← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 71

Sashe 58

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baba nizan koma, sabuwar 'yarkice Bahar tace inzo in gaisheki, me martaba ne yake matsayi  uban rik'ona a yanzu ta sanarmun rashin lafiyar ki tace kema uwatace ina miki fatan alkhairi" Da wannan naga ta bini da ido, kallon datamun ya dasa wani abu a raina harnabar wurin bata dena kallo naba, a k'wayar idanta na hango tsantsar k'auna, tabbacin cewar tana tsananin jin duk abinda nake cewa, a hakan na kasa bacci a wannan daren ban yadda batada lafiya akai ba, inada yak'inin garas take,mesa take pretending? Kasawar hak'urina ya sanya najewa Bahar da maganar lallai Baba surbajo lafiyar ta k'alau kokuma dai ta warke, da farko bata yardaba akan cewar cutace datak'i samun waraka fin shekaru talatin aduniya amma dana k'ara komawa namata addu'a sanda zan tafi seta rik'e hannu ta k'ara mayarwa akanta alamun tana buk'atar addu'an fiye da yanda nake mata, dan haka sena k'ara k'aimi na d'auki tsawon sati d'aya ina zuwa ahaka harna soma samun damar tana mun magana, lokaci zuwa lokaci sedai na kula cewar a sirrance takemun magana dan haka wata rana senaja bahar mukaje wurinta acikin talatainin dare, wanda na jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya a wannan daren, na farko A ranar nafara yin arba da mutan k'ungiyar aci duhu, aranar kuma mukayi nasara Baba Surbajo ta bamu cikakken labari akan lokacin haihuwar ka, tace damu.....

"Bayan na samu ciki sena dinga b'oyon cikina, badan komai ba sedan dalilai guda biyu na farko dai sabida an tabbatar mun da cewar Maryama itace ta sanya aka kashemun yarana guda biyu, nayiwa Me martaba maganar a wancen lokacin amma se gaba d'aya ya nunamun be aminta ba gulmar gidan sarauta ne! Na biyu kuma an tabbatar mun dacewar tace bazata k'ara barin ciki yayi k'wari ajikina ba ga wannan cikin nima bansan dashiba har seda ya soma motsi, nayi mamaki sosai danko girma bayayi, haka nida kuyanga ta ta wancen lokacin muka rufe maganar, ga mamakina rana d'aya ina lissafin ciki wata bakwai sega nak'uda gadan gadan, kuyangata taso sosai ta karb'i haihuwata da kanta amma se haihuwar tazo da gaddama yasa dole ta sanar a Fadar me martaba inda ala dole aka had'ani da Maryama wacce a lokacin itama tana gargarar haihuwa. Dukda azabar datake ciki hakan be hanata d'agowa ta kalleni ba tace cikin bak'in ciki

"Yanda kika b'oyemun wannan mugun cikin dake jikinki sena nuna miki iyakarki idan har na haifi Mace ke kuma kika haifi Namiji" Bance da ita komai ba kawai na kawar da kaina abinda nakeji a lokacin ya isheni, haka inaji ina gani aka sallami masu taimakona ya rage dagani se ita sekuwa Ungowar zomar dabata amsa umarnin kowa sena Sarauniya Maryama. Itace ta fara haihuwa kafin ni sedai Na mace ta haifa, akan idona ta kawar da kanta gefe sanda aka nuna mata yarinyar sannan tace

"Banason ganin ta tazone takanas danta wargazamun shirina, so take ta lalatamun duniya ta, tanason kafawa bayana mummunan tarihi, inzo in k'are da haihuwar mace! Akan me gwandamun mutuwar ta da rayuwar ta akan rayuwar ta" Ungowar zoman ce ta soma bada hak'uri tana ban baki, a lokacin nikuwa wata azababbiyar nak'uda ta tasomun wacce tasa nakusa fita hayyacina koma ince na fita hayyacina! Cikin ikon Allah sena haifo yarona Namiji santalele me tsananin kamanni da yayunsa marigaya, koda na dawo hayyacina abinda suka bani shine abinda yafi bani tsoro Maryama ce rik'e da yaron tana murmushin mugunta, ta kalleni kallo me kyau tace dani

