← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 71

Sashe 52

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke daga yau daga yanxu ma duk abinda zakiji kibarshi a haka ma'ana karkiyi musu, za'azo ana cewa yarima hammood ya miki fyad'e ki tafi ahakan, indai kinason wanda ya taimakeki.ya rayu, indai kinason karmu kasheshi tokuwa ki mana biyayya inba haka ba nan bakida kowa kasheki kawai zamuyi mu kashe banza" wannan maganganun sune suja tilasta bakin gaza motsawa dukda kuwa inaso ya motsa akan fad'ar gaskiya, haka na tabbata a zillimi bana iya cin komai, har maganar aurena dashi tazo kunnena, wata ziyara da Ummin sa ta kawomun baki ta bud'e ta gayamun gaskiyar ita ba kurma bace in sanar da ita gaskiya kuma na gaya mata gaskia, daga baya ne labari ya sameni cewar tayimun magana dan kawai ta tabbatar turoni mak'iya sukayi setaji shiru har gobe babu tashin zancen, a gurguje abubuwa da dama sun faru, mutane da dama sun zo akan ran Hammood sa hannuna sukeso, wasu na amsa musu da to wasu na bisu da dabara wasu kuma na zagesu dama kamar yanda na fad'a na iya tsiwa. Bayan munbar k'asar sena fahimci hankalin fada gaba d'aya yana kanmu, acikin kuyangi da bayi ma akwai wanda takanas ko motsin me yayi sesun fad'a, sena shige acikin su, hatta Kuyangin Khairiyya akwai wanda sukeda aiki akan Mood kawai, bayan na fahimci komai da kowa nasan kowa abinda yake ka sa senayiwa Bahar tiryan tiryan daganan tayi waya da ummi inda atake muka had'e kai da Uncle Jay da kuma Barra acikin taimakon kai da kai gani mun tsamoshi a hannun mak'iya, kuskuren farko da Hammood yayi shine rashin yarda dani, na biyu kuma ya barwa kansa tunanin cewar inya bayyana kansa mak'iya zasu kashesa, ni kuwa nake tunzurashi da kalamaina masu zafi dan kawai nasanya ya dena shakka yafito yayiwa kansa fighting, uncle jay bayaso yayi magana amma ni inaso, da wannan na gayawa 'yan jarida tabbacin yana magana har akayi caa akansa dama haka nakeso, k'ungiyar danake da tabbacin akwai sena shiga acikin ta a b'oye...... tabasu labarin duk abinda ya faru sannan tace

"Wani dare a k'ungiyar munkai ziyara nida Hammood a tare inda aka tashi kamamu shinema ya ceceni, amma seyayi canjiya da uncle Jay shi uncle jay seya koma yana gaya musu be ganni ba, Uncle Jay tsohon d'an kungiyar Ne wanda yake nuna musu atare amma ina zargin sa akan bayason Hammood ya gaji wannan sarautar sabida dalilai masu yawa, ban yanke masa hukuncin komai ba senaga yanda ta yiyu, se iya yiyuwa hujjar dayakeda ita me k'arfi ce. Na fahimci cewar khairiyya 'yace awurin tsohuwar marik'iyata wato Hajiya Barira, na fahimci anaso ayi amfani da ita a cutar da hammood abinda ya sanya nayi gangancin fita kenan wanda hammood keta bibiyata kuma nasan da hakan, nayi sanasar tattare muhimman sirrikan Idan fada, sedai kuma sun murd'e abin ta hanyar daban zata ba, inada shaidu sosai, inada hujjoji inada sautikan muryoyin su a ajiye suna maganganun cutarwa agaremu baki daya, ganin na kamasu a saukake shine sukamun wannan sharrin" kallon nutsuwa Data ya mata

"Mesa kika gayawa 'yan jarida yana magana" Tana kallon cikin idansa tace

"Sabida yana magana, akan me ze rayu a kurumce akan wasu banzayen mutane, akan me yana namiji ze zama wani irin mace ma ta fishi, akanme ze rik'a rayuwa ta rashin 'yanci alhali shi saraki ne, koni nan danake mace aka d'aura aurena da d'an sarki inajin izza tana fizgana akan me yarima ze mayar da kansa sakarai? Danme yasa Uncle Jay ze tilasta masa datse harshen sa? Akan me ? Nisawa Hammood yayi kafin yace

