← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 71

Sashe 4

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Yamma sosai ya dawo daga wurin motsa jiki ya tsaya yabi wurin da kallo, yau ina wannan yarinyar ne? idan baze manta ba ya ganta wurin yafi so bakwai, kota dena zama a k'asan bishiyar ne? meke damunsa na damuwa da ita sosai haka ya tambayi kansa? Bafa komai kawai tausayi take bashi ko ba'a fad'a ba yasan akwai abinda yake damun ta, besan fuskarta ba dan kuwa kullum kwanan duniya kanta a sunkuye yake amma ta masa tsaaye tsayin alif ajikin allo a zuci kome yasa oho! Nisawa yayi kawai  yaci gaba da gudunsa jikinsa yana nan a murd'e se gumi yake had'awa a sukwane ya isa gida amma kamar kullum a masallaci ya tsaya yayi sallah tukunna har isha sannan ya shiga ciki. A gaggauce yayi wanka ya shirya yauma kamar kullum, wurin Muhsin ze tafi suyi maganar abinda ya shafi kasuwan cinsu sabida harga Allah k'asar yake neman dalilin daze d'aga mata idan ba yabar k'asar ba D'an galadima ze sanya yazo ya aikata abinda bashi kenan ba, D'an galadima munafiki ne...

    'Yar shara kuwa a tasha da suka sauka anan dirama ta tashi akan kud'in motar da tace zata bayar idan sun iso, dan kuwa batada ko k'wandala banda uban zogin da k'afafunta ke mata na rad'ad'in k'una... wata iriyar kallon banza kwandastan motar ya wurga mata yana lashe leb'ensa sannan yace

"Idan kin yarda in bashi kud'insa in rufa miki asiri, kekuma ki biyani daga baya" jikinta yana rawa ta amince da hakan aganinta zata samu kud'insa seta biyasa daga bayan koma a inane, dan haka ta masa godiya shikuwa ya biya kud'in cas bisa ass. Godiya ta masa azuwan idan ta samu zata biyasa kud'insa shikuwa yace alambaran kwana zasuyi atare ya fanshe hamsin d'insa, tun suna magana a cikin rad'a har maganar ta tashi atasha aka zagayesu, atake ya murd'eta akan itace ta masa alk'awarin ze fanshe ajikinta, gashi ta gaji da tsayuwar sabida akan duga duganta take tsaye, wani mutum ne yace da kwandastan

"Shinkai Zubairu dakata, nawane kud'in nata" Seda ya kalleta sannan ya kawar da kansa yace "D'ari bakwai ne" Mutumin ne ya zaro d'ari bakwai ya mik'a masa sannan yace yana kallon sa

"Bata amince da kaiba, dan haka gankud'inka nan ta biyaka, wannan yarinyar yar luwai caras da ita bazatabi k'azami kuma karen mota irinka ba zubairu, kumama akan wannan gajeran farashi, yarinya muje nizan baki dubu biyu" Cikin kuka tace

"Niba karuwa bace dazaku rik'a cilli dani tamkar wata k'wallo, wannan salon wani wulak'ancine kuma, ni a k'auyen d'an biram suka d'akkoni akan idan munzo zan basu naira hamsin, yaya kuma zezo yace d'ari bakwai ne? banisa hamsin amma inada zoben azurfa na tabbatar zekai dubu biyun da kai kake ik'irarin zaka bani, sabida haka gashi kaje ka sayar kabiya karuwa irinka badai niba" Ta k'arashe maganar tana cilla masa zoben ya daki k'irjinsa ya fad'i a k'asa

"Abinda kukamun se anwa 'ya'ya ko matanku ko k'aninku wlh, na barku da Allah shine ze sakamu  mugwayen banza" Ta juya tana d'ingishi ta fita tabar cikin tashan yayinda su kuwa sukayi cirko cirko suna kallon ikon Allah.