"Surbajo ya rage naki ki zab'i d'aya daga cikin biyu abinda zan fad'a, kindaiga iyani dakene se Ungozoma a d'akin nan ko? To kodai ki amshi wannan yarinyar data rigada ta mutu a matsayin abinda kika haifa kokuma wlh tallahi summa tallahi billahi in kashe yaron nan har lahira yanzu yanzu in sauya akalar zancen, zance kin haifi mace kin kashe danna haifi Namiji, kuma kin had'a harshi muna k'ok'arin k'arb'arsa kika kashe shi zan sokawa kaina wuk'a a kafad'a duk ince kece kika sokamun, kinga dai gaba d'aya bayan kinyi asarar d'anki zakuma kiyi asarar mutincin ki k'arshe kema a kasheki a banza" Cikin bak'in tashin hankali na mik'e jiri yana d'ebana nace cikeda rauni

"Maryama wace irin mara imani ceke wai? Yanzu jinjirar nan kasheta kikayi? Hankali a tashe na karb'i yarinyar hannun unguwar zoma ina kuka ita kuwa seta baiwa unguwar zoma jinjirin hannunta tace

"Yauwa yanzu kinga 'yata tana hannunku, tsaf dani na shiga wanka in kimtsa kaina in fito na tarar kin shak'eta har lahira ta mutu kin kuma ce nice na kashe miki 'ya'ya shisa kika kashe tawa! Ya kikaga wannan wasan? Ina sharar k'wallah nace

"Keda Allah Maryama, Allah yafiki wlh, muguwar mace kawai" Wata dariyar shak'iyanci tayi ta amshi jinjirin nawa ta matse masa hanci a haukace nayo kanta nayi wurgi da gawar jinjirar ina k'ok'arin k'watar yarona a hannun ta, kawai se gani nayi ta baiwa Ungozomar yaron da sauri ta k'wallah uwar k'ala take matan dake waje da kuyangi sukayo d'akin tana kuka ta kasa ciro jinjirar ashe a tafasashen kaskon ruwan zafi ta fad'a ban kulaba Allah ma ya sani, ganin sun shigo ta nuna yarinyar tana kuka tace

"Kunga Surbajo ta haukace, sabida haihuwar mace Surbajo ki d'auki d'anyar jinjira ki wurga a ruwan zafi dan zafin kishi a dole sekin haifi magajin sarki, ni sanda banida d'a banda jika kike hayayyafa haka kikaga nayi musu? Take wurin ya d'auki salati aka ciro yarinyar, wata tace zataje ta sanar, nidai gaskiyar datamun yawa ta sanya banje komai ba, kallon marar Maryama tayi

"Ku rufa mata asiri,abarshi akan bisa kuskure yarinyar ta su 'buce mata,ni ina tausayin ta na tabbatar tab'in hankaline ya sameta amma kubar nan wurin da jinjiri na, karta hallaka shi, ban yarda koda kallom sa tayiba, kishi ze iya sakata aikata komai dan haka da sauri kubar nan wurin dashi" Inaji ina gani suka gudumun da yarona ko nono ban bashi ba! Haka ina zaman zamana akazo da Likitan gargajiya ya dubani yace na samu tab'in hankali, maryama seta ziyarceni da sunan dubiya tace duk na kuskura nace da hanakali na seta hallakar da Jinjiri na dake hannunta har lahira, indai inason ya rayu tokuwa sena kawar dakai daga gareshi! Akan tilas na rayua haka dan inason yaron dako ganinsa ban tab'ayi ba ya rayu a duniyar nan.

Sanda Hafsa tazo nan abada labari sadda kabta tayi a k'asa ta dinga rusar uban kuka tamkar babu gobe! Hankalinta a tsananin tashe, Hammood ma kukan yake su Data kowa yayi shiru dan a yanda Hafsa tayi laushi ga alama sesun bata break na 1 hour!!!

Mom Nu'aiym.

