice jahila kawai" yamutsa fuska hafsat tayi har seda duka gefen chicks nata suka lob'a, tana kallon cikin idon khairiyya tace

"Koda wane lokaci ina mamaki idan akace waike gimbiya ce haihuwar babbar masarauta irin ta Baiha, gabaki d'aya yanayin magana kike irinta 'ya'yan buje, wannan dalilin ne ya sanya bazan tab'a jinginka ainahin sunanki da wata kalmar gimbiya ko princes ba, ki bari tukunna randa duk kika zama me irin kalaman tushenki, ni matsa ki bani wuri danla" Cikin d'aga murya khairiyya tace "Kutmar uban cen kai ni kike gayawa magana a baud'e, hannu ta d'aga zata kaiwa Hafsat mari Hafsa ta tare hannun ta cillar dashi
Chapter 39 · 0% Book details