     A bakin junction taje ta zauna ta sunkuyar da kanta, ga dare yayi koda babu waya a hannunta ta tabbatar cewar tara na dare yayi idan ma be gota ba, koda ganin yanayin yanda mutane suka rage kai kawo kasan cewar dare ya ruga sosai, Ganin zata b'atawa kanta lokaci ya sanya ta mik'e ta soma d'ingishin datake gidan momy zata koma, itace rufin asirinta gwanda zama wurin Bilal idan Allah yaso baze samu abinda yakeso awurin taba amma wadannan mutanen ba Allah a ransu ko dukkansu farmata zasuyi, tana wannan unguwar datasha yake da nisa sosai da gidan momy amma haka zata taka, bazata hau wani abin hawa batada kudiba dan batasan yanda za'a k'arb'eta ba agidan, da wannan shawarar taci gaba da d'ingishi tana takawa a hankali.........

  Hamood be bar wurin Muhseen ba se k'arfe sha d'aya da 'yan mintuna, babu yalwar abun hawa kazalika jefi jefi zakaga mutane suna yawo, kuma duk wanda ka gani zakaga alaman sauri a tattare dashi, yanayin yanda take tafiya ya shagaltar dashi, d'ingishi takeyi alama sun nuna cewar da dugaduganta take takun tome yasa? yasan wannan kalan hijabin da zanen jikin amma a inane ma? yaya take tafiya babu takalmi a k'afarta? da wad'an nan tunane tunanen yaje gida batare daya tsaya wurin yarinyar ba sedai tambayoyi marasa amsa fal a kansa.

'Yar shara tayi tafiya sosai har k'arfe d'aya na dare ya tadda ta babu alamun zata isa gidan Momy, hankalinta ya soma tashi sabida ta kula cewan daga ita se karnuka akan hanyoyin datakebi d'in, sannan idan ta kaucewa titunama bawai b'ullewa zatayi ba, kana ko yanzu a yanda take hange akwai nisa sosai da inda take hari..... Takun dataji a bayanta ne ya sanya tayi hanzarin waigowa mazane sunkai su bakwai, a yanayin yanda ta gansu kuwa babu alamar mutunci a tattare dasu, wannan ya bata damar k'ara mai a tafiyar datakeyi dukda bata iya taka k'afarta sedai d'ingishi, tun suna k'ara saurin dasuke har suka soma gudu kad'an, ganin haka itama ta k'arawa dokinta linzami ta soma gudun cikin azabar k'una da radad'in da k'afarta keyi,dama gashi tana lokacin al'adarta wannan ya sanya mararta ta murd'e mata wuri d'aya lokaci d'aya jini ya kuma b'alle mata ga dama matarin data saka tuni ya jik'e sharaf! gudun fanfalak'i suka somayi atare suna ihu suna sowa suna mata dariya tsuntsu daga sama gashashe shine abinda suketa fad'a!

Agogon dake ajiye agefen bed side drawer d'insa ya kalla, k'arfe d'aya saura kwata, mesa ya kasa bacci, yarinyar batayi kama da cewar tana cikin nutsuwa ba, mesa yakeji a ransa tamkar ya baro wani aiki me muhimmanci atiti beyiba gameda yarinyar, ya ganta a yanayi irin na rashin lafiya yakuma ganta tabbas tana neman taimako, ba wannan bama ya ganta lokacin da dara yaja k'afar mata sosai tayi k'aranci akan titi shin mesa be tsaya yaji meke damun taba? zabura yayi sannan ya zari key na motar sa, gajeran wando ne ajikinsa iya gwiwa sekuma riga mara hannu med'an fad'i, hanyar waje kawai ya nausa aguje yauma kamar kullum, hadiman dake hidima a b'abgarensa wanda basuyi bacci ba se gulmarsa suke.....

