← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 71

Sashe 25

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Muhseen kace sunan ka ko? Gyad'a masa kanta yayi tace

"Muhseen ban saniba kozanyi tsawon rai, ban saniba kozankai safiya, muhseen zuciyata tanamun tsananin nauyi da zafi, muhseen na tab'a Allah da yawa banaji ze gafartamun, bansanka ba amma tabbas hankalina ya kwanta da kai, bansaniba ko Allah ne ya dubeni da idan Rahama ya jehoka a rayuwata a daidai lokacin danake tsananin bukatar kafad'un dazan dafa in mik'e" Murmushi yayi yanajin taisayin ta

"Ma babu a duniyar nan girman laifin dazaki rayu kina yiwa Allah harki tuba tsakaninki da Allah akan bazaki k'ara aikata zunubi ba, Allah be gafarta miki shiba, istigfari yana tsananin kankare zunubai, kuma babu wanda yasan ze mutu ko sanda ze mutu, inshaa Allahu zaki samu lafiya ma, nidai koma menene kiyi kok'arin ciresa a ranki zekiji zuciyar taki ta miki sauk'i" Nisawa tayi kafin tace

"Hadda inna samu yaron mutane yana d'an shekaru goma sha bakwai besan komai ba inada shekaru kusan ashirin da shida da 'ya'ya biyu na tab'a aure na fito na lalata shi? kana gani Allah ze tab'a gafartamun wannan mummunan zunubin, nina lalata rayuwar Bilal, nice da kaina na sanya hannu wurin ganin na la'anta rayuwar sa, shekaruna bakwai ina d'aurasa akan hanyar danakeso yabi, daga k'arshe yayi gurb'acewa mara muni, ya lalata 'yan aikina sunkai biyar yayiwa biyu ciki amma duk sabida biyan bukatana na d'aure masa gindi, yanzu gashi yayimin ramuwar gayya mafi ciwo" Muhseen gaba d'aya ji yayi bayason jin zancen yace

"Kinga Ma bakida lafiya,yishiru kawai da wannan zancen kinji? zaki warware ne da yardar Allah, da izinin Allah zaki mik'e kiyita istigfari, yanzu ki bani address d'in dai" Haka tq bashi atake ya kira driver ya masa duk bayanin daya dace sannan ya kashe wayar, ya k'ara kiran waya wani restaurant yayi placing order na abinci sannan ya dawo kusa da ita ya zauna aranashi yana tunani iri iri..

****************

Mood ya rasa yanda zeyi da khairiyya, duk iya tunanin sa ya tsaya cak waze tinkara da ita ahaka? hatta muhseen bayaso yasan wannan abun ya faru da khairiyya, toshi ya zeyi? idan yace ya d'akko wasu daga cikin bayin sa ya gayyato munafunci da kud'insa, idan yace yaje da ita fada yasan wannan ma masifa ce, idan yace ya dawo nan ya kula da ita abu biyu ne ze biyo baya na farko Galadima seyasan inda yake da abinda yakeyi na biyu kuma.shi yaya ze rayu iyashi da mace acikin gida? anya baze turata gidan iyayenta ba kuwa? wannan jarabawar dame tayi kama ne haka? zamanyayi akan kujera ya dafe kanshi, bayaso yayi tunani me yawa dan tabbas ze iya haddasawa kansa ciwon kai daze iya janyo masa komai ,dukda bayasob kiwa yaji abinda ya samu khairiyya amma ya xame masa dole ya gayawa Uncle Jay da ant Barra, dan bashida yanda zeyi da ita, wannan tunanin ne ya sanya ya mik'e yaje har asibiti wurin Dr. Yaseer ya rok'esa sukaje har gidan Uncle Jay bayan ya masa bayanin sanda sukaga Khairiyya ita da wacce ke cewa uwarta ce sekuma ya baiwa Yaseer dama ya zayyanemu abinda yakeda yak'inin shine ya faru, Ant Barra ta tausaya mata ainun tace tana kallon Jay

"Jay anan gidan babu wanda ze zargi komai akan khairiyya, yadai dace mu d'akkota ta dawo nan inyaso senake kulawa da ita zamanta acen bashida wani amfani koda yake babu wanda yasan da gidan amma dai idon fada idon masifa ne idone na duniya ko ina yawo suke" Saukar da kanshi yayi a k'asa yana wani nazari kafin daga bisani ya gyad'a kansa cikin gamsuwa da bayanin datayi.

******************
Lokacin da Khairiyya ta farka babu kowa a d'akin se ita kad'ai, sosai takejin jikinta yana mata zogi, har ranta tanaji cewa bazata iya tafiya konan dacen ba, a zuciyar ta kuwa tayawa take zata kashe kanta har abada, gwanda ace bata duniya akan wannan mummunanr bak'ar rayuwar data fad'a, motsin tab'a k'ofar dataji shine ya mayar da hankalin ta zuwa wurin bazata iya tuna komai ba, yaushe tazo nan? waya kawota nan kuma? kallon sa tayi ganin kurma ba k'aramin tayar mata da hankali yayi ba da sauri tasoma kok'arin mim'ewa zaune sedai azabar dataji ya tilasta mata k'walla k'ara ta koma da azama da kwanta lokaci d'aya idanta ya kawo ruwa a hankqli tace

"Wayyoo Annah its really painful" da azama shikuwa ya matsa ya rik'e hannunta, da ido suka kalli juna lokaci d'aya hawayen idanta ya gangaro, bakinsa ya motsa amma be iya cewa ko k'ala ba, da azama ya zaro wayarsa ya rubuta