"Akan me kika sadaukar da rayuwarki akan tawa ? Mesa zaki taimaki wawa kamar ni? Murmushi tayi

"Wawane ya fara taimako na dole in biya bashi, bayaga haka kai yayana ne ka manta? Above all kuma akwai k'auna" Murmushi Data yayi kafin yayi gyaran murya yace

"Kin d'auki hanya me kyau sosai sedai kuma hanyace mafi hatsari agareki, sedai dabadan keba bansan yanda za'ayi abubuwa su warware acikin sauk'i haka ba, yanxu da kikayi nasarar gano komai da kowa menene taimakon gaggawa dakika shirya bamu sabida bamuda lokaci, bamu kad'ai muke shiri ba harsu nasan sunacen suna shirin yak'i babba damu" Kallon sosai tayiwa Hammood kafin tace

"Dabadan mahaifiyar khairiyya ba dabazan kawo wannan lokacin a wannan garin ba harna samu wayewa, da k'arfin dukiyar ta nayi nasarar samun ilimi na addini dana zamani, itace take ciyar dani banda so dakuma k'auna babu abin ta nunamun, har lokacin danayi yunk'urin tozartar da ita in tona mata asiri ko bak'ar magana bata gayamun ba, tayi zaman amana dani, ta d'aga darajata har kawo wannan lokacin tayaya zanyi kishi da 'yarta data rayu batare dajin dad'in uwartaba har zuwa aurenta, ni abokiyar zaman khairiyya ace nasan sirrin mahaifiyar ta mafi muni, nakuma san nata mafi muni duk a matsayinta na kishiyata anya anmata adalci kuwa? Tayaya zata rayu a farin cikin sanin cewar abokiyar zamanta tasan labari mafi muni akan mahaifiyarta da wani b'angare anata, da wannan nakeso kafin na bayar duk wasu hujjoji da kuma shaidu dana tara in sanya sharad'i na" kallon ta sosai Hammood keyi lokaci d'aya zuciyar sa ta shiga luguden tashin hankali, me yarinyar nan take nufi, Data dake nazarin ta yace

"Toohh wannan wane irin sharad'ine haka? Gyaran zaman ta tayi sannan tace

"Tun daga kan sarki da sarauniya har duk wani wanda baya cikin k'ungiyar aci duhu ta idan fada rayuwar su tana cikin hatsari, ya rage na Hammood ya cecesu ta hanyar rubutamun saki har k'waya uku in bashi duk wani abu daze tarwatsa mutanen fadar sa danakedasu a hannu, kokuma yak'i ya sakeni in adanae hujjoji da shaidun danake dasu al'ummar dasuke iyayensa, da talakawan sa su mutu a banza akan sonkan sa, banaji wannan aikine me wahala agaresa yasha gayamu ya tsanani, bashida wata alak'a dani na mata da miji tun bayan auren mu bare yace mun saba, dan haka yanxu dabara ta ragewa me shiga rijiya" Yanayin sa kad'ai zaka kalla ka tabbatar wa kanka cewar wani sabon tashin hankali ya ziyar cesa, gaba d'aya ya gid'ime wata iriyar zuface ta keto masa ya kalli Data cikin tashin hankali yace

"Uncle Sufyan kanajin wani zance kuma na mata, wannan wane irin magana ne" Shiru Data yayi na wani lokaci sannan ya kalli Hafsa, seda ya had'a rai sannan yace

"Ke waya gaya miki aure abun wasa ne? Kokuma mu sa'anninki ne dazaki gindaya mana wannan sharad'in e ? Turo baki taki tanajin azuciyarta iya abinda take so kenan, sannan tace

"Nidai abarni da zab'i na kawai, Uncle mutumin nan yanda yakecin zalina, ya tugemun gashin kaina, ya dinga marina kuma ba sona yake bafa, daga kawai na tausaya masa na rabashi da abinda bayaso, ni idan yanaso in tattare komai in bashi ya bani takardana, in bayaso kuma kowa ya rik'e abinda yakeda iko dashi" Sosai data yake kallonta ee lallai batada kunya yarinyar nan, shi zata gayawa magana, kallon Laure yayi yace