A hankali yake tafiya da motar sa haryakai inda yake tsammanin ganinta, direction datakebi anan yabi amma sam ko alamarta babu, beji ya karaya ba haka yaci gaba da zagayen titunan yana k'arewa wuraren kallo, cen ya hangota a kwance sedai wannan karon babu zani ajikinta babu hijabin duk gasunan agefen ta, da hanzari yayi parking motarsa yafito aguje ya k'araso inda take, bin yanayin ta yayi da kallo yana me haske ta da hasken fitilar wayar hannunsa, hannunta taja ta rufe fuskarta inda zata karewa musamman idanta, sannan taja hanninta d'aya tana k'ok'arin rufe jikinta dake a tsiraice ko pant d'inta yana gefe cen a yashe iya rigarta ne kawai ajikinta kuma itama duk an yaga ta, alamomi tas sun nuna fyad'e aka mata tunda gashi harda jini sosai ajikinta, zaninta yayi hanzarin zara ya rufa mata sannan ya juya bayansa kawai ya koma motarsa.

*Idan baku manta ba na gaya muku bazan samu daman yin posting kullum ba, bayan kwana d'add'aya zankeyi da izinin Allah.*

*Mom Nu'aiym.*

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA UKU*

Sumar kansa ya shafa zuwa k'eya cikin tsananin damuwa da fad'uwar gaba mara misaltuwa, mekenan ya faru wa 'yar mutane? yaya zeyi da ita a yanzu? wannan laifin sane ko me? mesa dacen datake tafiya acikin dare tana d'ingishi be tsaya yaji inda zataje ba? menene amfanin zuwansa yanzu? ina ze kaita? Asibiti? they will surely ask of police report ta ina ze fara? besan komai ba, acikin dare yaganta akan ttii anyi raping nata sai kuma me? shi daga ina yake? iska me zafi ya furzar daga cikin bakin sa sannan ya juya ya kuma kallon ta. Wayarsa ya janyo ya kira Muhseen be d'aukaba dama baze d'auka d'inka ba dan yasan baze masa magana ba, dan haka ya masa txt na wurin daze sameshi yanzu amma shiru shiru babu alamun dawowar sako har zuwa mintuna goma,yanada yak'inin cewar tabbas Muhseen bacci yake. k'ara mayarda dubanshi yayi zuwa ga yarinyar k'ok'arin d'aura zaninta take daga kwancen, sanan kuma seja baya take dashi, ganin yana nufota ya tilasta mata mik'ewa da k'yar tana kuka tare da motsa labb'anta sedai sam baya jin metake cewa, gyaran zaman zanin take kokarin yi amma ina se jiri ya d'ebeta ta tafi luuu zata fad'i a sume, da hanzari yayi azamar rik'ota sannan ya zube akan gwaiwowinsa d'auke da ita, kallon fuskarta yake tabbas suma tayi, lallai abun yafi k'arfin tunanin sa, be b'atawa kansa lokaci ba ya zurata a mota ya finciki motar se gida, nanma kwasarta yayi hannu bibbiyu zuwa b'angaren sa yanzu ma aguje kamar kullum, sedai wannan karon kana gani kasan a uzurcen gaske yake, be had'u da kowa ba se mutanen dayake da tabbacin idansu biyu wato munafukan fada, ya tabbatar munafukan fada idansu yanzu yake bude ma, be wani damuba ya haura samansa da ita.

Yafi minti 30 yana tunanin abinda zeyi da yarinyar har lokacin idanshi be kaishi akan tafukan k'afarta, daga bisani sai ya mik'e ya debo ruwan sanyi ya soma kokarin dawo sa ita hayyacin ta ta farka amma ga alama she's unconcious dafe kanshi yayi ya kalli lokaci k'arfe hud'u saura yan mintuna, yaya zeyi? Family Dr. nasu yawa message akan by 6 ya kasance a b'angaren sa akwai patient daze duba masa sannan ya koma yaci gaba da aikin kallon ta har zuwa sanda yaji ana kiran sallan asubah wannan ne ya tilasta masa mik'ewa ya d'auro alwala ya fita masallaci!
Chapter 4 · 0% Book details