"Please dont cry dear, u'll soon get better" Haska mata screen d'in yayi ta kawar da kanta batare data kalla ba, hannun sa ya sanya ya waigo da hab'arta ta kalleshi ya nuna mata screen d'in wayarsa, badan taso ba ta kalla, kallon sa tayi bayan ta gama karantawa sannan tace cikin kuka

"Banaso na warke, so nake in mutu wlh, i just want to meet with Annah na before i die, zan gaya mata wasiyya idan na mutu kada su bari momy na tazo kusa da gawana, she's evil, she's a monster i hate her" Kallon mamaki ya mata, sannan ya hasko matar datace mahaifiyar tace, da sauri ya goge wance ya rubuta

"Subhanallah khairii, she's ur mother remember? take back ur words now! ya k'arashe maganar yana tsatsare ta da ido, tana karantawa ta d'auke kanta tace

"Noo never, i will never take those word's back! i hate her she's evil, she's a selfish mother, ta wargazamun rayuwata, ta cutar dani, ta zalinc.....Da sauri yakai hannunsa ya rufe mata baki suka soma kallon juna, a hankali tasanya hannunta ta ture hannunsa dake bakinta tace

"Dan Allah ka saurara kaji mezan gaya maka, idan naci gaba da rik'e maganar nan mutuwa zanyi kafin inje gun Annah na" Da idanshi ta fahimci yana sauraren me take fad'a dan haka a hankali ta fara bashi tarihin rayuwar ta.

**************
"Lokacin dana tashi bansan kowa ba se Annah na, itane ta haifi mahaifina so she's my granma, Anna love's me so much a yanda take fad'a tace tanajin tausayina, sabisa mamana ta tafi ta barni when i was very young i mean a little cute Annah's pet, bansan wani damuw aba nida brother na Bilal, kawai nasan sauran siblings namu ba mamanmu d'aya ba, and mu muna rayuwa ne awurin granny su kuma sauran a main part na gidan wurin sa sarki yake da family nashi, inada son mulki sa izza, inada jinkai kamar yanda naji ake fad'a kowane lokaci, nayi primary school na a k'asar nan, amma a UK nayi High school na wurin yaa Bilal a lokacin yana college acen, ni 'yar gatace sosai sanda na kammala secondry school naso inci gaba a UK but Annah tace sam ita indawo gida kawai haka na hak'ura na dawo nan da zama ba samu admn nashiga 100 level ban saniba ashe duk mutunci na danaketa kariya a UK shirme nake, ban saniba ashe budurcin nan danake tak'ama dashi mahaifiya ta sayar dashi tun kafin in gama sanin darajar sa aguna! Sanda nake zuwa jami'a a met with a guy Sunansa Bilal, had'uwa na dashi na farko dana biyu duk fad'a a na uku ne muka soma zama ftiends, wannan kafin nan kawai se maganar aurena dakai ya fito, Jinkai da isa ya sanya naji bana son auren wani abu wai kurma, da haka dana gaya masa ya xigani ..............
............ tas ta kwashe komai ta gaya masa ta k'ara da cewa

"My mother sold out my dignity, she let him with no option but to take away my virginity which i value the most, i just hate her i hate my self, how can she be so heartless? she's inhuman she's an animal, she should have marry idan tasan bazata iya rik'e kantaba, now u ce because of what she did i lost everything am a looser!! ta k'arashe maganar cikin d'aga murya tana kuka" Bashida bakin magana a wannan gab'ar, besan ta ina ze fara ba, tausayin ta ya kashe shi, amma wannan Bilal d'in idan ya had'u dashi seya kaishi lahira, wane irin haukane zaka nunawa yarinya tsiraicin uwarta tana aikata masha'a, wannan yaran ya cancanci a kashe sa ma. Hannunta ya rik'o se kuka take ta kallesa girgiza mata kansa yayi alamar ta dena kuka sannan ya zaro yawar da dauri ya rubuta

"U know i can't talk ko? Haska mata yayi ta karanta kafin ta girgiza masa kanta, mayar da wayar yayi zuwaha dubansa kafin ya rubuta mata

"Please zanyi rubutu a jotter ki daure ki karanta" Nanma daya haska mata d'aga masa kanta tayi alamar "to" Da sauri ya zaro k'aramar jotter da pen ya duk'ufa rubutun kusan 19mns kafin ya mik'a mata ta karb'a tana daga kwancen sannnan ta soma dubawa

"Khairii pleasee wannan maganar ya zama sirri a tsakanina dake, karki sanar da kowa har Annah ma kinji, wannan mummunan labarine mara dad'in ji, wabban labarin idan ya bazu ke kanki se fita ya gagareki, ba komai ake gayawa kowa ba Khairii, ki rufawa mabaifiyar ki asiri ina yace dake ta tuba ? toki yarda da tubanta ki k'addara cewar koda babu wannan abun daya shiga tsakanin ke da mahaifiyarki da wannan yaron se hakan tafaru dake, just be grateful to Allah daya kareki ma, karki d'auka cewar addu'ar dakike bata karb'u ba a lokacin, keda kanki kince bakisan mesa ya fasa raping naki da gaske ba so kikasan wanne kalan ciwon ne ajikin sa Allah ya kareki? so please karna kuma jin kin gayawa mamanki wannan munanan kalaman, ki yafe mata tunda k'addarane baya wuce kan kowa, sannan kuma wannan maganar na kasheshi daga yanzu nan nidake ban yarda ki gayawa kowa ba. maganar mutuwa kuma karna kuma ji addinin musulunci ya mana umarni da yarda da kaddara ta alkhairi dakuma akasin ta ke musulma ne, kisan me kike ciki, wasu yaran zakiga basukai 18 bama amma samari sama da goma suke raping nasu at thesame time su me kikeso suce? ehm? d'agowa tayi bayan takai k'arshen jotter d'in sannan tace
Chapter 25 · 0% Book details