"Laurah jeki kawomun biro da takarda" Jiki a mace ta mik'e taje ta kawo karb'a yayi ya baiwa Mood yace yana kallon sa

"Kasan dai akan mace bazamu sadaukar da rayukan dukka wad'an nan mutanen bako, dan haka kq rubuta mata saki ukun datake buk'ata yanzu yanzu" Sororo yayi yana kallon Data shi kuwa ya d'auke kansa daga dubansa cikin basarwa yana furta

"Kai muke jira"

*Nagode da addu'oinku, yara sun samu sauki Alhamdulillah, na lek'okuna daba samu sararin yi hakan, nasan idan muka shiga week days aka soma maganar aikin yarona daya zakuji ni shiru nagode da son so.*
Mom Nu'aiym.

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI*

27.
  Be rubuta komai ba se kallon Data da yake, wanda shi kuma ya gama karantawa matarsa abinda yakeso tace akan maganar, gyaran murya tayi sannan tace

"Wannan ciwone na 'ya mace babu wanda ze fahimceshi semu mata, tabbas Hafsat kinada kaifin basira kin cika 'yar halak me adalci kuma sannan ni kinyi matuk'ar burgeni da wannan sadaukarwar taki,zamu baku wurin kuyi shawara amma mintuna goma kacal, muje ciki Hafsat" Tana zumb'ura  baki ta mik'e duk suka bisu da kallo, Data yana murmushi yace yana kallon Mood

"Yaro ka d'akko ruwan dafa kanka, wannan yarinyar dakake gani rigimammiya ce, tanada wayo sosai amma tanada wawta, idan muka mata uzuri muka duba maganarta tana kokari ne kawai ta zama me kirkin gaske, sedai kanta zata cutar keda bakida wani dangi tsayayye idan ka sake ta gidanwa zataje? Koda yake anyi adopting nata agidanku zata yita zama anan ko bayan kun rabu, yanzu kai me zakace game da wannan" Kallon Data yake sosai yana wani tunani kafin daga bisani yace

"Ni bawai son yarinyar nake ba, kawai dai ni son rabuwa da itane banayi, sabida wasu dalilai kaga ai kaima shaidane ta taimakemu da iyakacin k'arfinta, sannan batada wani jigo kuma batada gata semu se Allah" Gajeran murmushi Data yayi tunawa da yanda yayi akan soyayyar dayakewa Laure daya kasa ganewa seda ta kusa kashesa, bazece da Mood komai ba, ze barshi dan kanshi ya gane da kanshi

"Yanzu kaga bamuda lokaci, yaya zamuyi da ita? Kawar dakai Mood yayi gefe guda sannan yace

"Barni da ita, k'aryar rashin kunya takeyi, ni zata gayawa saki? Bari su dawo" Da ido kawai Data ya bishi ya barsa da dabarar sa yaga iya gudun ruwan sa a wannan lokacin, shin mezeyi? Haka sukayi shiru har zuwa lokacinda suka dawo palon se kumbura suke, yana ganinsu ya soma b'ata fuska tamkar akwai abinda yake damun sa lokaci d'aya yakai hannun sa saman kafad'arsa inda aka harbesa ya soma furta wai! Da azama ta k'araso cikin parlor sosai ta durk'usa kusa dashi hartana d'aura hannun ta akan kafad'ar sa

"Yaa Mood meya same ka? Kanne ido d'aya yayi yace

"Kawai senaji wannan raunin yanamun zafi har cikin zuciya ta, inaga mutuwa zanyi kidacen likita ya sanar dani da k'yar inzan rayu, idan na mutu ki yafemun duk abinda na miki kinji" kallon Data tayi cikin rud'u

"D'an sanda mukaishi asibiti mana" Sunan data kira Data dashi ga kuma k'aryar da hammood ya karkace kai yana laftawa yasanya Data jin wata uwar dariya tana shirin tasimai da k'yar ya danne yace
Chapter 52 · 0% Book details