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

      *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA TALATIN DA D'AYA*

31.

Gabaki d'aya banda sautin kuka  Hafsat da saukar numfashin Hammood babu abinda kake ji, seda ta nutsu sannan taci gaba cikin raunin Murya.Baba Surbajo tace "Abinda yafi bani mamaki shine yanda gaba d'aya Sarki baya ziyartar inda nake, sanda se labaru nakeji barkatai akan Hammood, akace kurma ne aka dawo akace yanaji amma baya magana, akace Maryama ta kurumce alhali ni tana zuwa tamun tatas da bakinta me tsini tamkar jab'a tasha fiya fiya. Duk wannan bidirin da ake fa ina gaya miki awurin bayi da kuyangin dake zuwa mun aiki nakejin su, tsammani suke banajin me suke fad'a tunda na kurumce amma ni nasan tabbas akwai mugun abun da ake k'ullawa Hammood batare da sanin saba, wani lokacin zezo mun kamar baya cikin nutsuwar sa, wani zubin inyazo wurina seya wuni be tashi ba, yana nan dai muna kallon kallo, hardai rana d'aya na bud'e baki na masa inda ga mamakina shima mayarmun yayi anan nayita so in bashi labarin nan danake baki amma sam seya zamana bakina yanamun nauyi, inajin tsoron yanda ze d'auki abun, amma seya zamana na rok'eshi akan ya rufe sirri na nacewar ina lafiya nakuma sanar masa ya rage kawomun ziyara da rana dan kuwa ido ze iya kai sak'o kuma tabbas wani abu mara dad'i ze biyo baya akaina ko kuma shi, ashe ban tsiraba dankuwa maganar barin k'asar gaba d'aya nashi ya sameni, na kuma tabbatar dan kawai an gano yana zuwar munne, daga haka dai na dena jin labarin sa se bayan wasu shekaru ina nan zaune a zullumi da fargaba, haka har labari ya riskeni akan ya dawo ya zama babba amma yanada fad'in rai da jiji dakai, haka harna soma samun labarin yanada mak'iya anaso a kashe sa! Shiru Hafsa takumayi kafin tace

"Acikin k'ananan bayi da hadiman b'angaren ta ta samo mana labarin ainahin wanene Uncle Jay, kuma su waye 'yan k'ungiyar aci duhu dake k'ark'ashin kulawar idan fada! Nida kaina nayita ziyartar tarukan na idan fada, nayita aikawa wakilai na anan nagano wani abu, da farko dai shi Uncle Jay yayarsa itace ta sanyashi ya shiga wannan k'ungiyar sedai tsuntsu biyu zasu jefe da dutse d'aya, da farko dai babu wani magaji kuma jinin sarautar daze iya gadon wannan sarautar se Usman, shikuwa bashida d'a baikuma da jika sun shigar masa ne dan idan ta tashi sesuce kai suke wa aikin sirri se'a kashe Usman ko'a korashi inyaso seya zamana kai kad'ai kayi saura, bayan nan kuma sesu maka kisan mummuk'e kaida me martaba gaba d'aya kaga fada zata tashi babu makusanci se Jay! Wanda shi kuma k'anin matar sarki ne ze yak'i mutanen fada da rabinsu mutanen sane ciki haffa D'an galadima da Galadima shi seya d'are kujerar mulki, ina fatan ka fahimce ni?" K'ura mata idanshi yayi da suka kad'a sukayi ja, cikin tsananin mutuwar jiki yace

"Hafsat yanzu abinda kikeso ki gayamun shine gaba d'aya matsalar rayuwata makullin rayuwar tawane yake bud'ewa kowa k'ofofi da zasu shigo su cutar dani, barni haka Hafsat banason jin sauran mutuwa zanyi idan kikaci gaba zuciyata fashewa zatayi akan Mulkin dabeko dameni ba" kallon tausayi tayi masa sannan cikin raunin murya tace

"Yas Mood bazaka tab'a gujewa jin zallan gaskiya ba, gwanda ka saurareni" Bece komai ba taci gaba
Chapter 58 · 0% Book details